Pogba zai ci gaba da zama a Old Trafford zuwa karshen kakar bana

Asalin hoton, Getty Images
Watakila Paul Pogba zai ci gaba da taka leda a Manchester United, domin da kyar a kammala cinikinsa a Janairu in ji wakilinsa a fanni tamaula.
A baya can Mino Raiola ya ce dan kwallon tawagar Faransa mai shekara 27 bai jin dadin taka leda a Old Trafford, ya kamata ya sauya kungiya.
Sai dai Pogba ya bayyana irin kwazon da zai ci gaba da sawa a kungiyar, bayan da aka dunga caccakar kalaman wakilinsa.
Raiola ya taba sanar da cewar Pogba na son barin United da zarar an bude kasuwar saye da sayar da 'yan kwallo, amma ya kara da cewar ''Ina magana kan kasuwar badi.
''Da wuya kaga manyan kungiyoyi na cinikayyar fitattun 'yan wasa a watan Janairu. Bari muga abinda zai faru bayan kammala kakar bana.''
Pogba wanda kwantiraginsa zai kare a karshen kakar 2022 a United - ya kasa taka rawar da ta kamata a Old Trafford tun bayan da ya koma Ingila kan fam miliyan 89 daga Juventus a 2016.
Dan kasar Faransa ya ci kwallo 35 a wasa 172, sai dai United ta kasa lashe kofi tun 2016-17 lokacin da ta dauki EFL da kuma Europa League.
Pogba ya buga wasa shida da aka fara da shi daga 11 da ya yi a Premier League ta bana da cin kwallo biyu, ya kuma yi sanadin fenariti biyu da aka ci Manchester United.











