Iyaye matan da dole su zaɓa tsakanin aikinsu ko kula da jariransu a Kenya

- Marubuci, Daga Evelyne Musambi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nairobi
- An wallafa
Sophy Saronge na jin kamar ta aikata ba dai dai ba.
Wata mata 'yar shekara 25 a Kenya ta koma bakin aiki, watanni uku bayan ta haihu, wanda sanadin hakan ba ta samu damar shayar da jaririyarta nonon uwa na tsawon watanni shida ba kamar yadda ƙwararru suka amince.
Matar wadda ƙwararriya ce kan nau'ukan abinci ta ce ba ta da zaɓi saboda iyalanta na matuƙar buƙatar kuɗi.
Ta ce, "Dole na koma aiki saboda mu rayu."
To amma an rinka ba ta shawarwari a kan cewa ta tafka kuskure domin ta yi wa 'yarta ba dai dai ba.
Jami'an lafiya a Kenya sun amince cewa dole a rinka shayar da jarirai nonon uwa zalla a farkon watanni shida na haihuwa.
Kazalika, gwamnatin kasar ta wajabta wa kamfanonin da ke samar da madarar jarirai su rinka tallatawa tare da nuna muhimmancin shayar da da jarirai nonon uwa a kayayyakinsu.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce bai wa jarirai nonon uwa zalla tsawon watanni shida na haihuwa, na kare yaran daga fuskantar ƙarancin abinci mai gina jiki, kuma nonon na aiki a matsayin riga-kafin farko da za ta kare jarirai daga dukkan wasu cututtuka da suka jiɓinci jarirai.
A takaice, Kenya na da yawan masu yawan shayarwa, inda kusan dukkan jariran da ake haifa ana shayar da su a tsawon lokacin da aka haife su.
To amma akwai kashi 60 cikin 100 na irin wadannan jariran da ake shayar da su nonon uwa zalla tsawon watanni shida.
Ms Saronge, ta ce "ala dole nake bai wa jaririyata madarar shanu duk da kasancewa ta ƙwararriya kan nau'ukan abinci, da kuma sanin lallai illa da ke tattare da hakan."
Yawancin madarar jarirai ana yinta ne madarar shanu inda ake sarrafata don ta yi wa jarirai daɗi.
Ms Sophy, ba ta da damar sayen madarar jarirai saboda tsadarta.
A tsawon watanni ukun da Ms Saronge ta dauka na hutun haihuwa, ba a biyanta albashi, kamar yadda ake yi wa sauran mata a Kenya, kuma ba ta da damar da wasu ma'aikatan ke da ita ta biyan kudi yayin haihuwa.
Akwai wadanda ke da wannan damar.
Ita kuwa Caroline Wairimu, mijinta na da hali saboda yana daukar albashi mai tsoka, don haka sai ta daina aiki bayan da ta haifi tagwaye.

Asalin hoton, Caroline Wairimu
Caroline Wairimu ta ce "Hanya mafi sauƙi ta za a ƙarfafa wa iyaye gwiwar shayar da jariransu nonon uwa zalla tsawon watanni shida shi ne a rinka biyansu albashi a tsawon waɗanan watannin."
A yanzu, iyaye sabbin haihuwa ne kaɗai waɗanda ke da takardar kwantiragi ta aiki ake biyan albashi a tsawon watanni uku na haihuwa.
Wata mai fafutuka Ruth Mumbi, ta ce gwamnati ba ta damu da batutuwan da suka shafi mata ba, don haka ne ba su damu da bai wa matan dogon hutun haihuwa ba.
Ma'aikatar ƙwadagon ƙasar dai ba ta cewa BBC komai ba kan kalaman mai fafutukar.
Yanzu ma'aikatar lafiyar kasar ta ce shirye-shirye sun yi nisa domin fara biyan iyaye mata da suka haihu cikakken albashi a tsawon watanni uku na haihuwa.
To amma gwamnatin a yanzu ba ta fara tunanin tsawaita watanni ba.
Wasu masu sharhi sun yi amanna cewa mahukunta na fuskantar turjiya sosai daga ma'aikata.
Shugaba Uhuru Kenyatta, ya gaza sanya hannu a kan wani kudurin doka da majalisar dokokin kasar da zartar a 2016, wanda zai wajabta samar da dakunan shayarwa a ma'aikatau da kamfanoni.
An sake gabatar da kudurin a 2019, amma har yanzu majalisar ba ta amince ba.
Aiwatar da wannan ƙuduri zai bai wa iyaye mata damar zuwa wajen aiki da mai taimaka musu da riƙon jaririyar, sannan kuma uwa za ta samu damar shayar da jaririnta ko da a wajen aiki.
Evelyne Mueni, uwa ce da ke kula ɗanta amma ba ta da miji, kuma ta dogara ne a kan ayyukan hannu don samu kudin shiga, ta ce dole ta koma aiki bayan ta haihu da wata daya.
Ta ce, "Dole na bar ƴata a wajen maƙwabciyata wadda ta ke ba ta madarar shanu ko koko da kunu, ina zuwa na yi wankau da gyaran gidan mutane don na samu kuɗin abinci da biyan haya."
Ms Kirogo ta ce iyaye matan da ake aiki a ma'aikatu ko kamfanoni ana ƙarfafa musu gwiwar su ci gaba da tatsar nonon da hannu a cikin gora sannan su sanya a waje mai sanyi tsawon awa takwas idan za su fita aiki don bai wa jariransu.
To amma ga Ms Mueni, ta ce ya fi mata sauƙi ta sayi madarar shanu saboda ba za ta iya tatsar nonon da zai ishi ƴarta ba.
Wani ƙwararre a kan lafiyar jarirai sabbin haihuwa Dakta Moses Lango, ya ce ba dai dai ba ne a yaye yaro da wuri duk da cewa cikakkiyar shayarwa ta tsawon watanni shida ta ishi jariri.
Ya ce akwai dalilai da jami'an lafiya ke bayar da shawara a kan yaye yaro, amma idan babu ƙwaƙƙwaran dalili gara a bar yaro ya sha ya ƙoshi saboda ya fi ƙara musu lafiya.
Hukumar Lafiya ta Duniya na kira da a rage yawan tallar madarar jarirai ta gwangwani, saboda tallar na janyo wasu iyaye su manta da bayar da nono su koma madarar gwangwani.
Kamar Kenya, Majalisar dokokin Laberiya ma ta zartar da kudurin doka da za ta taƙaita yawan tallace-tallacen madarar gwangwani da kuma ƙarfafa shayar da nonon uwa.
Namibiya kuwa a kwanan nan ta ƙara kudin hutu ga mata masu haihuwa.











