Boris Nemtsov: Makasan boye da ake zargi da kashe mai adawa da Putin

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Sashen Bincike na BBC Eye Investigations
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, World Service
- An wallafa
An samu wani mai alaka da masu kisa a Rasha da bibbiyar ɗan hamayyar siyasar kasar Boris Nemtsov na tsawon shekara guda kafin a harbe shi, a cewar bincike.
Nemtsov ya kasance wanda ke sukar manufofin Shugaba Vladimir Putin. Kashe shi a 2015 ya kasance kisa mafi girma da aka aikata kan dan siyasa tun hawan Putin mulki.
Hukumomi sun musanta hannunsu a kisan.
Bellingcat, da kungiyar bincike na The Insider da BBC sun gano shaidu da ke tabbatar da cewa ana ta bibiyar Nemtsov a tafiye-tafiye 13 da ya yi kafin a kashe shi.
Boris Nemtsov ya kasance mutumin da ya yi fice sosai a shekarun 1990, ya riƙe mukamin mataimakin Firaminista karkashin mulkin Shugaba Boris Yeltsin, kuma a lokacin ana masa kallon wanda zai maye gurbin Yeltsin.
Maimakon haka, Mista Putin ya hau mulki, yanayin da ya tunzura Mista Nemtsov kafa nasa gangamin siyasar a Rasha.
Ya kasance mutumin da ke kan gaba wajen gangami, sun bankado masu rashawa da Allah-wadai da harin Rasha da mamaya a gabashin Ukraine a 2014.
A ranar 27 ga watan Fabarairun 2015, aka harbe Mista Nemtsov, a wuri mara tazara daga Kremlin, kuma kwanaki kafin ya jagoranci gangamin adawa da yaƙin.
An cafke maza biyar na kabilar Chechen cikin hanzari da kuma ɗaure su kan laifin kashe shi. Amma binciken hukumomi ya diga ayar tambaya kan tambayoyin da aka gagara amsawa: waye umarci a kashe shi kuma kan wani dalili?
Shekaru bakwai bayan haka, tawagar BBC - da ke aiki tare da shafin bincike na Bellingcat da The Insider - sun bankado shaidu watanni gabannin kashe shi, ana bibbiyar Nemtsov a duk sassan Rasha kuma wakilan gwamnati ke aikata hakan da ake alakantawa da kashe shi a asirce.
Amfani da zirga-zirgarsa na jiragen kasa da bayanansa na jirgin sama, binciken ya nuna cewa an bibiye Mista Nemtsov a tafiye-tafiye 13.
Lokaci na karshe da aka bibiye Mista Nemtsov shi ne a ranar 17 ga watan Fabarairun 2015, kwanaki 10 kafin a hallaka shi.
Bisa bayanan takardunsa, sunan wakilin Valery Sukharev. Dukkanin shaidun sun nuna cewa a wannan lokacin, yana aiki da hukumar FSB, ta jami'an tsaron Rasha.
Ɗaya daga cikin ayyukansu shi ne bibiyar batutuwa ko barazanar siyasar cikin gida a madadin fadar Kremlin, ciki harda sa ido kan shige da fice mutane a kasar.
An tattara bayanan mutanen da suka saye tiketin jirgin kasa dana sama a kundin bayyanan FSB da ake kira Magistral.
Amma bayanan bai tsaya kan tattara hada-hadar mutanen Rasha ba, ana iya amfani da shi wajen gano ayyukan jami'an - mutane irin su mista Sukharev.
Irin waɗannan bayanai ana bankaɗo su gaban duniya har abin ya kai ga faɗawa hannun 'yan jarida.

Wasu daga cikin ainihin bayanan da aka tattara daga binciken an samo su ne daga Bellingcat.
Masu binciken na tattara bayanasu daga jami'an da ke aikata rashawa da ke da daman samun bayanai daga kudin Magistral.
Ita ma BBC tayi amfani da wadanna bayanai da aka ba ta, ba tare da ta biya sisin kobo ba, daga majiyoyin da ke da alaka da Magistral.
Bellingcat sun sha amfani da bayanai daga kudin Magistral domin binciken kisa ko kokarin aikata kisa a Rasha.
Bincikensu ya bankado shaidu kan wasu bayanan sirri na tawagar da ke aiki da FSB, wanda ke kai samame kan mutanen da ke adawa da Kremlin. Gwamnatin Rasha dai ta sha musanta waɗannan zarge-zarge.
Akasarin tafiye-tafiyen Mista Nemtsov yana soma wane daga Moscow, inda ya ke rayuwa, zuwa Yaroslavl - kilomita 272 daga arewa maso gabashin birnin.
Ya kasance Mista Sukharev ya san tsare-tsaren Mista Nemtsov a kan lokaci, saboda yana isa birnin da zai je kwana guda ko 'yan sa'o'i kafin ya iso.
A ɗaya daga ciki tafiye-tafiyensa an ga yadda aka rinka bibiyar Mista Nemtsov sosai. A lokacin bazara a 2014 ya je Siberia.
Mista Nemtsov ya siya tiketin jirgi a shafin intanet a ranar 2 ga watan Yuli a tsakiyar dare.
Dakika 10 bayan haka, Mista Sukharev shi ma ya siya irin wannan tiketi kuma suka isa rana guda da Mista Nemtsov.
Jami'an FSB na iya amfani da Magistral wajen farwa mutum ko da suna daga nesa, a cewar Mista Grozev.
Tawagar da ta kasance guba
Ba wai sabon abu ba ne a Rasha a samu jami'an tsaro na bibiyar manyan abokan hamayyar siyasa.
Amma Mista Sukharev ba wai karamin jami'in FSB ba ne da aka dauka domin wannan aikin.
A bincikenta na baya Bellingcat ta alakanta shi da wasu manyan mutane biyu da aka yi kokarin hallakawa, duk sun kasance masu matukar sukar Putin.
Mutum na farko da aka soma farwa ya kasance abokin Mista Nemtsov Vladimir Kara-Murza, babban dan hamayya, wanda makonni da yin harbin ake ta ɗaura laifi kan Kremlin.
A Mayun 2015, Sukharev ya kasance cikin tawagar da suka je birnin Rasha na Kazan a wannan lokaci tare da Mista Kara-Murza.
Kwana biyu bayan Mista Kara - Murza ya koma Moscow ya fadi ya gaggara numfashi. Ya shiga yanayi na dogon bacci kuma sassa da dama na jikinsa sun daina aiki amma daga baya ya ji sauki.
An sake ba shi guba a karo na biyu a 2017, kuma ya sake tsira. Gwamnatin Rasha ta musanta zarge-zargen da ake mata cewa akwai hannunta wajen ba shi guba.

Mutum na biyu da aka sake kai wa hari shi ne Alexei Navalny, wanda yanzu ake garkame da shi kan wani bidiyonsa na adawa da rashawa da ya kai ga milyoyin 'yan Rasha.
A 2020, An bai wa Mista Navalny gubar Novichok, da ke lalata laka wanda aka samar a Tarayyar Soviet kuma aka haramta amfani da shi karkashin dokokin kasa da kasa.
Bellingcat ta kafa hujjar cewa tawagar FSB sun bibiyi Mista Navalny har zuwa birnin Tomsk kafin ba shi gubar.
An kuma gano cewa Mista Sukharev baya cikin tawagar da suka bibiye Mista Navalny.
Amma bayanan waya sun bankado cewa, watanni kafin ba shi gubar, Mista Sukharev sun yi musayar sakonni da yin wayoyi sau 145 tsakanin mambobi 145.
Hudu daga cikin waɗannan mazan na cikin jami'an FSB bakwai da Amurka da Burtaniya suka kakabawa takunkumi kan zargin akwai hannusu a kokarin aikata kisa.
Gwamnatin Rasha ta sha musanta cewa akwai hannunta a kokarin hallaka Mista Navalny da guba.
BBC ta tambaye gwamnatin Rasha da FSB cewa su yi tsokaci kan shaidun da ke nuna cewa an samu wanda ya rinka bibbiyar Mista Nemtsov wanda ke da alaka da kugiyarta na masu kisa.
Kakakin Kremlin, Dmitry Peskov, ya ce: "Dukkanin waɗannan zarge-zarge ba su da alaka da gwamnatin Rasha. Ya kasance kamar abin da aka shirya." FSB taƙi yin tsokaci.
Bincike: Christo Grozev, Yordan Tsalov, Roman Dobrokhotov
Shiryawa: Aliaume Leroy, Antoine Schirer, Bertram Hill, Charlotte Pamment
Tacewa: Daniel Adamson











