Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda Boko Haram ‘ke horar’ da mayaƙan Bello Turji - Rahoto
Wata ƙungiyar tabbatar da adalci a Najeriya ta yi ikirarin cewa mayaƙan Bello Turji na samun horo daga wasu da ake zargin mambobin ƙungiyar Boko Haram ne a wasu dazuka da ke jihar Sokoto kusa da iyakar Zamfara.
Rahoton ƙungiyar ya ce waɗanda ke ba da horon na koyar da mayaƙan Turji dabarun yaƙi da kuma yadda ake amfani da sabbin makamai, ciki har da abubuwan fashewa kamar bama-bamai da nakiyoyi.
Ƙungiyar ta ce bayanan da ta tattara sun nuna cewa ana gudanar da irin waɗannan horaswa ne a wasu wurare da ke cikin dazukan yankin, inda mayaƙan ke samun ƙwarewa kan amfani da makamai da kuma dabarun kai hare-hare.
Shugaban kungiyar Bashar Altine Guyawa Isa, ya shaida wa BBC Hausa cewa ''Bello Turji ya samo wasu manyan makamai da muke zargin an kai masa har daji, kuma su wadannan fandararrun 'yan Boko Haram da suka bar sansaninsu kuma suka ki mika wuya ga hukumomin Najeriya ne suka horar da yaran na sa yadda ake amfani da su''
Ya kara da cewa baya ga haka, ana kuma koya musu yadda ake sarrafawa da uma amfani da nakiyoyi ko bom, don sake dagula lamuran tsaro arewacin Najeriya.
A cewar rahoton, wannan lamari na nuna yiwuwar samun haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyoyin masu aikata ta'addanci da kuma ƙungiyoyin ƴan bindiga da ke aiki a yankunan arewa maso yammacin Najeriya.
Ikirarin na zuwa ne bayan wani bidiyo da Bello Turji ya fitar a baya-bayan nan, inda ya ɗauki alhakin wani hari da aka kai wa sojojin Najeriya.
Bidiyon ya janyo muhawara a tsakanin jama'a da masu bibiyar al'amuran tsaro, musamman ganin yadda ɗan bindigar ya fito fili yana magana kan ayyukansa duk da ƙoƙarin hukumomi na daƙile ayyukan ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.
Dama dai masana harkokin tsaro sun sha bayyana damuwa kan yiwuwar alaƙa tsakanin ƙungiyoyin ƴan bindiga da ƙungiyoyin masu ikirarin jihadi, suna masu cewa irin wannan haɗin gwiwa na iya ƙara wa matsalar tsaro rikitarwa.
Har yanzu dai hukumomin tsaro a Najeriya ba su fitar da wata sanarwa da ke tabbatar ko musanta ikirarin da ƙungiyar ta yi ba.
Sai dai rahoton ya ƙara fito da damuwar da ake da ita kan ci gaba da tabarbarewar tsaro a wasu sassan arewa maso yammacin Najeriya, inda hare-haren ƴan bindiga suka ci gaba da yin barazana ga rayuka da dukiyoyin al'umma.
Yayin da ake jiran ƙarin bayani daga hukumomin tsaro, masu ruwa da tsaki na ci gaba da kira ga gwamnati da ta ƙara ƙaimi wajen bincike da kuma ɗaukar matakan da za su hana ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai ƙara samun ƙarfin da zai iya jefa yankin cikin sabon ƙalubalen tsaro.
Sunan Bello Turji ya karaɗe wasu sassa na Najeriya musamman a arewa maso yamma sakamakon masarautar fashi da makami da ya kafa a dazukan jihohin Zamfara da Sokoto.
Garuruwa da dama da suka haɗa da Isa na Sokoto da kuma yankunan Ƙaramar Hukumar Shinkafi na Zamfara na daga cikin yankunan da Turji ya mayar kamar masarautarsa, inda yake sace mutane don karɓar kuɗin fansa da kuma kashe ko barin waɗanda ya ga dama.
Kazalika, basaraken ɗan fashin da mayaƙansa kan karɓi harajin amfanin gona daga mazauna yankunan, wasu lokutan kuma sukan ƙona gonakin idan mutanen suka yi gardama.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa ƙasurgumin ɗan fashin na neman yin sulhu da gwamnati har ma ya sako mutum fiye da 50 da ya yi garkuwa da su a watannin baya. Kodayake 'yan sanda sun ce mutum 68 ne, kuma su suka ceto su.