'Yan wasan Atletico da suka doke na Barca a La Liga 2-0

An wallafa

Atletico Madrid ta yi nasarar cin Barcelona 2-0 a wasan hamayya da suka fafata ranar Asabar karawar mako na takwas.

Bayan da Barcelona ta sha kashi a Champions League a gidan Benfica da ci 3-0 ranar Laraba, za kara fuskantar matsi a gasar La Liga.

Thomas Lemar ne ya fara cin kwallo daga baya tsohon dan wasan Barcelona, Luis Suarez ya zura na biyu a raga.

Shima Antoine Griezmann dan kwallon Barcelona da ke buga wasannin aro a tsohuwar kungiyarsa Atletico ya shiga karawar daga baya.

Kungiyoyin sun kara a bara a La Liga, inda Atletico ta yi nasara da ci 1-0 ranar 21 ga watan Nuwambar 2020, a wasa na biyu suka tashi 0-0 ranar 8 ga watan Mayun 2021 a Nou Camp.

'Yan wasan Atletico Madrid:

Masu tsaron raga: LECOMTE da kuma OBLAK

Masu tsaron baya: J.M. GIMÉNEZ da RENAN LODI da SAVIC da FELIPE da M. HERMOSO da TRIPPIER da kuma VRSALJKO

Masu tsaron baya: R. DE PAUL da KOKE da LEMAR da MARCOS LLORENTE da HÉCTOR HERRERA da kuma CARRASCO

Masu cin kwallo: JOÃO FÉLIX da GRIEZMANN da SUÁREZ da CORREA da kuma SAPONJIC

Jordi Alba ya murmure zai buga wa Barcelona wasan, amm dai Pedri na jinya, Ronald Koeman ba zai ja ragamar karawar ba, sakamakon hukuncin dakatarwa wasa biyu da aka yi masa, bayan jan kati a karawa da Cadiz.

'Yan wasan Barcelona:

Ter Stegen da Dest da Pique da R. Araujo da Sergio da Riqui Puig da Memphis da Ansu Fati da Demir da Neto da Coutinho da Lenglet, da kuma L. De Jong.

sauran sun hada da Jordi Alba da S. Roberto da F. De Jong da O. Mingueza da Umtiti da Eric da Inaki Pena, Nico and Gavi.

Atletico Madrid za ta buga wasan gaba ranar 17 ga watan Oktoba, inda za ta ziyarci Granada, ita kuwa Barcelona za ta karbi bakuncin Valencia a dai ranar da Atletico za ta fafata.