Za a kori Solskjaer daga aiki, Real Madrid na shirin sayen Kante

Asalin hoton, Getty Images
Masu shahi sun zuba ido domin ganin an kori kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer daga aiki bayan United sun sha kashi a hannun Newcastle ranar Lahadi. Ana sa ran kocinTottenham Mauricio Pochettino ne zai maye gurbinsa. (Sun)
United sun aika da matasan 'yan wasansu domin kallon dan wasan Lyon dan kasar Faransa Moussa Dembele, mai shekara 23, yana murza leda ranar Lahadi. (Mail)
Kocin Arsenal Unai Emery na duba yiwuwar sayo dan wasan baya na Wolves Willy Boly. Da alama Wolves din za su bukaci a ninka a kan £10m da suka sayo dan wasan dan kasar Ivory Coast mai shekara 28 daga Porto idan ya nemi komawa Emirates Stadium. (Sun)
A shirye Real Madrid suke domin fafatawa da abokan hamayyarsu Juventus wajen zawarcin dan wasan Chelsea da Faransa N'Golo Kante. Madrid na iya sayen dan wasan mai shekara 28 a kan £70m. (Sport, via Mail)
Tsohon dan wasan Liverpool Glen Johnson ya yi kira ga dan wasan Tottenham mai shekara 26 dan kasar Ingila, Harry Kane, ya bar Livepool domin ya koma Manchester City. (Manchester Evening News)
Manchester United sun fasa sayen dan wasan tsakiya na Ajax Donny van de Beek bayan da aka ambato su da cewa suna shirin sayen dan wasan mai shekara 22 a kan £35m. (Mirror)
Tsohon dan wasan Liverpool Steve McMahon ya ce ya kamata kocin kulob dinJurgen Klopp ya sayo dan wasan Leicester City mai shekara22 James Maddison. (Stadium Astro, via Express)
Kocin Manchester United Ole Gunnar Solskjaer yana bukatar sayen karin 'yan wasa biyar idan har yana so kulob din ya dawo kan ganiyarsa, in ji tsohon kocin na Old Trafford Ryan Giggs. (Sun)
Kazalika tsohon dan wasan United ya yi kira ga kulob din ya sauke mataimakin shugaban kulob din Ed Woodward daga kan mukaminsa na kula da harkokin wasanni. (Metro)
Kocin Bournemouth Eddie Howe ya yi kira ga dan wasan Ingila Callum Wilson, mai shekara 27, ya yi watsi da rade-radin da ke alakanta shi da yiwuwar komawa Manchester United a watan Janairu. (Daily Echo)
AC Milan na daf da korar kocinsu Marco Giampaolo lokacin da aka tafi hutun rabin lokaci a wasan da suka doke Geona ranar Asabar. (SempreMilan)).











