Asamoah Gyan: Ya koma Legon Cities ta Ghana da taka leda

Asalin hoton, BBC Sport
Tsohon kyaftin din tawagar kwallon kafa ta Ghana, Asamoah Gyan, mai shekara 34 ya koma kasarsa da taka leda.
Hakan na da nasaba da fatan bunkasa wasannin gasar kasar da kuma na Afirka.
Gyan wanda shi ne kan gaba a ci wa Black Stars kwallaye a tarihi mai 51 a raga, ya koma Legon Cities kan kwantiragin shekara daya, za kuma a iya tsawaitata nan gaba.
Tsohon gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC, ya ki amincewa da tayi daga kungiyoyin Qatar da sauran wurare, domin ya buga gasar kwallon kafa ta Ghana.
Kungiyar da Gyan ya taka leda a Ghana ita ce Liberty Professionals, wacce ya bari a 2003 ta zamar masa tsani a buga wasa a Italiya da Faransa da Ingila da Turkiya da China da kuma Hadaddiyar daular Larabawa.
Cikin sana'arsa ta tamaula, Gyan, ya ci kwallo da dama musamman a gasar kofin Afirka, ya kuma zama dan Afirka da ya ci kwallo shida kuma na daya a wannan bajintar a tarihin gasar kofin duniya.






