Da gaske ne dora ƙanƙara kan ƴaƴan maraina na inganta maniyyi?

- Marubuci, Jacqui Wakefield
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Global Health reporter
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Kowace safiya idan Simon ya tashi daga barci, ya kan tafi wani ɗakin da yake kunna tiriri domin ya tara zufa (sauna).
Zufar kan taimaka masa wajen fitar da abubuwan da jikinsa ba ya buƙata, wanda ya ce hakan na taimaka masa wajen inganta maniyyinsa - amma kuma yana buƙatar kariya daga zafin da ke sanya shi zufar.
"Nakan yi amfani da pakitin ƙanƙara, da ake kira Chill Nuts, domin ɗora shi a kan ƴaƴan maraina na, don kiyaye yawan maniyyina," kamar yadda ya shaida BBC.
Wannan ita ce hanya da yake bi domin tattalin maniyyinsa, duk kuwa da rashin hujjar hakan a kimiyyance.
Mai shekara 28 ɗan Amurkan asalin Venezuela, da ke zaune a birnin Miami na jihar Florida, yakan fita domin shan rana a kullum.
Yakan yawaita shan ruwa tare da sanya gajeren wandonsa da aka yi da auduga, domin kauce wa illar da gumi zai iya yi masa.
Simon bai shirya wa haihuwa nan kusa ba, hasali ma ba shi da abokiyar zama - sai dai ya fi damuwa game da ko ƙarancin maniyyi zai iya shafar lafiyarsa.
Simon na daga cikin mazan a yanzu suke yawan ɗaukar matakan ƙara yawan maniyyinsu.
Batun ƙara yawan maniyyi da ƙwayoyin haihuwar maza na ci gaba da ɗaukar hankalin miliyoyin mutane a shafufan Istagram da TikTok, tun watan Janairu.

Masana ƙwayoyin haihuwa na duniya sun ce an samu ƙaruwar mazan da ke neman bayanai game da maniyyi da waɗanda ke nuna damuwa game da makomar ƙwayoyin haihuwarsu.
Masanan sun ce hakan ba ya rasa nasaba da amfani da wasu hanyoyi na dashen ƙwayayen halitta da kuma damuwar da ake da ita kan wasu tarin guba da ake samu a muhalli, da ke shafar ƙwayoyin haihuwa.
Farfesa Suks Minhas ƙwararren masanin ƙwayoyin haihuwa ya ce yana da muhimmanci maza su riƙa inganta ƙwayoyin haihuwarsu amma ta hanyar neman shawarar likitoci.
Kamar dai sauran mutane, Simon ya fara ganin wannan batu a shafukan sada zumunta.
Amma har yanzu bai taɓa gwada maniyyin nasa ba, kuma ba shi da wani takamaiman dalili na nuna damuwa ga lafiyarsa ba.
"Ina matuƙar fargabar hakan, don haka na zaɓi na kare ƙwayoyin haihuwata ," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani bidiyo ne da fitaccen mai amfani da shafin sada zumunta, Bryan Johnson - ya wallafa ya ja hankalin Simon wajen ''kula'' da lafiyar maniyyinsa.
Dangane da yanayin raguwar ingancin maniyyi a duniya, tsohon hamshakin attajirin na Silicon Valley ya yi iƙirarin cewa yana da matsakaicin ingantaccen maniyyi har sau huɗu.
Ya riƙa ƙarfafa wa mutane su riƙa shiga ɗakin tiriri domin zubar da zufa daga jiki da kuma ɗora ƙanƙaƙara a kan ƴaƴan maraina, domin ƙara wa maniyyinsu inganci, wani abu da Simon yake bi sau da ƙafa.
Bidiyon na Johnson ya samu miliyoyin masu kallo, lamarin da ya ƙara masa tarin mabiya a shafinsa da kuma jaridarsa, waɗanda yake amfani da su wajen tallata magungunansa.
Ba Johnson ne kaɗai ya taɓa yaɗa irin waɗannan maganganu na inganta maniyyi ba.
Akwai fitattun masu amfani da shafukan sada zumunta da ke tallata hanyoyin ƙara yawan maniyyi ga maza, ba tare da hujjar kimiyya ba.
Wasu daga cikin dabarun da ake yaɗawa sun haɗa da tsayuwa a cikin hasken jan ƙwan lartarki da kuma bayar da jini domin fitar da wasu ''guba'' daga jiki.
Maganganun nasu na zuwa ne a daidai lokacin da duniya ke ci gaba da tattauna batun raguwar yawan haihuwa a duniya.
A baya-bayan nan Sakataren Lafiya na Amurka, RFK Jr - ya yi tsokaci game da batun ''matsalar haihuwa'', yana mai cewa a shekarun 1970 maza sun fi maniyyi mai inganci, idan aka kwatanta da mazan yanzu.
To amma babu wata hujjar hakan a kimiyyance, amma dai wasu bincike sun nun akwai yiwuwar tabbatuwar hakan.

Naturopath Lucas na daga cikin masu amfani da shafukan sada zumunta da ke gargaɗi game da ƙwayoyin haihuwa.
"Muna ganin wata annoba a duniya, raguwar ingancin maniyyi tsakanin maza,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.
Wasu daga cikin bayanan da yake wallafa wa shafukan sada zumunta da ba su tabbatar da ingancin hanyoyin inganta ƙwayoyin halitta, sun yaɗu a shafukan sada zumunta.
"Ina bai wa samari shawara su riƙa shafa ƙanƙara a kan marainansu ko ta kan gajeren wandonsu ne aƙalla sau biyu zuwa uku a rana na tsawon mintuna 10 zuwa 15," in ji shi.
Yana mai cewa abokan hulɗarsu sun shaida masa cewa abokan zamansu sun samu juna biyu bayan sun gwada wannan hanya.
Wasu daga cikin mabiyansa na amfani sa hasken jan ƙwai, ko su haska ƴaƴan marainansu da hasken wutar wayarsu.

Wannan batu na inganta ƙwayoyin haihuwa ya zo ne a daidai lokacin da ake samun yawan mazan da ke shan ƙwayoyin haɓaka sinadarin haihuwa.
To sai dai likitoci sun yi gargaɗin cewa yawan shan magungunan kan lalata ƙwayoyin haihuwa.
Haka kuma masu amfani da shafukan kan sayar da magungunan da suka ce suna magance matsalar.
Waɗannan sun haɗa da maganin HCG da HMG, wanda maza da mata suka fi amfani da su wajen inganta ƙwayoyin haihuwarsu.
To amma waɗannan na da illa ga lafiya, sannan sukan haifar da matsala idan aka sha ba tare da shawarar likita ba.
Wani mutum ya faɗa min cewa yana tunanin zai ''haifi ƴaƴa'' da yawa idan ya sha maganin HMG da HCG.

Jamal, ba sunansa na ainihi ba, kan sha magunguna masu yawa na inganta sinadaran haihuwa domin ƙarfafa jikinsa, wanda ke rage masa yawan ƙwayoyin haihuwa.
A shekarar da ta gabata ya dakata da shan maganin lokacin da shi da abokiyar zamansa suka yanke shawarar samun haihuwa.
Ya samu shawarar haɓaka ƙwayoyin haihuwa daga wasu maza da suka ɗauki irin matakan a baya.
"Mutanen sun kwatanta min yadda zan sha maganin, kuma hakan na yi,'' in ji Jamal.
"Na sani abin da ya fi dacewa shi ne zuwa wajen ƙwararrun likitoci, amma haka na saye shi ba tare da shawarar likitocin ba."
To sai dai da buƙatarsa ta kasa biya sai ya tuntuɓi, Farfesa Jayasena, wani ƙwararren likitan haihuwa, wanda ya ce masa hakan na da illa ga lafiya.
Bayan samun shawarar likitan, Jamal ya daina shan duka magungunan.
Wata shida bayan nan kuma sinadaran ƙwayoyin haihuwarsa suka inganta, to sai dai har yanzu ƙwayoyin inganta maniyyinsa ba su gama farfaɗowa ba.
Farfesa Jayasena ya gargaɗi maza irin su Jamal su riƙa neman shawarar masana lafiya kafin shan kowane irin magani, saboda ba koyaushe masu tallata magungunan ke tuntuɓar likitoci ba.











