Brazil ta fitar da Argentina a gasar Copa America

Asalin hoton, Getty Images
'Yan wasan gaba na Brazil Gabriel Jesus da Roberto Firmino ne suka zura kwallaye biyun da suka baiwa kasar nasara kan Argentina da ci 2-0 a wasan daf da karshe na Copa America.
Jesus ne ya fara bude raga a minti na 19 bayan da Firmino ya bashi kwallo.
Sergio Aguero da Lionel Messi sun kai munanan hare-haren da suka daki turken raga.
Kwallon da Firmino ya ci cikin sauki a minti na 71 ita ce ta tabbatar da nasarar, inda a yanzu za su kara da Peru ko Chile a wasan karshe.
Brazil ta samu nasara ne a filin wasa na Mineirao a birnin Belo Horizonte ina suka sha mummunan kashi a hannun Jamus da ci 7-1 a wasan daf da karshe na gasar kofin duniya ta 2014.

Asalin hoton, Reuters
Rabon Argentina da ta doke Brazil a babbar gasa tun 2005.
Rashin nasarar ta Argentina na nufin har yanzu Messi bai kai ga lashe kofi da babbar tawagar kasar ba.
Akwai alamun Lionel Messi zai ci gaba da taka leda a Argentina.









