Trippier ya koma Atletico Madrid daga Tottenham

Kieran Trippier

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Kieran Trippier zai kasance dan Ingila na farko da zai buga wa Atletico Madrid a cikin shekara 95
    • Marubuci, Daga David Ornstein
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
  • An wallafa

Dan wasan baya na Ingila Kieran Trippier ya koma Atletico Madrid daga Tottenham kan fan miliyan 20.

Dan kwallon mai shekara 28, wanda ya koma Spurs daga Burnley a watan Yunin 2015 sannan ya buga wasa sama da 100, ya sanya hannu kan jarjejeniyar shekara uku.

Dama tuni ya bayyana cewa ba shi da tabbas ko zai kammala kwantiraginsa a Spurs, wacce ya kamata ta kare a shekarar 2022.

Trippier shi ne dan wasan baya na uku da Atletico ta dauka tun bayan bude kasuwar musayar 'yan wasa.

Tuni koci Diego Simeone ya dauki Felipe daga Porto da Renan Lodi daga Athletico Paranaense, sannan kuma Diego Godin ya koma Inter Milan.

Sun kuma dauki matashin dan wasan gaba na Portugal Joao Felix da Marcos Llorente daga Real Madrid.

Kawo yanzu sun kashe fam miliyan 170 kan sababbin 'yan wasa, sai dai su ma sun samu fam miliyan 107 bayan da suka sayar da Antoine Griezmann ga Barcelona.