Raheem Sterling ya yi kiran a samu ƙarin koci baƙaƙen fata a kwallon Ingila

Asalin hoton, PA Media
Dan wasan Manchester City, Raheem Sterlin ya ce ci gaba da za a samu a kwallon kafar Ingila ya hada da a samu ƙarin koci bakaken fata a kasar.
Dubban mutane ne ke zanga-zanga a Birtaniya kan kisan da aka yi wa bakar fata George Floyd a Amurka ranar 25 ga watan Mayu.
Sterling -- dan kwallon tawagar Ingila -- ya ce "Zanga-zangar tana da kyau kuma hanya ce da ake bayyana bacin rai".
Ya kara da cewar "sai an kara tashi tsaye wajen yakar wariyar launin fata, bayan yin zanga-zanaga".
Sterling ya ce ya kamata a samu masu horar da kwallon kafa a Ingila bakaken fata da wasu daga Asia da kananan kabilu a harkar jagorancin kwallon kafa har da aikin koci-koci da ya kamata a bai wa tsofaffin 'yan kwallo.
Ya bayar da misali da Lampard wanda yake horar da tamaula a Chelsea da Steven Gerrard kocin Rangers da ya ce fararen fata ne, yayin da bakaken fata da ke irin aikin sun hada da Sol Campbell da kuma Ashley Cole.
Cambell ya horar da kwallon kafa a Macclesfield da kuma Southend masu buga karamar gasar Ingila, shi kuwa Cole yana jan ragamar matasan Chelsea 'yan shekara 15 ne, bayan da ya yi ritaya.
Sterling ya ce da akwai 'yan wasan da ke buga gasar Premier sama da mutun 500 kuma kaso uku daga ciki bakaken fata ne, amma babu wakilci a harkar koci a Ingila.











