Ya kamata United ta hada kai — Solskjaer

United

Asalin hoton, Reuters

An wallafa

Ole Gunnar Solskjaer ya bukaci 'yan wasan Manchester United su zama tsintsiya madauri daya, bayan da magoya baya suka nuna fushinsu ranar Asabar.

Magoya bayan United sun nuna bacin ransu ga mai kungiyar da kuma jami'i, Ed Woodward kan yadda abubuwa ke tafiya a kungiyar.

Manchester United ta yi nasarar doke Norwich 4-0 a gasar Premier da suka yi a Old Trafford karawar mako na 22..

Magoya bayan da suke wajen zama na Stretford sun yi ta rera wakar cewar ba sa kaunar zaman Glazer da kalaman rashin kyautawa ga Woodward.

Solskjaer ya ce ya tabbatar 'yan wasa sun ji duk abin da ake fada, amma bana son ya shiga ransu.

Kalaman rashin kyautawar da aka dunga yi ya watsu zuwa wasu sassan 'yan kallo inda daga ko ina ana jin me ake cewa.

Kocin na United ya kara cewar shugaban kungiyar da Woodward suna goyon bayansa da 'yan wasa, saboda haka ya kamata su hada kansu.

A lokacin da aka ci kwallo na uku ne magoya bayan United suka bayyana fushinsu a minti na 54, kuma wannan ba shi ne karon farko da suke hakan ba.

A watan Octoba kafin wasanm da United ta yi da Liverpool, magoya bayan Manchester sun yi rubuce-rubuce na rashin kyautawa ga shugabanin kungiyar.

Doke Norwich da United ta yi shi ne na farko a wasa hudu da ta buga, bayan da Arsenal ta yi nasara a kanta a gasar Premier.