An cire wa Messi takunkumin yi wa Argentina kwallo

Asalin hoton, AFP
Sunan Lionel Messi na cikin tawagar 'yan wasan Argentina da za su buga wasa da Brazil da Kuma Uruguay a wata mai kamawa, bayan dakatarwar wata uku da aka yi masa daga buga wa kasarsa wasanni.
Dan wasan gaban Barcelonan mai shekaru 32, an ba shi jan kati ne a wasan Agentina da Chile na neman matsayi na uku a gasar Copa America wanda kuma Chilen ta samu nasara kansu a ranar 6 ga watan Yulin da ya gabata.
An dakatar da shi ne bayan ya yi ikirarin masu shirya gasar " 'yan rashawa ne".
Messi wanda ya ci wa Barcelona kwallo biyar a wannan kakar, wasannin hudu ne kawai bai buga wa Argentinan ba yayin dakatarwar.
Argentina za ta kara da Brazil a ranar 15 ga watan Nuwamba a Saudiya, ta kuma buga da Uruguay ranar 18 ga watan dai shi kuma a kasar Isra'ila.
Cikakkiyar tawagar
Masu tsaron raga: Agustin Marchesin, Juan Musso, Emiliano Martinez, Esteban Andrada
Yan baya: Juan Foyth , Renzo Saravia, Nicolas Otamendi, German Pezzella, Marcos Rojo, Walter Kannemann, Nicolas Taglafico, Nehuen Perez, Guido Rodriguez
Yan tsakiya: Giovani lo Celso, Leandro Paredes, Nicolas Dominguez, Rodrigo de Paul, Marcos Acuna, Roberto Pereyra, Lucas Ocampos
Yan gaba: Lionel Messi, Sergio Aguero, Nicolas Gonzalez, Lucas Alario, Lautaro Martinez, Paulo Dybala











