Yadda cutar kwalara ta yi ɓarna a jihar Borno

Ƙungiyar agaji ta likitoci Médecins Sans Frontières (MSF), wadda aka fi sani da 'Doctors Without Borders', ta ce cutar amai da gudawa ta kama dubban mutane tare da ƙara matsin lamba kan cibiyoyin kiwon lafiya a jihar Borno da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Ƙungiyar ta sanar da cewa aƙalla "mutum 74 ne suka mutu, yayin da wasu 7,850 da ake zargin sun kamu da cutar" a jihar tun farkon watan Mayu.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta ce cutar ta bazu a ƙananan hukumomi 14 da kuma unguwanni 50.
A cewar ƙungiyar, adadin majinyatan da ke buƙatar kulawar gaggawa na ƙaruwa tun bayan da aka samu rahoton ɓullar cutar ta farko a ranar 1 ga watan Mayu.
Ba wannan ne karon farko da wannan cuta ke ɓarkewa a jihar Borno cikin ƴan shekarun nan ba, amma ɓarnar da ta ke yi a wannan karon yana matuƙar tayar da hankali.
Cibiyoyin kiwon lafiya na fuskantar barazana

Asalin hoton, MSF/FB
Ƙungiyar likitoci ta MSF, ta ce a farkon watan mayu ta haɗa hannu da gwamnatin jihar wurin buɗe wata cibiyar kula da waɗanda suka kamu da cutar a yankin Ngarannam, a Maiduguri babban birnin jihar.
Tun daga wannan lokacin, yawan majinyatan da take karɓa ya karu cikin sauri, wanda ya tilasta ƙara yawan gadajen da ke cibiyar daga 121 zuwa 271.
Ta ƙara da cewa MSF buɗe sabon sashin kula da cutar kwalara mai gadaje 20 (CTU) a yankin Dalaram na birnin Maiduguri.
MSF ta ce ta yi jinyar waɗanda suka kamu da cutar ta kwalara guda 7,439 a cibiyoyinta, inda ta ce ta na karɓar aƙalla marasa lafiya 185 a kowace rana.
Ta ƙara da dewa a ranar juma'ar da ta gabata ta karɓi marasa lafiya 500, wanda shi ne mafi yawa da aka samu tun da aka tabbatar da ɓullar cutar.
Cutar kwalara ta kasance cikin cututtuka masu yaɗuwa a Najeriya, inda wani babban kaso daga cikin al'ummar ƙasar ke fama da matsalar rashin tsaftataccen ruwan sha.
Lamarin cutar yana ƙamari a jihar Borno, inda a Maiduguri, babban birnin jihar, ke fama da cunkoson al'umma sai da kuma al'ummomin yakunan karkara ke fama da rashin cibiyoyin lafiya.
BBC ta yi ƙoƙarin ji daga bakin hukumomin jihar kan matakin da suke dauka, sai dai hakan ba ta samu ba.
Mece ce cutar kwalara?
Kwalara ƙwayoyin cuta ne da ke yaɗuwa ta hanyar ruwa, wadda ruwa ko abinci maras tsafta ke yaɗawa.
Kwalara na haifar da gudawa da amai, kuma tana saurin yin kisa idan har ba a ɗauki mataki a kan lokaci ba.
Waɗanda cutar ta yi wa tsanani za su yi fama da rashin ruwan jiki wanda zai kai ga haddasa babbar matsala kuma idan ba a yi gaggawar magani ba mutum na iya mutuwa.
A cikakken bayanin da hukumar yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Najeriya (NCDC) ta yi kan kwalara ta ce kusan mutum miliyan uku ke kamuwa da cutar duk shekara kuma tana kashe mutum 95,000 duk shekara a duniya.
Ana iya kamuwa da cutar ba tare da nuna wani alamu ba, amma kuma takan iya yin tsanani.
Alƙalumman NCDC sun nuna cewa mutum ɗaya cikin 10 da suka kamu da cutar kwalara za ta iya yin tsanani da nuna alamu na amai da gudawa sosai da kuma mutuwar jiki.

Asalin hoton, MSF/FB
Mutum na iya kamuwa da cutar kwalara ta hanyar shan gurɓataccen ruwa ko abinci.
Kuma a lokacin annobar, wanda ya harbu na iya ƙara gurɓata ruwa da abinci.
Cutar kuma na iya bazuwa cikin sauri a yankunan da ba a ɗauki matakan tsaftace ruwan sha da magudanan ruwa ba.
Sai dai kuma Hukumar CDC ta ce yana da wahala cutar ta yaɗu daga wani mutum zuwa wani, don haka mu'amula da wanda ya kamu da kwalara ba ya cikin hatsarin kamuwa da cutar matuƙar za a ɗauki matakin wanke hannu yadda ya kamata.
Mutanen da ke rayuwa a wuraren da babu ruwa mai tsafta da rashin tsaftar muhalli sun fi hatsarin kamuwa da kwalara.
Alamomin kwalara
- Alamomin kwalara sun haɗa da:
- Gudawa (ba-haya mai ruwa sosai)
- Amai
- Rashin ƙarfin jiki
- Ƙishin ruwa
- Zazzaɓi
- Jiri
Hanyoyin kare kai daga cutar kwalara
Kamar yadda Hukumar daƙile yaɗuwar cutuka ta Najeriya ta bayyana, hanyoyin kare kai daga kamuwa da kwalara su ne:
- Shan ruwa mai tsafta
- Tsaftace muhalli
- Zubar da shara a wurin da ya kamata
- Tsaftar jiki ta hanyar wanke hannu da sabulu da ruwa mai gudana
- Ƙaurace wa shan kayan zaƙi (Zoɓo ko Jinja) da babu tabbas kan tsaftar su
- Ƙaurace wa shan kayan marmarin da ake sayarwa a kan titi ba tare da rufewa ba, musamman waɗanda aka fere kamar kankana da abarba
- Guje wa cin abincin da ba a dafa yadda ya kamata ba











