Real za ta dauki Haaland a badi, Henry ya caccaki Wenger

An wallafa

Har yanzu Raheem Sterling, mai shekara 26, na fuskantar rashin tabbas kan makomarsa a Manchester City. (Daily Telegraph - subscription required)

Dan wasan Fiorentina da tawagar Serbia Dusan Vlahovic, ya yi mafarkin ya koma Manchester City. Tun kafin fara kakar bana an yi ta alakanta dan wasan da cewar ya koma taka leda a kungiyar Ettihad. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Thierry Henry ya caccaki tsohon kocinsa na Arsenal, Arsene Wenger da yin ja gaba wajen tsara gudanar da gasar cin kofin duniya duk bayan shekara bibiyu. (Sun)

Kocin Manchester United, Ole Gunnar Solskjaer ya bukaci Jadon Sancho da ya kara sa kwazo ko y afara ci wa kungiyar kwallo a karon farko. (Mirror)

Dan wasan Chelsea,Timo Werner, na fuskantar kalubalen makomarsa a Stamford Bridge, yana da ya baya kan ganiya tun zuwan Romelu Lukaku kungiyar a bana. (London Evening Standard)

Jose Mourinho na son daukar dan wasan da ya horar a Tottenham, Tanguy Ndombele, mai shkara 24 zuwa Roma. (Calciomercarto via Express)

Manchester City na duba yiwuwar daukar dan kwallon Villarreal, Pau Torres. (Marca - in Spanish)

Everton za ta yi kokarin daukar dan wasan Newcastle, Sean Longstaff a watan Janairu. (Independent)

Real Madrid za ta tanadi kudin sayen dan kwallon Borussia Dortmund, Erling Haaland a karshen kakar bana, za kuma ta ci gaba da bibiyar Kylian Mbappe na Paris St-Germain. (AS - in Spanish)

Axel Tuanzebe, mai shekara 23 wanda ke buga wasannin aro a Aston Villa na son komawa kungiyar gabaki daya daga Manchester United. (Birmingham Mail)