Filip Stevanovic: Man City za ta dauki dan wasan Partizan Belgrade

Asalin hoton, Getty Images
Dan kwallon tawagar Serbia, Filip Stevanovic zai koma taka leda a Manchester City a watan Janairu in ji kungiyarsa Partizan Belgrade.
Stevanoci, mai shekara 18 ya ci kwallo 12 a wasa 54 da ya yi wa Partizan, tun lokacin da ya fara taka mata leda a Disambar 2018.
A kakar 2019-20 dan kwallon ya taka rawar gani mai kyau da ta kai ya zura kwallo tara a raga ya kuma buga gasar Zakarun Turai ta Europa League.
Partizan ta ce sayar da dan wasan ''ga daya daga babbar kungiyar tamaula a Turai na nuna namijin kokari da aiki tukuru'' da kungiyar ta Serbia ta sa a gaba.
''FK Partizan na farincikin sanar da cinikin Filip Stevanovic zuwa Manchester City a watan Janairu.'' kamar yadda kungiyar ta bayyana.
Sai dai har yanzu Manchester City ba ta ce komai ba kan batun.







