KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • Sadis Buba

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Yusuf Mohammed

  1. Ƴan sanda sun gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu da hannu a kisan maraban Jos

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta sanar da gurfanar da wasu ƙarin mutane 17 da ake zargi da hannu a kisan gayyan da aka yi wa wata mata a Ungwar maraban Jos, na jihar Kaduna a makon da ya gabata.

    Wata sanarwar da ta fito daga ofishin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar DSP Mansir Hassan ta ce an gurfanar da waɗanda ake zargin ne yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

    Sabarwar ta ƙara da cewa bayan kammala binciken farko, an gurfanar da wasu mutane talatin da uku (33) da ake zargi da laifin haɗa baki da kuma yin taro ba bisa ƙa’ida ba.

    Rundunar ta kuma bayyana cewa mutane talatin (30) da aka kama bayan aukuwar lamarin, ba same su da hannu wajen aikata laifin ba, kuma an sake su ba tare da wani sharaɗi ba.

    Rundunar ta sake nanata cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda ta bayar da tabbacin cewa ta na ƙara ƙaimi wajen ganowa da kamo duk waɗanda ke da hannu, ko kuma suka taimaka wajen aikata wannan laifi.

  2. Kotu ta soke rajistar jam'iyyar NDC

    ...

    Asalin hoton, NDC

    Wata babbar kotun tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ta yi watsi da hukuncin da ta yanke tun farko da ta umarci hukumar zaɓen Najeriya INEC ta yi wa jam’iyyar NDC rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, mai shari’a Isah Dashen, alkalin kotun ya ce dole ne a saurari dukkan ɓangarorin da abin ya shafa kafin a yanke wani hukunci kan lamarin.

    Kotun ta amince da buƙatar da jam’iyyar Peace Movement Party (PMP) ta shigar, inda ta ce ya kamata a ce jam’iyyar ta zama tana cikin ƙarar.

    A cewar mai shari’a, hukuncin da aka yanke a baya ya saɓawa tsarin mulki domin an zartar da shi ba tare da jin ta bakin dukkan masu ruwa da tsaki ba.

    Ya bayyana cewa irin wannan kuskuren ya soke gaba ɗaya duk wani abin da ya shafi hukuncin da aka yanke kan batun.

    Don haka, kotun ta bayar da umarnin a sake fara shari’ar daga farko, inda INEC da PMP da kuma NDC za su kasance a matsayin ɓangarorin da ke cikin shari’ar.

    Hukuncin dai ya mayar da tirka-tirkar da ake yi kan batun rajistar jam'iyyar ta NDC zuwa babbar kotun tarayya domin ci gaba da sauraren ƙarar, inda ake sa ran za a ji daga bakin dukkanin ɓangarorin da abin ya shafa kafin a yanke hukunci.

  3. Faransa ta hana shan barasa a wasu wurare a birnin Paris

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin Faransa sun sanar da taƙaita shan barasa da kuma sayar da ita ga da jama'a a birnin Paris, a wani yunƙuri na rage matsin lamba kan asibitocin babban birnin ƙasar a lokacin da ake fama da matsanancin zafi.

    Za a hana mutanen Paris shan barasa a bainar jama'a daga tsakar ranar Juma'a har zuwa ƙarfe 07:00 na ranar Asabar. Matakan za su kasance daga irin wannan lokacin daga Asabar zuwa Lahadi.

    Yanayin zafi da ya bar Spain, da Burtaniya da Faransa cikin matsanancin zafi na tsawon kawanak, wanda yanzu haka ya ke shirin komawa gabas, inda masu hasashen yanayi a Jamus da Jamhuriyar Czech suka yi gargadin matsanancin yanayi.

    An yi hasashen cewa yanayin zafi a Jamus na iya kai wa 40C a duk faɗin ƙasar ranar Juma'a.

  4. MDD ta dakatar da shirin kwashe jirage daga Mashigar Hormuz

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumar kula da sufurin jiragen ruwa ta Majalisar Dinkin Duniya (IMO) ta dakatar da shirin kwashe jiragen ruwa sama da 11,000 da suka maƙale a mashigar ruwan Hormuz bayan an kai wa wani jirgin ruwan dakon kaya da ke wucewa hari.

    Shugaban hukumar ta IMO Arsenio Dominguez ya ce an riga an kwashe jiragen ruwa da dama, amma hukumar na son tabbatar da cewa “akwai tabbacin samar da tsaro”.

    Hukumar tsaron ruwa ta Burtaniya UKMTO ta bayar da rahoton a ranar Alhamis cewa, an kai haeri kan wani jirgin ruwa da ke da nisan mil 7.5 daga yankin kudu maso gabashin tashar jiragen ruwa ta Dahit na ƙasar Oman.

    Ba a dai samu rahoton asarar rai dafga harin ba.

    Harin dai ya zo ne bayan rundunar IRCG ta (IRGC) ta yi gargaɗin cewa ''ba za a amince'' da yunƙurin tsallakawa mashigar ta hanyar da IMO ya tsara ba, kuma abu ne "mai hatsarin gaske" don haka akwai buƙatar jiragen ruwa su haɗa kai da Iran.

    Jami'an Amurka sun ce Iran ta harbo jirgin, kamar yadda kafafen yada labaran Amurka suka ruwaito.

  5. Gwamnatin Kebbi ta ƙaryata rahoton mutuwar yara saboda yunwa

    Gwamnan jihar Kebbi

    Asalin hoton, The Governor Of Kebbi State/FB

    Gwamnatin jihar Kebbi da ke arewa maso yammacin Najeriya ta ce babu gaskiya a rahoton ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières, MSF, kan mutuwar ƙananan yara sakamkon cutar tamowa a jihar.

    Wani rahoto da MSF ta fitar ya nuna damuwa kan ƙaruwar alƙaluman UNICEF da ke nuna cewa ana rasa kusan yara 30 cikin 100 ƴan ƙasa da shekara biyar a kowace rana sakamakon rashin abinci mai gina jiki, kuma kusan rabin mace-macen na faruwa ne a jihar Kebbi.

    Sai dai kwamishinan yaɗa labarai na jihar Yakubu Ahmed, ya shaida wa BBC cewa gwamnati ba ta gamsu da ƙididdigar da aka fitar ba.

    Gwamnatin ta kuma buƙaci MSF da UNICEF su gabatar da gamsassun hujjojin da za su tabbatar da rahoton saboda sun san abin da aka faɗa bai faru ba.

    "Gaskiya muna taƙaddama da wannan ƙididdiga da suka bayar". Idan hakan na faruwa, mu a matayin gwamnati ya kamata mu fara sani."

    "A ce yara suna mutuwa cikin ɗarurwa a kowace rana a jihar Kebbi ba tare da gwamnati ta sani ba, abin mamaki ne.Shi ya sa muke son su kawo mana shaida, dan mun san ba ta faru ba, babu wannan mutuwa da suka faɗa," in ji shi.

    Gwamnati ta kuma buƙaci su nemi afuwa kan kuskuren da suka yi, idan suka kaa gabatar da hujja.

    "Ko su ba mu hujja, ko su ba da haƙurin cewa hakan bai faru ba." in ji kwamishinan.

  6. Duk wata yarjejeniya da aka yi kan Hormuz ba da mu ba, shirme ne - Iran

    ...

    Asalin hoton, Tasnim News Agency

    Wani babban jami'in Iran ya ce ba za a iya ba da tabbacin wucewa ta mashigar Hormuz lafiya ba a ƙarƙashin duk wani tsari da aka yi ba tare da sanya hannun Tehran ba.

    A wani sakon da ya wallafa a shafin sada zumunta, mataimakin ministan harkokin wajen ƙasar (Kazem Gharibabadi) ya yi nuni da 'tsare-tsare da kuma hanyioyin da ba a fayyace ba' - wani batu da ke nuna yatsa ga Oman wadda ta kafa wata hanya ta daban da ke bi ta mashigar wanda ke kusa da gaɓar tekun ƙasarta.

    Katafaren kamfanin jiragen ruwa na Evergreen, ya tabbatar da cewa an kai wa ɗaya daga cikin jiragensa hari a lokacin da suka tashi daga mashigar ta hanyar Omani a ranar Alhamis.

    Babu wanda ya ji rauni amma manazarta sun ce aƙalla jiragen ruwa biyu ne a yanzu suka sauya shawarar wucewa ta sabuwra hanyar ta Oman.

  7. Hotunnan yadda ake zaƙulo mutanme a Venezuela

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata tawagar ƙwararrun masu bincike da aikin ceto daga Chile ta tashi zuwa Venezuela
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wani mai aikin ya na leƙowa daga wani gini da ya lalace sakamakon girgizar ƙasar a La Guaira
    ...

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Ma'aikatan ceto na aiki a wani gini da ya ruguje a Caracas, babban birnin Venezuela.
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Mutanen gari na ƙoƙarin sauke wata katanga yayin su ke aikin ceto a La Guaira
    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Wata mata tana jira yayin da ake bincike cikin ɓaraguzai a La Guaira
    ...

    Asalin hoton, EPA/Shutterstock

    Bayanan hoto, Yankin Catia la Mar na ɗaya daga cikin yankunan da lamarin ya fi muni, a jihar La Guaira
  8. CBN ya umarci bankuna su toshe asusun waɗanda ake zargi da 'ta'addanci'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Babban bankin Najeriya ya umurci cibiyoyin hada-hadar kudi da su gano tare da dakatar da kadarorin waɗanda ake zargi da ɗaukar nauyin ayyukan ta’addanci na take.

    A wata sanarwa da Daraktan Sashen kula da Ka'idojin Bankuna na CBN, Olubunmi Ayodele-Oni ya sanya wa hannu, bankin ya ce umarnin ya biyo bayan sabbin sunayen da Kwamitin kula da ƙa'idojin sanya takunkumi na Najeriya da kuma hukumar kula da kadarorin ƙetare na ma'aikatar baitulmalin Amurka suka fitar.

    Hukumomin Najeriya da na Amurka sun bayyana sunayen wasu mutum shida da kamfanoni huɗu da ake zargi da hannu cikin lamarin.

    CBN ya ba da umarni da dama ga cibiyoyin hada-hadar kuɗi, ciki har da bayar da rahoton wasu ma’amaloli da ake zargi cikin sa’o’i 48 da kuma tantance kwastomomin da ake da su, da asusun ajiya, da kuma mamallakan kamfanoni da sunayensu suka bayyana a cikin waɗanda ake zargin.

    ''Babban Bankin ya kuma ce kada a bai wa mutanen ko kamfanonin da aka sanya wa takunkumin kuɗi, ko ayyukan kuɗi ko wasu albarkatun tattalin arziki damar hada-hada kai tsaye ko ta bayan fage.” in ji sanarwar.

    A halin da ake ciki kuma, hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) na shirin shigar da ƙara a gaban kotu kan wani mutum ɗaya da kamfanoni uku da ake zargi da hannu a hada-hadar kuɗaɗe da ke da alaƙa da ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta ISWAP.

    Gwamnatin Najeriya dai ta sha yin gargaɗin cewa ƙasar ba za ta zama maɓoyar ƴan bindiga da masu tallafa musu da kuɗaɗe ba.

  9. NECO ta fitar da sakamakon jarabawar BECE ta 2026

    ...

    Asalin hoton, NECO

    Hukumar shirya jarabawar ta ƙasa ta Najeriya (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar kammala karatun shekra uku na farko a Sakandare (BECE) inda jimillar ɗalibai 186,291 suka yi rijistar jarabawar a faɗin ƙasar.

    A cewar NECO, ɗalibai sun rubuta jarabawar ne a darussa 12, a jihohi 36 na Najeriya da babban birnin tarayya (FCT) da kuma ƙasashen ƙetare guda biyar.

    An fara jarrabawar ne a ranar 20 ga Afrilu, 2026, kuma an kammala a ranar 30 ga Afrilu, 2026. An amince tare kuma da fitar da sakamakon ne bayan kammala taron kwamitin bayar da lambar yabo ta 2026 BECE da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Minna, Jihar Neja, ranar Alhamis.

    Kwamitin ya kuma amince da ranakun 22 da 23 ga Yuli, 2026, a matsayin ranakun sake rubuta jarabawar BECE a darussan lissafi da turanci.

    NECO ta yi bayanin cewa an tsara sake rubuta jarabawar ne musamman don bai wa ’ɗailiban da ba su samu sakamakon da ya gamsar da su b a fannin lissafi da turancin Ingilisghi.

  10. JD Vance ya ce an kafa hanyar sadarwa ta 'kai tsaye' tsakanin Amurka da rundunar IRGC

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Mataimakin shugaban ƙasar Amurka J.D. Vance ya ce Washington da Tehran sun amince da kafa wata hanyar sadarwa ta kai tsaye da dakarun kare juyin juya halin Musulunci (IRGC) don rage haɗarin sake ɓarkewar rikici.

    A wata hira da ya yi da shafin yada labarai na masu ra'ayin mazan jiya na Burtaniya, UnHard, Mr. Vance ya ce, wannan tsari zai haɗa da ganawa tsakanin jami'an sojojin Iran da na Amurka a birnin Doha na ƙasar Qatar, domin warware bambance-bambance da ke tsakanin ɓangarorin biyu.

    Yayin da yake bayani kan tattaunawar da suka yi da jami'an Iran, ya ce: "Sun ce, 'To, za mu tura wani daga rundunar IRGC zuwa Doha domin ya yi aiki a can tare da wani daga Rundunar Sojin Amurka mai kula da yankin Gabas ta Tsakiya (CENTCOM),' kuma ta haka ne za mu warware yawancin waɗannan sabanin ra'ayoyi."

    Mataimakin shugaban ƙasar ya kuma shaidawa kamfanin dillancin labaran Associated Press cewa, Hadaddiyar Daular Larabawa ta kafa sabbin hanyoyin sadarwa da Iran waɗanda a da ba su wanzu ba, wadanda suka haɗa da na tattaunawa kai tsaye da rundunar IRGC.

  11. Amurka ta zargi Iran da kai hari kan wani jirgin ruwan dakon mai na Singapore

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami’an Amurka da ba a bayyana sunayensu ba sun shaidawa kafafen yaɗa labaran Amurka cewa sojojin ruwan Iran ne suka kai hari kan wata tankar mai da ke kusa da mashigar ruwan Hormuz a ranar Alhamis.

    Iran dai ba ta mayar da martani kan wannan zargin ba, amma rundunar sojin ruwa ta IRGC ta yi gargaɗi a daren Larabar da ta gabata cewa duk zirga-zirgar jirage ta mashigar Hormuz ba zai yiwu ba sai ta hanyoyin da aka sanar, kuma dole ne jiragen ruwa su bi ta mashigar tare da hadin gwiwar sojojin Iran.

    Gargadin na rundunar IRGC ya zo ne bayan da Oman ta sanar lokacin ziyarar da Marco Rubio ya kai a wasu ƙasashen yankin Gulf, cewa ta samar da wata sabuwar hanyar teku domin gaggauta tsallakawar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz.

    Wannan labari dai ya samu karɓuwa daga Bahrain, amma bisa ga dukkan alamu sanarwar da rundunar sojojin ruwan ta IRGC ta yi wani martani ne mara kyau kan samar da wannan sabuwar hanyar.

    Sai dai har yanzu Iran ba ta amince ko musanta alhakin harin da aka kai kan jirgin ruwan na Singapore ba.

  12. Adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasar Venezuela ya kai 235

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu aikin ceto na ci gaba da binciken ɓaraguzan gine-gine a Venezuela tyayin da su ke ƙoƙarin ceton rayuka bayan girgizar ƙasar da ta yi sanadin mutuwar mutane aƙalla 235.

    Rahotanni na cewa baya ga waɗanda suka mutu, aƙalla mutum 4,300 sun jikkata sakamakon girgizar ƙasar guda biyu masu karfin maki 7.2 da kuma 7.5 da ta suka afku da yammacin Laraba.

    A Caracas da La Guaira, ana jin mutane suna kiraye-kirayen neman taimako a ƙarƙashin ɓaraguzan gine-gine da suka ruguje.

    Shugaban majalisar dokokin Venezuela, Jorge Rodríguez, ya ce gine-gine 250 ne suka ruguje, akasarinsu a La Guaira, inda BBC ta tabbatar da hoton wani otal mai hawa 10 da ya koma ruguje har ƙasa.

    Har ila yau, an rasa gine-gine da dama a birnin ƙasar, in ji ministan harkokin cikin gida Diosdado Cabello. An kuma samu ɓarna sosai a Trujillo da Yaracuy da Carabobo da Aragua da kuma Miranda.

  13. Assalam Alaikum

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiya

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kamar yadda aka sani za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.