Lionel Messi ya kamo tarihin Pele na cin ƙwallaye

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Argentina Lionel Messi ya kamo tarihin da Pele ya kafa na cin kwallo 643 a kungiya daya, bayan kwallon da ya ci wa kungiyarsa ta Barcelona a wasan da ta buga da Valencia ranar Asabar.
Messi ya buga wa Barcelona da ke Sifaniya wasanni a kaka 17 da ya yi, tun bayan fara wasansa a 2004.
Gwarzon dan wasan Brazil ya fi kowa yawan cin kwallaye a kungiyar Santos a kaka 19 da ya buga da kungiyar.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Messi na cikin manyan 'yan wasan duniya da suke haskakawa sama da shekara 10 a jere, tare da takwaransa na Juventus Cristiano Ronaldo.
Sai dai a wannan kakar Messi na fuskantar koma baya na rashin kokarin kungiyarsa ta Barcelona wadanda wasu ke dora alhakin hakan a kan shi.
Hakan na da alaka da rikicin da ya fuskanta a baya da kungiyar kan cewa sai ya sauya sheka, inda La Liga da Barcelona suka sanya sharudan abin da za a biya kafin tafiyarsa.
Sharadin kuwa shi ne dole duk kungiyar da ke son sayensa ta biya euro miliyan 700 kudin darajar dan wasan.
Mafi yawan kungiyoyi sun ce ba za su iya cika sharadin ba lamarin da ya sa Messi ya fasa barin kungiyar a watan Agustan da ya wuce.











