Premier League: Arsenal ta sake barar da damarta

Arsenal vs Wolves

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Karo biyu kenan a jere Arsenal na gaza cin wasa bayan ta fara jefa kwallo
An wallafa

Wani sabon makon ya wuce ya bar Arsenal da barar da nasarar da ta yi a kan Wolves a filin wasa na Emirate.

Pierre-Emerick Aubameyang ne ya bai wa Arsenal nasara tun a minti na 21 bayan an bar shi ba tare da wani tsaro ba, inda ya ci kwallonsa ta 50 ga Arsenal.

Sai a minti na 76 ne Raul Jimenez ya farke wa Wolves tare da taimakon Joao Moutinho.

Wannan dai kusan maimaici ne na abin da ya faru a makon da ya gabata, inda Arsenal din ta kasa cin wasa bayan ta zira kwallo biyu a ragar Crystal Palace.

Wolves tana mataki na 11 daga maki guda dayan da ta samu, yayin da Arsenal take a mataki na biyar.