Newcastle ta kara jefa Man United cikin matsi

Man United

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa

Manchester United ta kara cin karo da koma baya a wasannin Premier bana, bayan da ta yi rashin nasara a hannun Newcastle United da ci 1-0 ranar Lahadi.

Matty Longstaff ne ya ci kwallon, kuma a karon farko da ya fara buga wa Newcastle wasan Premier, inda hakan ya sa kungiyar ta kara yin sama daga matakin 'yan karshe a kasan teburi.

Da wannan sakamakon Manchester United tana ta 12 a kasan teburin Premier da maki tara bayan wasa takwas da ta yi.

Ita kuwa Newcastle United tana ta 15 da maki takwas da tazarar maki daya tsakaninta da 'yan ukun karshe a teburin Premier.

Wannan ce kaka mafi muni da Manchester United ta hada maki tara a karawa takwas a gasar Premier tun bayan 1989/90.

Mai masaukin baki ta sayi dan wasa Joelinton mai wasan gaba kan fam miliyan 40 a bana, ita kuwa United ta dauko mai tsaron baya Maguire kan fan miliyan 80.

Sai dai dukkan 'yan wasan suna cin karo da koma baya, sakamakon kasa takarawar gani a kungiyoyin da suke yi wa tamaula.

Manchester United za ta karbi bakuncin Liverpool a wasan mako na tara ranar 20 ga watan Oktoba a Old Trafford.

Ita kuwa Newcastle United za ta ziyarci Chelsea ranar 19 ga watan Oktoba a Stamford Bridge a wasan mako na tara a Premier.