Watakila a dakatar da Cabani daga buga wasa uku

Edison Cabani

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

An tuhumi Edison Cabani kan rubutun da ya yi a kafarsa ta sada zumunta da harshen Spaniya da aka ce cin mutunci ne a wata fassarar.

Daga baya Cabani, mai shekara 33, ya goge rubutun da ya yi, ya kuma nemi afuwa, bayan da aka nusar da shi fassarar abinda ya rubuta.

Hukumar kwallon kafar Ingila za ta iya dakatar da Cabani daga buga wasa uku da zarar ta sameshi da laifi.

Cabani tsohon dan kwallon Paris St-Germain ya koma United da taka leda a cikin watan Oktoba a matakin wanda bai da kungiya.

FA ta fitar da bayani tare da tuni kan dokar da aka amince da ita, ta kuma kara da cewar an zargi rubutun nasa da ''cin mutunci ko zagi ko bai dace ba ko zai kawo tsaiko a lokacin tamaula''.

Ta kuma kara da cewar kalaman da ya rubuta ya saba dokar da ta shafi fadin albarkacin baki kan kabila ko launin fatar jiki''.

An bai wa Cabani zuwa ranar Litinin 4 ga watan Janairu, domin ya kare kansa.

United ta ce za ta amince da hukuncin da hukumar za ta dauka, amma ta ce rubutun da dan wasan ya yi da kyakkayar niya ya yi.

United ta kuma ce ba ta goyon kalaman wariya kona cin zarafi.