FA Cup: Man City ta kai zagaye na biyar

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta kai karawar zagaye na biyar a gasar FA Cup bayan da ta doke Fulham da ci 4-0 ranar Lahadi.
City mai rike da kofin bara ta zama ta farko cikin manyan kungiyoyin Turai da ta ci kwallo 100 a kakar da muke ciki.
Tun farko Raheem Sterling da Jesus sun barar da fenariti kafin daga baya Ilkay Gundogan ya buga ya ci kuma ta farko da City ta zura a raga.
Daga baya ne Bernardo Silva ya kara ta biyu sannan kuma Gabriel Jesus ya ci biyu a fafatawar.
A ranar Litinin za a raba jadawalin zagaye na biyar, a lokacin ne City za ta san abokiyar da za ta kara da ita.
City wadda take ta biyu a teburin Premier da tazarar maki 16 tsakaninta da Liverpool ta daya a teburi na fatan lashe kofi uku a bana.
Kungiyar tana buga gasar Zakarun Turai ta Champions League, sannan tana cikin gasar League Cup da take rike da shi.







