Barca na harin Kane, Rashford ya amince a rage masa albashi

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Dan wasan Aston Villa da ƙasar Ingila, Morgan Rogers, na son komawa ƙungiyar Arsenal wadda ta lashe gasar Firimiy a wannan bazara, inda kungiyar ta Gunners ta sanya ɗan wasan mai shekara 23 a cikin jerin 'yan wasan da take son ta dauka .(Talksport)

Dan wasan Ingila da ke taka leda a Manchester United, Marcus Rashford mai shekaru 28, ya amince a rage masa albashi domin komawa Tottenham kan kudi fam miliyan 40 a wannan bazara, bayan kammala zaman aro da ya yi a Barcelona. (i paper)

Kungiyar Tottenham na da kwarin gwiwar kulla yarjejeniya da dan wasan Newcastle, Sandro Tonali, kan kudi kusa da fam miliyan 85. Sai dai dan wasan na tawagar Italiya mai shekara 26 ya fi son komawa Arsenal, abokiyar hamayyar Tottenham.(Daily Mail - subscription required)

Dan wasan Chelsea Trevoh Chalobah mai shekara 26, wanda aka kira shi a makare cikin tawagar Ingila ta gasar cin kofin duniya, yana cikin wadanda kocin Como, Cesc Fabregas, ke sha'awar dauka.(Fabrizio Romano)

Kungiyoyin Bayern Munich da Tottenham duka suna sha'awar daukar dan wasan Juventus , Bremer mai shekara 29. Sai dai dan wasan na ƙasar Brazil ya nuna yana son ya ci gaba da zama a Turin.(Gianluca DiMarzio - in Italian)

Kungiyar Barcelona ta yi wani yunƙuri na bazata domin ganin ko dan wasan Ingila, Harry Kane mai shekaru 32, zai amince ya bar Bayern Munich ya koma kungiyar ta Sifaniya.(Sport - in Spanish)

Kungiyar Manchester United ta shirya yin asara kan dan wasan Uruguay Manuel Ugarte mai shekaru 25, domin ta sayar da shi a wannan bazara. (Sun)

Kungiyar Leeds United ta kara matsawa kusa da kammala yarjejeniya daukar dan wasan Southampton da yankin Arewacin Ireland, Shea Charles mai shekara 22, wanda ya rage masa shekara guda kacal a kwantiraginsa na yanzu.(Teamtalk)

Kungiyar Brighton na kara matsowa kusa da kammala daukar dan wasan Venezia kuma da ƙasar Austria Michael Svoboda.mai shekaru 27 (Sky Sports)

Kungiyar Arsenal har yanzu ba ta kai ga cimma yarjejeniya ba domin daukar dan wasan kungiyar Kolkheti kuma na tawagar 'yan kasa da shekara 21 ta Georgia, Andria Bartishvili. Haka kuma kungiyoyin Liverpool da Paris FC su ma na kokarin kulla yarjejeniya domin daukar matashin mai shekaru 17.(Talksport)

Dan wasan West Ham da ƙasar Faransa Jean-Clair Todibo mai shekaru 26, na daf da amincewa da komawa aro zuwa kungiyar Fenerbahce bayan da West Ham ta fadi daga gasar Firimiya.(Star - in Turkish)