Lewandowski ne gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2020

Asalin hoton, Getty Images
Dan wasan Bayern Munich da tawagar Poland, Robert Lewandowski ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na duniya na Fifa na 2020.
Dan wasan ya yi takara ne tare da dan kwallon tawagar Portugal da Juventus, Cristiano Ronaldo da kuma Lionel Messi na Barcelona da tawagar Argentina.
Dan kasar Poland ya ci kwallo 35 a wasa 47 a bara da hakan ya taimaka wa Bayern Munich ta lashe kofi uku a kakar da ta wuce.
Lewandowski, mai shekara 32, shi ne ya zama kan gaba a cin kwallaye a Bundesliga da kofin kalubale da na Champions League a bara.
Wannan ne karon farko da Lewandowski ya lashe kyautar da ya takara da dan kwallon Barcelona. Messi da na Juventus, Cristiano Ronaldo.
Dan kasar Poland ya dora a bana kan kwazon da ya yi a kakar da ta wuce, wanda ya ci kwallo 16 a wasa 14 da ya yi wa Bayern Munich.
Kocin tawagogin kwallon kafa da kyaftin-kyaftin na mambobin Fifa ne ke yin zaben da kuma ta yanar gizo da 'yan jarida 200.
Ga jerin sauran kyaututtukan da aka lashe:
Lucy Bronze ta lashe kyautar gwarzuwar 'yar wasan tamaula
'Yar kwallon Manchester City da tawagar Ingila, Lucy Bronze ta lashe kyautar macen da ba kamarta a kwallon kafa a 2020.

Asalin hoton, BBC Sport
Wadanda suka yi takara:
Lucy Bronze (Manchester City da Ingila)
Pernille Harder (Chelsea da Denmark)
Wendie Renard (Lyon da France)
Jurgen Klopp shi ne kocin kungiyar kwallon kafa ta maza da ya yi fice
Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya lashe kyautar karo na biyu a jere.

Wadanda suka yi takara:
Jurgen Klopp (Liverpool)
Marcelo Bielsa (Leeds)
Hans-Dieter Flick (Bayern Munich)
Sarina Wiegman ita ce macen da ba kamarta a horar da kwallon kafar mata
Sarina tana horar da tawagar kwallon kafar Netherlands.

Asalin hoton, BBC Sport
Wadanda suka yi takara:
Emma Hayes (Chelsea)
Jean-Luc Vasseur (Lyon)
Sarina Wiegman (Netherlands)
Son Huen-min shi ne ya lashe kyautar kwallon da aka ci mafi kayatarwa
Dan wasan Tottenham, Son Heung-min ne ya lashe kyautar Puskas, sakamakon kwallon da ya ci Burnley.

Asalin hoton, BBC Sport
Wadanda suka yi takara:
Son Heung-min (Tottenham v Burnley)
Luis Suarez (Barcelona da Mallorca)
Giorgian de Arrascaeta (Flamengo da Ceara)
Manuel Neuer ya lashe golan da ba kamarsa a 2020
Mai tsaron ragar Bayern Munich, Germany, Manuel Neuer shi ne golan da ba kamarsa a 2020.

Asalin hoton, BBC Sport
Wadanda suka yi takara:
Alisson (Liverpool da Brazil)
Manuel Neuer (Bayern Munich da Jamus)
Jan Oblak (Atletico Madrid da Slovenia)
Sarah Bouhaddi ta zama mace mai tsaron raga da tayi fice a 2020
Mai tsaron ragar Lyon da tawagar Faransa, Sarah Bouhaddi ta zama mace mai tsaron raga da ta yi fice a 2020.

Asalin hoton, BBC Sport
Wadanda suka yi takara:
Christiane Endler (Paris St-Germain da Chile)
Alyssa Naeher (Chicago Red Stars da Amurka)
Sarah Bouhaddi (Lyon da Faransa)
'Yan kwallon Fifa 11 da ba kamarsu a filin tamaula

Asalin hoton, BBC Sport
Alisson da Alexander-Arnold da Van Dijk da Ramos da Davies da Kimmich da De Bruyne da Thiago da Messi da Lewandowski da kuma Ronaldo.











