Me ya sa Nijar ta fice daga kotun duniya?

Asalin hoton, Anadolu via Getty Images
- Marubuci, Hafsa Khalil
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 2
Jamhuriyar Nijar ta miƙa buƙatar a hukumance ta neman ficewa daga kotun hukunta manyan laifuka ta ƙasa da ƙasa wato ICC, watanni tara bayan ta bayyana aniyar ta na ficewa daga kotun.
A watan Satumban 2025, Nijar, tare da ƙawayenta Mali da Burkina Faso - waɗanda dukkansu ke ƙarƙashin mulkin soja - sun fitar da wata sanarwa ta haɗin gwiwa, suna cewa ba za su amince da ikon kotun ta ICC ba, inda suka bayyana kotun a matsayin wani ''mataki danniya na mulkin mallaka.''
Kotun ta ce ta karɓi "sanarwar janyewa" a ranar 18 ga watan Yuni, a cewar wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani. Janyewa daga kotun dai yana fara aiki ne shekara guda bayan miƙa sanarwar yin hakan.
Kotun ta ICC ta ƙara da cewa tilas ne Nijar ta mutunta duka haƙƙoƙin kotun da suka rataya a wuyanta har zuwa wannan ranar.
A shekara ta 2002 ne aka kafa kotun ta ICC da ke birnin Hague na ƙasar Netherlands domin gudanar da shari'ar kan laifukan da suka haɗa da kisan kiyashi da cin zarafin bil'adama da laifuffukan yaƙi da kuma ta'addanci.
Sanarwar da kotun ta bayar a ranar Talata, ba ta yi magana kan Mali ko Burkina Faso ba.
A lokacin da suke bayyana ficewarsu, ƙasashen na yankin sahel guda uku sun ce suna son kafa "tsare-tsaren cikin gida da za su tabbatar da zaman lafiya da adalci".
A bara, Nijar, Mali da Burkina Faso a lokaci guda sun fice daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (Ecowas), tare da kafa ƙungiyar ƙasashen Sahel da ta ƙunshi ƙasashen uku.
Sojoji ne ke iko da ƙasashen bayan juyin mulki a cikin shekarun baya bayan nan.
Dakarun sojinsu na fuskantar tuhuma kan laifukan da suka shafi fararen hula, yayin da ake ci gaba da samun tashe-tashen hankula a yankin sakamakon ayyukan ƙungiyoyi masu iƙirarin jihadi da ke da alaƙa da al-Qaeda da kuma ƙungiyar IS.
A cikin ƴan shekarun nan, ƙasashen uku, waɗanda a baya Faransa ta yi wa mulkin mallaka, sun ƙara zama saniyar ware daga ƙasashen yamma tare da ƙarfafa alaƙarsu da ƙasar Rasha.
Akwai sammacin kama shugaban Rasha Vladimir Putin da kotun ICC ta bayar kan zargin aikata laifukan yaƙi a Ukraine.
Rasha, da ƙasashe irin su Amurka da Isra'ila da China, ba sa cikin ƙasashe 125 da suka kasance mabobin kotun.
Nijar za ta kasance ƙasa ta uku da za ta fice daga kotun ICC bayan Philippines da Burundi.











