Kafar Munich daya ta kai Quarter finals a Champions League

Asalin hoton, Getty Images
Mai rike da kofin Zakarun Turai, Bayern Munich ta doke Lazio da ci 4-1 har gida a wasan zagaye na biyu a Champions League ranar Laraba.
Jamal Musiala ya zama matashin dan wasan Ingila da ya zura kwallo a raga a Champions League a karawar da suka yi a Rome.
Mai shekara 17 da haihuwa kuma shi ne mai karancin shekaru a kungiyar ta Jamus da ya ci kwallo a gasar ta zakarun Turai a tarihi.
Robert Lewandowski ne ya fara cin kwallo kuma na 72 da ya zura a raga a gasar, ya zama na uku a jerin wadanda suka fi cin kwallaye a gasar ya haura Raul kenan.
Leroy Sane ne ya ci na uku sannan ya sa Lazio ta ci gida daga baya kungiyar ta Italiya ta zare daya ta hannun Joaquin Correa.
Bayern Munich wadda ta lashe kofi shida a wata tara baya ta barar da maki a gasar Bundesliga, tun bayan da ta lashe Club Wold Cup.
Kwallon da Lewandowski ya ci ya zama na uku a cin kwallaye a Champions League, bayan Cristiano Ronaldo mai 134 da kuma Lionel Messi mai 119 a raga.
Matashin dan kwallon Ingila da ya zura tamaula a raga a Champions League a tarihi a baya shi ne Alex Oxlade-Chamberlain - wanda ya ci wa Arsenal kwallo a karawa da Olympiakos.
Ya yi wannan bajintar cikin watan Satumba 2011 a lokacin yana da shekara 18 da kwana 44.
Wannan ne karon farko da Lazio ta kai wasan zagaye na biyu a Champions League tun bayan shekara 21.
Bayern Munich za ta karbi bakuncin Lazio a wasa na biyu ranar 17 ga watan Maris.










