Abin da muka sani kan bidiyon dandazon masu ɗauke da makamai kan babura a Najeriya

Jamai'an ƴansanda da wasu ƴanbindiga

Asalin hoton, UGC

Bayanan hoto, A cikin bidiyon an ga mutanen a kan babura fiye da 40 rike da makamai
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Rundunar ƴansandan Najeriya ta musanta bayanan da suka bazu a ƙasar game da wani bidiyon da ya nuna jami'in ɗansanda na ɗaga wa wasu da ake zargi da kasancewa ƴanbindiga hannu a kan titi.

Sai dai har yanzu ƴan ƙasar na ci gaba da muhawara kan bidiyon, wanda ya nuna wasu mutane a kan babura riƙe da makamai lokacin da suka iske wani abu da ya yi kama da shingen jami'an ƴansanda a wani yankin arewacin ƙasar.

Bayanai sun ce lamarin ya faru ne a yankin Matazu da Musawa na jihar Katsina, ɗaya daga cikin jihohin da ke fama da matsalar tsaro.

Yankin arewa maso yammacin Najeriya ya jima yana fuskantar matsalar tsaro, inda ƴanbindiga ke addabar al'umma ta hanyar kai hare-hare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Me bidiyon ya ƙunsa?

A cikin bidiyon, mai tsawon ƙasa da minti ɗaya wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga wasu jami'an ƴansanda da ke tsaye a wani wuri da ya yi kama da shingen binciken ababen hawa a kan titi.

Jami'ai biyu aka gani a cikin bidiyon sai kuma wata mota da ta yi kama da ta ƴansandan.

An ga jami'an biyu suna ɗaga hannu ga ayarin mutanen da ke kan babura, alamar sun amince musu su ci gaba da tafiya yayin da mutanen suka ci gaba da tafiya a baburansu cikin ayari.

Mutanen a kan babura kusan 40 kowane da goyo, sun riƙa wucewa riƙe da bindigogi, suna musayar ɗaga hannu da jami'an ƴansandan da ke tsaye.

Mene ne ya ja hankalin mutane?

Wasu mutane riƙe da makamai a kan babura

Asalin hoton, bidiyo

Babban abin da ya janyo muhawarar shi ne yadda aka ga mutanen riƙe da makamai kuma a kan babura, wani salo da ƴanbindigar suka yi fice wajen amfani da shi.

Sannan yadda ƴansandan suka ba su damar wucewa ta kusa da su har ma suna musayar ɗaga hannu na daga cikin abubuwan da suka ɗauki hankalin masu muhawarar a shafukan sada zumunta.

Haka kuma a cikin bidiyon an ji wata murya da ke kusa da kyamarar na cewa ''duk waɗannan fa ɓarayin daji ne... ka ga wani da kakin sojoji...'', sai wasu da ke kusa da wurin suka katse shi da cewa ''kai me ya sa kake haka ne Aminu'', sai ya yi shiru.

Me ƴansanda suka ce?

ƴansanda

Asalin hoton, Nigerian Police

Bayanan hoto, Ƴansanda sun gargaɗi masu yaɗa abin da suka kira ƙarya game da bidiyon

Rundunar ƴansandan Najeriya ta musanta zargin cewa mutanen ƴanbindiga ne.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴansandan ƙasar, CSP Anietie Okokon Edem Iniedu, ta fitar ta ce binciken da rundunar ƴansandan ƙasar ta gudanar ya nuna mutanen ƴan bijilanti ne da kuma mafarauta masu rajista da ke taimaka wa jami'an tsaro a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa a jihar Katsina.

A cewar CSP Iniedu bidiyon ya nuna yadda kyakkyawar hulɗa ta kasance tsakanin jami'in ɗansanda da ƴan sa-kan a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa wurin aiki a yankunan.

"Mutanen da aka gani a cikin bidiyon ba ƴanbindiga ba ne. Ƴan ƙungiyar bijilanti ne da kuma mafarauta masu rajista da ke tallafa wa ayyukan jami'an tsaro a aikin haɗin gwiwa da suke yi tare'', in ji kakakin ƴansandan ƙasar.

"Don haka duk wata magana saɓanin wannan ba gaskiya ba ne, an ƙirƙire ta ne domin yaɗa labaran karya da haifar da fitina ga al'umma.''

Abin da masana suka ce

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

BBC ta tuntuɓi wani masanin tsaro a Najeriya da ya buƙaci a sakaya sunansa, wanda kuma ya ce mutanen da aka gani a kan baburan ƴanbindiga ne ba mafarauta ba.

''Na kalli bidiyon da kyau, kuma gaskiya ƴanbindiga ne ba ƴan bijilanti ba, kuma a jihar Katsina abin ya faru'', in ji shi.

''Idan ka duba mashinan da suke kai duka ƙirar Honda ne da aka fi sani da Boko-Haram a yankin, wanda kuma ƴanbindigar ke amfani da su, su ƴanbijilanti da mafarauta sukan yi amfani da babura ƙirar Bajaj ko TVC ne''.

Masanin tsaron ya ce wata alama da ke nuna cewa ƴanbindiga ne ita ce duka baburan an rufe mazauninsu da wata shimfiɗa, wanda ya ce wata alama ce da ƴanbindiga ke amfani da ita don gane baburansu.

Sai dai ya ce an daɗe da yin bidiyon, ba na yanzu ba ne, an ɗauke shi ne lokacin da wasu ƙananan hukumomin jihar Katsina suka riƙa yin sulhu da ƴanbindiga.

''A lokacin da aka yi sulhu da ƴanbindigar, suna kan hanyarsu ta dawowa daga wajen sulhu ne aka ɗauki bidiyon'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ya ci gaba da cewa maganar sulhun ce ma ta sa suka wuce salin-alin ba tare da sun far wa ƴansandan ba, haka su ma ƴansandan ba su farmake su ba.