Enyimba ta doke Wikki a kwantan Firimiya

Nigerian Premier League

Asalin hoton, NPFL

An wallafa

Enyimba International ta yi nasarar doke Wikki Tourist da ci 3-0 a kwantan wasan Firimiyar Najeriya da suka fafata ranar Laraba.

Enyimba ta fara cin kwallo ta hannun Stanley Dimgba daf da za a je hutu a gumurzun da suka yi a Aba.

Bayan da kungiyoyin suka koma zango na biyu ne Enyimba ta kara na biyu ta hannun Austin Oladapo sannan Victor Mbaoma ya ci na uku.

Usman Abdallah tsohon kocin Enyimba shi ne ya ja ragamar Wikki zuwa Aba, inda ta yi rashin nasara.

A cikin watan Janairu Enyimba da Abdallah suka raba gari, inda ta maye gurbinsa da Fatai Osho.

Ita kuwa Rangers International cin Jigawa Golden Stars ta yi 1-0, kuma Dauda Madaki ne ya ci kwallon saura minti 20 a tashi daga karawar.

Daya kwantan wasa da aka buga tsakanin Akwa United da Dakkada 2-2 suka tashi.

Sakamakon kwantan wasannin da aka buga ranar Laraba:

  • Rangers 1-0 Jigawa Golden Stars
  • Enyimba International 3-0 Wikki Tourist
  • Akwa United 2-2 Dakkada