Ana alakanta Cavani zai koma Chelsea

Asalin hoton, Getty Images
Kocin Chelsea, Frank Lampard ya ce Edison Cavani gogaggen dan wasa ne, bayan da ake alakanta cewar zai koma Ingla da wasa.
Chelsea za ta iya sayen dan kwallo a watan nan na Janairu, bayan da aka rage mata hukuncin daukar 'yan kwallo.
A karshen kakar nan kwantiragin Cavani zai kare a Paris St Germain, ta kuma bukaci ya matsa, bayan da Atletico ta yi tuntuba.
Cavani wanda ya koma PSG daga Napoli kan fam miliyan 55 a 2013, ya ci kwallo 198 a wasa 292 da ya yi a Faransa, amma kwallo hudu ya ci kawo yanzu a karawa 14 a bana.
Tammy Abraham, mai shekara 22, shi ne mai ci wa Chelsea kwallo da take da shi, bayan da ake sa ran Olivier Giroud zai bar Stamford Bridge a Janairun nan.
Ana kuma alakanta Cavani da Manchester United wanda ya ci kwallo 351 a wasa 577 da ya buga wa kungiyoyi da kuma 50 da ya zura a raga a tawagar kwallon kafar Uruguay wadda ya yi wasa 116.







