Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihohin Najeriya 10 da aka fi yi wa zamiyar bashi a shekarar 2026
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Alƙaluman da Hukumar Ƙididdiga ta Najeriya (NBS) da Kwamitin Raba Kuɗaɗen Tarayya (FAAC) suka fitar sun nuna cewa gwamnatin tarayya ta cire biliyoyin naira daga rabon kuɗin wasu jihohin domin biyan basussukan cikin gida da na ƙasashen waje a zangon farko na shekarar 2026.
Bayanan sun nuna cewa tsakanin watan Janairu da Maris na shekarar 2026, jihar Lagos ce aka fi cire wa kuɗi daga rabonta na FAAC domin biyan bashin ƙasashen waje, inda aka cire mata naira biliyan 26.38.
Kaduna ce ta biyu da aka cire wa naira biliyan 19.28, sai Edo ta uku da aka cire wa Naira biliyan 8.41.
Sai dai waɗannan alkaluma ba suna nufin cewa su ne jihohin da ake bin mafi yawan bashi a Najeriya ba.
Yawan kuɗin da ake cire wa jiha kan danganta ne da jadawalin biyan bashi da kuma yarjejeniyar bashin da aka karɓa.
Amma shin nawa ne basussukan da ake bin waɗannan jihohi, kuma me bayanan Hukumar Kula da Basussuka ta Najeriya (DMO) suka nuna game da nauyin bashin da ke kansu?
Me ya sa ake yi wa jihohin zamiya?
A duk lokacin da wata jiha ta karɓi wasu basussukan ƙasashen waje, ana ware wani kaso daga rabonsu na FAAC domin biyan bashin idan lokacin ya yi.
Lokacin da jiha za ta karɓi bashi daga hukumomi ko cibiyoyin kuɗi cikin gida da na ƙasashen waje, yawanci gwamnatin tarayya ce ke tsayawa/lamuni wajen karɓo bashin.
Saboda haka idan lokacin biyan bashin ya yi, gwamnatin tarayya kan zamiye kuɗin daga rabon jihar kafin a aika mata da sauran kuɗin.
Wannan tsari yana taimakawa wajen tabbatar da cewa Najeriya da jihohinta suna cika alƙawuran da suka ɗauka ga masu ba da lamuni, tare da kauce wa jinkiri ko kasa biyan bashin.
Idan aka yi wa jiha zamiyar kuɗi mai yawa, hakan na iya rage kuɗin da za ta samu a wata domin gudanar da ayyukan gwamnati, biyan albashi ko aiwatar da sauran ayyukan raya ƙasa.
Jihohi 10 da aka fi cire wa kuɗin
- Legas
Jihar Lagos ce a sahun gaba cikin waɗanda ake yi wa zamiyar kuɗaɗen, inda aka cire mata Naira biliyan 26.38 a cikin watanni uku na farkon shekarar 2026.
- Kaduna
Jihar Kaduna ce ta biyu bayan Lagos, inda aka cire mata Naira biliyan 19.28 daga rabonta na FAAC.
- Edo
Jihar Edo ce ta uku cikin jerin jihohin da aka fi yi wa zamiyar kuɗaɗen. An cire wa Edo Naira biliyan 8.41 a watanni ukun farko na 2026.
- Cross River
An cire wa Cross River Naira biliyan 7.08 daga kasonta na FAAC a zangon farko na 2026.
- Rivers
Jihar River da ke kudu maso kudancin Najeriya na daga cikin jihohin da ke da tarin albarkatun man fetur.
Tana daga cikin jihohin da ke samarwa ƙasar haraji sosai bayan Legas. Daga kasonta na FAAC an cire mata Naira biliyan 6.30.
- Bauchi
Jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya na daga cikin jihohin da ke da tarin bashi. Ita ma an cire mata Naira biliyan 5.99 daga kasonta na FAAC a farkon shekarar 2026.
- Katsina
A tsakanin watan Janairu zuwa Maris ɗin 2026, an cire wa Katsina Naira biliyan 5.68.
- Osun
An yi wa jihar Ogun zamiyar Naira biliyan 5.54 daga kasonta na FAAC a zangon farko na 2026.
- Oyo
Jihar Oyo ma daga cikin cikin goman farko da aka fi yi wa zamiya daga kasonta na FAAC a farkon 2026, inda aka cire mata Naira biliyan 4.09.
- Neja
Jihar Niger ce ta rufe jerin jihohin goma da aka fi yi wa zamiyar kuɗi, inda aka cire mata Naira biliyan 3.73 a zangon farkon shekarar 2026
Basukan da ake bin jihohin a cikin gida da ƙasashe waje
- Lagos
Bayanan Hukumar Kula da Basussuka ta Najeriya (DMO) sun nuna cewa a ƙarshen watan Disamban 2025, ana bin jihar Legas bashin cikin gida da ya kai Naira tiriliyan 1.22.
Jihar Legas na da bashin ƙasashen waje da ya kai dala biliyan 1.17, wanda shi ne bashi mafi yawa a tsakanin jihohin Najeriyar.
- Kaduna
A ƙarshen shekarar 2025, ana bin jihar Kaduna bashin cikin gida da ya kai Naira biliyan 84.64, yayin da bashin ƙasashen wajenta ya kai dala miliyan 684.3.
- Edo
Alƙaluman DMO sun nuna cewa jihar na da bashin cikin gida na Naira biliyan 91.18 da kuma bashin ƙasashen waje na dala miliyan 354.
- Cross River
Jihar na da bashin cikin gida da ya kai Naira biliyan 137.36, yayin da bashinta na ƙasashen waje ya kai dala miliyan 222.9.
- Rivers
DMO ta ce jihar na da tarin bashin cikin gida da ya kai Naira biliyan 378.81, yayin da bashinta na ƙasashen waje ya kai dala miliyan 170.9.
- Bauchi
Bashin cikin gida na jihar Bauchi ya kai Naira biliyan 156.05, yayin da bashinta na ƙasashen waje ya kai dala miliyan 220.6.
- Katsina
Jihar Katsina mai fama da matsalar tsaro na ɗaya daga cikin mafi ƙarancin basussukan cikin gida, inda alƙaluman DMO suka nuna ana binta bashin Naira biliyan 14.11. Bashinta na ƙasashen waje kuwa ya kai dala miliyan 200.6.
- Ogun
A ƙarshen 2025, jihar Ogun na da bashin cikin gida na Naira biliyan 227.47 da kuma bashin ƙasashen waje na dala miliyan 217.
- Oyo
DMO ta ce bashin cikin gidan jihar ya kai Naira biliyan 77.42, yayin da bashinta na ƙasashen waje ya kai dala miliyan 87.5.
- Neja
Bayanan DMO sun nuna cewa jihar Neja na da bashin cikin gida na Naira biliyan 142.67, yayin da bashinta na ƙasashen waje ya kai dala miliyan 140.6.
Nawa ne bashin da ake bin Najeriya?
A watan Afrilun 2026, Hukumar Kula da Basuka ta Ƙasa (DMO) ta bayyana cewa, adadin bashin da ake bin Najeriya ya kai Naira tiriliyan 159.28.
Wannan adadin ya haɗa da bashin cikin gida da na waje, wanda idan aka raba shi, ya nuna cewa kusan kowane ɗan Najeriya na ɗauke da nauyin bashin da ya kai Naira 724,000 a kansa.
Ofishin ya ce bashin da Najeriya ta ciyo daga ƙasashen ƙetare ya kai naira tiriliyan 74.43 a watan Disambar 2025.
Ko a watan Maris ɗin da ya gabata, sai da majalisar dokokin Najeriya ta amincewa shugaba Tinubu ciyo bashin dala biliyan 6.