Benzema ne kan gaba dan kasar waje a buga wa Madrid wasanni

Asalin hoton, Real Madrid FC
Dan wasan tawagar Faransa, Karim Benzema shi ne kan gaba dan kasar waje da ya buga wa Real Madrid wasa 528.
Dan wasan ya ci gaba da rubuta sunansa a kundin tarihin Real Madrid, bayan da ya buga wasan hamayya da Atletico Madrid ranar Asabar.
Real ce ta yi nasara a kan Atletico da ci 2-0 a gasar cin kofin La Liga kuma wasa na 528 da ya yi, ya haura Roberto Carlos mai 527 a matakin dan kasar waje da ya buga wasanni da yawa a kungiyar.
Benzema ya koma Real Madrid da taka leda a 2009, yanzu yana kakar tamaula ta 12.
Kawo yanzu ya lashe Champions League hudu da Club World Cups hudu da UEFA Super Cups uku da La Liga uku da Copa del Rey biyu da kuma Spanish Super Cups uku.
'Yan wasan kasar waje da suka buga wa Real wasa sama da 500, bayan Benzema da kuma Roberto Carlos, sai Marcelo da ya yi 515.
Shi kuwa Cristiano Ronaldo wasa 438 ya buga, yayin da Alfredo Di Stéfano ya yi wa Real Madrid fafatawa 396.
'Yan kwallon da aka yi nasara da su a fafatawa sun hada da Benzema a mataki na daya mai 358.
Wasa 352 aka ci da Cristiano Ronaldo a Real Madrid a matsayin dan kwallonta daga kasar waje, sai Roberto Carlos da aka yi nasara da shi a karawa 301.











