Indiya: Yadda maƙwabtakar masallaci da wurin bautar addinin Hindu ke rikiɗewa zuwa rikici

Asalin hoton, Robert Nickelsberg/Getty Images
A Varanasi, daya daga cikin tsofaffin birane a duniya, mabiya addinin Hindu da Musulmai suna gudanar da ibada a kusa da juna a matsayin wurin bauta da masallaci.
Ginin mai cike da matakan tsaro, ya kasance wurin takaddama mai cike da tarihi.
An gina Masallacin Gyanvapi, a wani fili da ainahi wurin bautar Vishwanath ne da aka lalata, wanda ya zama babban wurin bautar Hindu a karni na 16.
An lalata wurin bautar a shekarar 1669 bisa umarnin sarki Aurangzeb na shida na masarautar Mughal.
A yanzu wannan wuri ya zama cibiyar da ake takaddama akan mallakinta tsakanin mabiya addinin Hindu masu rinjaye da Musulmai da su ne tsiraru.
Gungun mabiya addinin Hindu sun shigar da kara a kotun yankin, inda suke bukatar a mallaka musu bayan masallacin da wasu wuraren a ciki domin su ma su dinga yin bauta.
Dokar kotun mai cike da ce-ce-ku-ce da ta ba da damar daukar bidiyon wurin bautar, ya tayar da ƙura sakamakon gano wani katon dutse mai dauke da adon abin bauta na Deity Shiva a tsakanin Hasumiyar masallacin guda biyu, wanda akai ikirarin shi ne ya kara tayar da kurar.
Bayan wannan, akwai wani bangaren na masallacin da kotu ta rufe ba tare da bai wa hukumomin masallacin damar halartar zaman kotun ba.
Takaddamar dai ta isa gaban kotun koli, kuma a ranar Talata kotun ta ce za a kare daukacin wurin, sannan za a ci gaba da yin sallah a masallacin.
Matakin ya ɗarsa ƙarin tsoron da aka kwashe gwamman shekaru ana yi kan batun da ya shafi dayan masallacin Babri, wanda 'yan dabar Hindu suka sauke shi a birnin Ayodhya mai tsarki a shekarar 1992.

Asalin hoton, Getty Images
Rushe ginin masallacin da aka dauki shekara shida ana gangamin yi karkashin jam'iyyar mabiya Hindu mai mulki ta BJP, wadda a lokacin take jam'iyyar adawa, ta janyo zanga-zangar da aka kashe kusan mutum 2,000.
A shekarar 2019, kotun koli ta yanke hukunci kan wurin da ake takaddama a Ayodhya a mika shi ga mabiya Hindu, wanda yanzu suke ginin wurin bauta. Sai aka bai wa musulmai wani filin na daban domin sake gina masallacin.
A shekarar 1991 wata doka da aka kira Places of Worship Act, ta yi watsi da mayar da wurin bautar da addinai ke zuwa ibada da aka samar ya saɓa wa doka.
An kuma sa ranar 15 ga watan Agusta 1947 wato tunawa da ranar 'yancin kai kotun ta zartar da hakan. Masu suka kan Varanasi sun ce wannan yi wa doka hawan kawara ne.
Fitaccen malamin addinin Musulunci Asaduddin Owaisi, ya ce "masallacin yana nan, kuma zai ci gaba da wanzuwa".
Shugaban jam'iyyar BJPa jihar Uttar Pradesh, inda Varanasi ya ke ya yi amanna da cewa babu wani abu a jikin dutsen.
"Gaskiya ta bayyana, za mu yi maraba da ci gaba da bin dokokin kotu," in ji mukaddashin ministan tsaro Keshav Prasad Maurya.
Babu karin bayani game da gaskiyar da ta bayyana, kamar yadda ya fada.
A karon farko an amince tabbas wurin bautar anan yake.
Kuma ''katon wuri ne mai fadi da tsawo, da gine-gine guda takwas kewaye da shi'', kamar yadda farfesa Diana L Eck, da ke nazarin addinai a Indiya a jami'ar Havard ta bayyana.

Asalin hoton, Robert Nickelsberg/Getty Images
An kuma samar da shi ne cikin kasa da shekaru 100, sarki Aurangzeb ne ya bada umarnin rusa wurin bautar," in ji Frfesa Eck.
"Rusau din rabi da rabi ne, kuma nan ne ya zama cibiyar da aka dasa ginin masallacin Gyanvapi".
An amince an gina masallacin ne akan rusasshen wurin bautar. Farfesa Eck ya yi karin bayanin "bangon daya daga cikin tsohon wurin bautar, ta na da muhimmanci ko a rushen da take, an kawata ta da hasumiyar da a yau ta zama ta masallaci.''
"Idan kana kallon masallacin daga nesa, haumiyar da ake takadddama akai na tsohon wurin bautar, da ginin yanzu".
Masana tarihi sun amince dalili guda da ya sa aka kai wa wurin bautar Aurangzeb, shi ne duk wanda ke shiga ciki a wancan lokacin sun kitsa tserewar wani makiyin masarautar Mughal wato sarkin Hindu Shivajiwanda ya yi fice a tsana da nuna kiyayya ga masarautar Mughal.

Asalin hoton, Getty Images
Mayakan Mughal sun rushe akalla wuraren bauta 14, lokacin mulkin Aurangzeb na shekaru 49, kamar yadda Farfesa Eaton da ya yi bincike kan misalai 80 kan wuraren bautar da aka lalata a Indiya tsakanin karni na 12 zuwa 18.
"Ba za mu iya sanin adadin wuraren bautar da aka lalata ko rushewa a tarihin Hindiya," in ji shi.
Duk da haka, masana tarihi sun san ana zuzuta wasu ikirari ne kawai, kan cewa sama da wuraren bauta 60,000 aka lalata karkashin mulkin Musulmai a Indiya.
Tarihi ba zai manta da mulkin turawa ba, wajen taka rawa a tashe-tashen hankulan da suka shafi addini da rusa majami'ai.
Idan muka dauki arewacin Turai, mun ga yadda aka dinga rushe majami'un mabiya darikar Katolika, lokutan zanga-zangar da ta barke a karni na 18.
Misali rushe majami'ar Utrecht Cathedral a shekarar 1566, ko wadda aka rusa ta St Andrews Cathedral da ke Scotland a shekarar 1559.

Asalin hoton, DeAgostini/Getty Images
Sai dai kamar yadda mai bayanin tafinta Pratap Bhanu Mehta ya fahimta, ya ce: "Jita-jita za ta yi tasiri matuka tare da tarihi ya maimiata kan shi, maimakon a ce tarihin ya zama wata fitila da za ta haska abin da ya faru a baya ba."
Takaddamar da ake yi akan Varanasi babu abin da za ta haddasa sai abin da ya kira "sabon rikicin al'umma".
Irin wannan damuwar da ake nunawa ba sa tasiri, in ji Swapan Dasgupta, mai makala a jaridun Indiya.
"Har yanzu akwai abin da ya rage ayi, amma babu wani bu da aka yi, bukatar rushe masallacin, da maida ainahin ginin wurin bautar Hindu, mataki neda gwamnati ya kamata ta yi nazarin tsanaki akai.
Haka kuma doka ba ta bada damar a rushe duk wani wurin bauatar addinai ba haka siddan,"abin da ya rubuta kenan.
"Abin da muke gani a wurin bautar da ke Vanarasi babu abin da muke gani sai dakunan da masu bauta ke shiga domin addu'a."
"Wannan gangami da ake yi a Varanasi, ɗan ba ne kan jerin bukatun da masu ibada za su yi ta kokarin ganin an yi musu a wuraren bauta daban-daban, wanda wannan na daga cikin ikirarin mabiya addinin Hindu," in ji mai shari'a Madan Lokur, da ta yi ritaya daga kotun kolin Indiya.
Wannan dambarwa ka iya daukar lokaci mai tsawo kafin a shawo kan ta ko cimma matsaya.










