Kasuwar cinikin 'yan ƙwallon ƙafa: Makomar Alli, Isco, Zidane, Khedira, Rondon, Depay, Dybala,

Asalin hoton, Getty Images
Everton na shirin dauko Dele Alli, dan wasan tsakiya mai shekara 24 na Tottenham Hotspur damar komawa can amma amatsayin dan aro a watan Janairu. (Star)
Dan wasan tsakiya na Juventus Sami Khedira mai shekara 33 na sha'awar barin kungiyar a watan Janairu, har ya tabbatar sun tattauna da kocin Everton Carlo Ancelotti. (Bild - in German)
Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya ce dan wasan Sfaniya Isco ba ya cikin wadanda ya ke son yin aiki da su nan gaba. Amma dan wasan mai shekara 28 na shirin komawa watan kungiyar a watan Janairu. (Marca - in Spanish)
Salomon Randon dan wasan gaba mai shekara 31 kuma dan Venezuela wanda a yanzu yake tare da kungiyar Dalian Pro ta China, na kan hanyarsa ta komawa Wolves domin maye gurbin Raul Jimenez saboda raunin da ya samu. (Sun)
Paris St-Germain na iya dauko Memphis Depay daga Lyon a watanni masu zuwa amma Barcelona ta dade tana sha'awar daukan dan wasan mai shekara 26. (Le Parisien - in French)
Tottenham a shirye ta ke ta biya Juventus fam miliyan 63.6 kan dan wasan gaba Paulo Dybala. (TodoFichajes - in Spanish)
Dan wasan tsakiya na Lyon da Faransa, Houssem Aouar mai shekara 22 Arsenal ta dade tana sha'awar shi, an kuma ce Paris St-Germain ma na daf da fara tattaunawa. (RMC - in French)
Leeds da West Ham na cikin kungiyoyi da ke sha'awar daukan Mathew Sorinola dan wasan baya mai shekara 19 daga MK Dons, (Teamtalk)











