Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Messi ya zama kan gaba a cin kwallaye a gasar kofin duniya mai 18

Takaitaccen Bayanin Wasa

Gasar Kofin Duniya
- Matakin rukuni
Argentina 2 , Austria 0 at Full time
Argentina
Austria
Full time
Hutun rabin lokaci Argentina 1 , Austria 0

Key Events

Argentina

  • L. Messi Goal 38 minutes, Goal 90 minutes plus 5

Austria

    Ba da ƙwallo a ci
    Argentina,F. Medina (38 minutes)

    Taƙaitattu

    Rahoto kai-tsaye

    Mohammed Abdu tare da taimakon AI

    1. Nan muka kawo karshen shirin

      Da fatan kun ji dadin kasancewa tare da BBC Hausa.

      Za mu kawo muku wasan Ingila da Ghana a gobe Laraba kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu, za mu fara da karfe takwas a take leda karfe tara na dare agogon Najeriya.

    2. Wasannin da za a buga nan gaba a gasar kofin duniya

    3. Yadda aka buga wasan

    4. Argentina ta kai zagaye na yan 32, FT: Argentina 2-0 Austria

    5. An tashi wasan, Argentina 2-0 Austria

    6. Argentina 2-0 Austria, Lionel Messi

      An samu gudun tazara mai kyau, kuma Argentina ta buga amma kwallon ya yi waje,

    7. GOAL - Argentina 2-0 Austria, Lionel Messi

      Kwallo na 18 da ya ci a raga a gasar cin kofin duniya.

      Kwallo ce mai kyau aka yi ta kokarin buga wa ba ta shiga ragar Austria ba, sai daga baya Messi ya buga ta fada raga.

    8. Katin gargadi mai ruwan d, Argentina 1-0 Austria

      Leandro Paredes ya karbi katin gargadi, sakamakon ketar da ya yi wa Carney Chukwuemeka.

    9. An yi karin minti biyar, Argentina 1-0 Austria

      Da alama Argentina za ta tafi da maki uku, domin lokaci ya cika an yi karin minti biyar.

      Hakan zai bai wa Argentina damar kai wa zagayen gaba da maki shida da cin kwallo hudu daga wasa biyu a cikin rukuni na 10 a gasar cin kofin duniya.

    10. , Argentina 1-0 Austria

      Enzo Fernandez ya yi nasarar shiga cikin akwatin Austria, amma babu matsala daga wajen Kevin Danso

      Har yanzu Austria na ci gaba da kai kora.

    11. Austria ta yi canjin dan wasa, Argentina 1-0 Austria

      A karshe dai Austria ta fitar da Michael Gregoritsch ta maye gurbinda da Carney Chukwuemeka.

    12. Argentina ta yi canji biyu, Argentina 1-0 Austria

      Ta fitar da Rodrigo de Paul da Facundo Medina ta maye gurbinsu da Leandro Paredes da kuma Nicolas Tagliafico.

    13. , Argentina 1-0 Austria

      Da alama magoya baya a filin Dallas suna jin dadin wasan nan sai kuwa suke yi, suna kallon yadda Messi ke taka leda da kafa tarhin zama kan gaba a yawan cin kwallaye a gasar cin kofin duniya a tarihi mai 17 a raga.

    14. , Argentina 1-0 Austria

      Hadari ba sai a mota ba, lokacin da golan Argentina zai kama kwallo, sai Arnautovic ya sa jiki, amma bai samu ba, Martinez ya rike kansa, za a duba lafiyarsa.

    15. , Argentina 1-0 Austria

      Ooooh, kufa yi a hankali jan kati na bayan aljihun rafli!

      Konrad Laimer da Facundo Medina sun ture juna, an kuma bai wa kowanne katin gargadi.

    16. An je hutun shan ruwa, Argentina 1-0 Austria

      An kammala hutun shan ruwa shi ne na biyu a wannan wasan.

      Har yanzu Argentina na cin kwallo 1-0, shin za a farke ko kuwa?

    17. Austria ta yi canji uku, Argentina 1-0 Austria

      Austria ta fitar da kyaftin dinta, David Alaba da Stefan Posch da Paul Wanner ta maye gurbinsa da Marko Arnautovic da Marco Friedl da kuma Alexander Prass.

    18. , Argentina 1-0 Austria

      Dama mai kyau da Austria ta samu, yayin da Marcel Sabitzer ya buga kwallo ga Michael Gregoritsch wanda ya sa kai, amma Facundo Medina yana wajen bai bayar da wata dama ba.

    19. Argentina ta yi canji biyu, Argentina 1-0 Austria

      Argentina ta saka Julian Alvarez da Nico Gonzalez a cikin fili, sun maye gurbin Lautaro Martinez da kuma Enzo Fernandez.