El Clasico: Hukumar La Liga za ta kai kara kotu

Wasan El Clasico

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Barcelona da Madrid za su hadu a karon farko a kakar wasannin bana
An wallafa

Hukumar shirya gasar La Liga na shirin kai kara kotu bisa matakin dage lokacin da za a buga wasan hamayya a tsakanin Barcelona da Real Madrid.

Hukumar kwallon kafar kasar Sifaniya ta bayyana cewa an dage wasan har sai ranar 18 ga watan Disamba.

Tun farko an tsara za a buga wasan mai zafi da ake yi wa lakabi da El Clasico a tsakanin ranar Asabar mai zuwa, to amma an dage wasan bisa dalilan tsaro a yankin Catalonia.

An dai shafe mako daya ana zanga-zanga a Barcelona bayan tsare shugabannin yan aware guda tara da ke fafutikar neman 'yancin Catalonia a farkon watan nan.

Shugabannin La Liga sun bukaci da a buga wasan a ranar 4 ga watan Disamba.

To amma kungiyoyin biyu sun zabi ranar 18 ga watan Disamba bayan da kwamitin da aka kafa ya bukaci jin ra'ayinsu.

A yanzu La Liga ta ce tana nazari kan dalilan amincewa da sabon lokacin buga wasan kafin su garzaya kotu da nasu dalilan na aminta da ranar 4 ga watan Disamba.

Tun da farko Barcelona da Real Madrid sun ki amincewa da buga wasan a birnin Madrid.

Yankin Catalonia yanki ne da ke cin kwarya-kwaryar gashin kansa a arewa maso gabashin Sifaniya.

A ranar 1 ga watan Oktoban 2017 ne aka jefa kuri'ar raba gardama, wadda Sifaniya din ta bayyana a matsayin haramtacciya, duk da kashi 90% na mazauna yankin sun jefa kuri'ar neman cikakken 'yanci.

Babbar kotun Sifaniya ta yanke wa shugabannin 'yan awaren na Catalonia hukuncin daurin shekara tara zuwa 13 bayan kama su da laifin kalaman tunzura 'yan kasa domin yi wa gwamnati bore.