Man City vs Watford: An yi yagayaga da Watford a Etihad

Asalin hoton, Getty Images
Kwallo biyar rigis tun kafin hutun rabin lokaci ne suka bai wa Manchester City damar yin yagayaga da Watford kafin su zama 8-0, inda City din ta rage girman tazarar da ke tsakaninta da Liverpool a saman teburi.
City dai ta farafado ne daga abin mamakin da ya faru a karshen makon da ya gabata bayan Norwich ta lallasa ta da ci 3-2 a filin wasa na Carrow Road.
Bernardo Silva ne ya ci uku rigis yayin da tawagar Guardiola ta samu nasara mafi girma tun bayan ya kama aiki a kungiyar a 2016.
Man City ta bugi turke har sau biyu a wasan sannan kuma ta ci gaba da neman kari har zuwa usur din karshe.
Nasarar da City ta yi a kan Ipswich a shekarar 1995 da ci 9-0 ita ce mafi girma ga kungiyar a Premier.
Sannan kuma ita ce ta bakwai da ta taba cin wasa da kwallo takwas a babbar gasa a tarihin kwallon Ingila na baya-bayan nan.







