Kano Pillars ta yi wasa 13 a jere ba a doke ta ba

Asalin hoton, Pillars Fans
A ranar Lahadi kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta doke Adamawa United da ci 2-0 a wasan mako na 18.
Hakan ya sa kungiyar ta Kano ta yi wasa 13 a jere ba tare da an doke ta ba a gasar cin kofin Firimiyar Najeriya ta bana.
Rabon da aka doke Pillars tun ranar 20 ga watan Nuwamba, inda Jigawa Golden Stars ta yi nasara da ci 1-0.
Pillars wadda ta buga wasa 16 tana ta takwas a teburi da maki 24, inda ta ci karawa biyar da canjaras tara da rashin nasara biyu.
Kawo yanzu Kano Pillars ta ci kwallo 18 inda aka zura mata guda tara a raga.
Kwantan wasannin da kungiyar ta Kano keda su shi ne da Enugu Rangers da kuma Enyimba, wadan da suke buga gasar Zakarun Afirka ta Confederation.
Wasanni 12 da Pillars ta jera ba a doke ta ba:
- Kano Pillars 0- 0 Wikki Tourists
- Plateau United 0 : 0 Kano Pillars
- Kada City 1-2 Kano Pillars
- Kano Pillars 6-1 Kwara United
- Nasarawa 0-0 Kano Pillrs
- Heartland 1-1 Kano Pillars
- Kano Pillars 1 - 0 Ifeanyi Ubah
- Kano Pillars 1 : 1 Warri Wolves
- Abia Warriors 0 : 0 Kano Pillars
- Katsina United 1 : 1 Kano Pillars
- Kano Pillars 2 : 0 Akwa United
- Sunshine Stars 2 : 2 Kano Pillars
- Kano Pillars 2 : 0 Adamawa United
Wasannin mako na 19
Lahadi 9 ga watan Fabrairu
- Enyimba International da Abia Warriors
- Lobi Stars da Wikki Tourists
- Sunshine Stars da Ifeanyi Ubah
- Adamawa United da Heartland
- Akwa United da Enugu Rangers International
- Jigawa Golden Stars da Nasarawa United
- Katsina United da Warri Wolves
- Mountain Of Fire And Miracles da Kano Pillars
- Rivers United da Kada City
- Akwa Starlets da Plateau United










