Kasuwar ‘yan kwallon kafa: Makomar Alaba, Emerson, Gattuso, Neymar, da Sarri

Paul Pogba

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Dan wasan baya na Bayern Munich David Alba na iya komawa Real Madrid, wani yunkuri da wakilinsa Pini Zahavi ke yi inda Inter Milan ma ke sha'awar sayen dan kasar Austrian mai shekara 28. (Calciomercato - in Italian)

A kakar wasa mai zuwa AC Milan na son sayo Emerson dan wasan Barcelona da Brazil wanda a yanzu an bayar da aronsa ne a Real Betis. (Todofichajes - in Spanish)

Neymar ba ya bukatar komawa Barcelona,kuma dan wasan gaba dan Brazil din mai shekara 28 ya ce yafi son yayi zamansa a Paris St-Germain. (AS - in Spanish)

Koci Gennaro Gattuso na Napoli ya bayyana cewa marigayi tauraron fim din James Bond Sean Connery, wanda ya mutu ranar Asabar, ya taba kokarin hana shi barin Rangers yayin da dan Italiyar ke buga wasa a can. (Sky Sports)

Tsohon kocin Chelsea Maurizio Sarri shi ne ke kan gaba cikin masu horarwa da Fiorentina ke bukata domin maye gurbin koci Beppe Iachini da za su iya kora. (Calciomercato)

Masu kula da Gasar Firimiya na fuskantar matsin lamba doin su yi watsi da tsarin nan na a biya a kalla dangane da wasanni kwallon kafa yayin kullen korona da ke tafe a Ingila. (Sun)

Gabriel Jesus dan wasan Brazil mai shekara 23 ya saki wani hotonsa da yake atisaye da abokan wasansa na Manchester City yayin da ake sa ran zai koma buga wasanni. (Manchester Evening News)

Kungiyar Wolves na shirin sayo dan wasan baya na Ingila da Middlesbrough, Djed Spence mai shekara 20 a watan Janairu. (Teamtalk via Birmingham Mail)