Donny van de Beek: Dan wasan Man Utd ba zai buga Euro 2020 ba

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Manchester United, Donny van de Beek ba zai buga wa tawagar Netherlands gasar cin kofin nahiyar Turai, Euro 2020 ba, sakamakon raunin da ya yi.
Mai shekara 24, ya fuskanci kalubale a kakar da aka kammala, bayan da ya buga mata wasan lik hudu tun komawarsa Old Traford a bara.
Van de Beek ya yi wa Netherlands wasa 19, wadda karawa ta karshe da ya yi mata ita ce wasan da ta doke Gibraltar 7-0 ranar 30 ga watan Maris.
Kawo yanzu kocin Netherlands, Frank de Boer bai maye gurbin dan kwallon mai wasa daga tsakiya ba.
"Donny van de Beek ya hakura da buga gasar cin kofin nahiyar Turai," in ji wani jawabi da hukumar kwallon kafar Netherlands ta fitar.
Netherlands za ta fara wasan farko na cikin rukuni na uku da Ukraine ranar Lahadi.







