Man Utd na son sayen Wilson, Capello ya so sayen Messi

Messi

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Dan wasan Bournemouth da Ingila Callum Wilson, mai shekara 27, da takwaransa na Juventus dan kasar Croatia mai shekara 33, Mario Mandzukic na cikin jerin manyan 'yan wasan da Manchester United ke son saya idan aka bude kasuwar musayar 'yan kwallo a watan Janairu, in ji (Sky Sports).

Mai yiwuwa burin dan wasan Tottenham da Denmark Christian Eriksen na komawa Real Madrid zai cika, a yayin da ake sa ran wakilin dan wasan mai shekara 27 zai yi balaguro zuwa Spain domin tattaunawa da jami'an kulob din da ke buga gasar Liga a karshen makon nan. (Star)

Tsohon kocin Chelsea Maurizio Sarri yana fatan ya sake haduwa da dan wasan gaba mai shekara 31 Willian a Juventus - sai dai kocin kulob din Frank Lampard ya ce dan kasar ta Brazil yana tattaunawa da jami'an Chelsea a kan sabon kwantaragi. (Calciomercato)

Dan wasan Real Madrid dan kasar Norway Martin Odegaard, mai shekara 20 - wanda kulob din Real Sociedad ya karbi aronsa- yana son dawowa Madrid a daidai lokacin da ake cewa Liverpool da Manchester United na son sayensa.(Goal)

Kulob din United ya barar da damar da ya samu ta sayen dan wasan Arsenal mai shekara 21, Gabriel Martinelli a bazara, inda dan wasan dan kasar Brazil ya zura kwallo hudu a wasa uku da ya buga wa Arsenal din. (Mirror)

Tsohon kocin Ingila Fabio Capello ya bayyana cewa ya yi kokarin karbar aron dan wasan Barcelona dan kasar Argentina Lionel Messi,mai shekara 32, lokacin da yake jagorancin Juventus. (Sky Sports Italia, via Mail)

Tsohon kocin Brighton Chris Hughton ya ki amsa tayin da aka yi masa na zama kocin Stoke City. (Mirror)

Inter Milan basu hada da kudin-kome ba a tattaunawar da suke yi da Manchester United a kan bayar da aron dan kasar Chile Alexis Sanchez saboda wasu kulob-kulob din na sha'awar aronsa abin da ya sa suke jin tsoro kada dan wasan mai shekara 30 ya ki amincewa da bukatarsu ta komawa can. (Calciomercato)

Real Madrid sun so bai wa Antonio Conte mukamin babban koci a bara, kafin tsohon kocin na Chelsea ya koma Inter Milan. (Fichajes.net, via Calciomercato)

Watakila kulob din Leicester City su nemi sayen dan kasar Turkiyya mai shekara 15 Burak Ince, wanda kuma Manchester City, Lille da Freiburg ke zawarcinsa. (Fotospor - in Turkish)

Tsohon dan wasan Arsenal Lukas Podolski, cikin raha, ya bayyana cewa ya kamata dan wasan Bayern Munich Serge Gnabry - wanda ya taba buga tamaula a Arsenal- ya zama gwarzon dan wasan Firimiya na na kulob din a watan nan, bayan dan wasan dan kasar Jamus mai shekara 24 ya zura kwallo hudu a ragar Tottenham Hotspur a gasar Zakarun Turai ranar Talata. (Mirror)