Yakin Ukraine: Hotunan ƙarya da aka yaɗa na rikicin Ukraine a Najeriya da sauran ƙasashen duniya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Daga Alistair Coleman da Shayan Sardarizadeh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Monitoring
- An wallafa
Harin da Rasha ake kai wa Ukraine ya haifar da hotuna da bidiyo na bogi da ke kokari janyo rudani a shafukan sada zumunta wadanda masu wallafa su ke cewa hotunan rikicin ne.
Wasu hotunan da BBC ta yi nazari kansu sun hada da wadanda aka samo daga tsohon rikicin Ukraine da kuma na wasu wurare a duniya baya ga na sojojin da ke yin rawar daji.
Da alama dandalin sada zumunta kamar Twitter na daukar matakan kawar da irin wadannan bayanan masu janyo rudani, inda suka cire bidiyo masu yawa.
Abubuwan da ake yaɗawa a Najeriya

Hoton wata ƙaramar yarinya da ke tunkarar wani soja wanda ya bazu kamar wutar daji, wanda kuma ake amfani da shi domin nuna jarumta yayin wani yanayi mai tayar da hankali, ba daga Ukraine yake ba.
Hotunan daga Falasɗinu aka samo su kuma sunan yarinyar da ke cikin hoton Ahed Tamini, wadda shekarunta 11 lokacin da aka dauki hoton a shekarar 2012.
Ana ci gaba da yada wannan hoton a shafukan sada zumunta a Najeriya.
Akwai kuma wani hoton da ke yawo a Najeriya na tsohon zakaran damben duniya kuma Magajin Garin birnin Kiev na kasar Ukraine, wato Vitali Klitschko sanye da kayan soja kuma yana dauke da mashin gan.
Hoton na Mista Klitschko ne wanda ya fara bayyana a shafinsa na Instagram a watan Maris din 2021.

Wasu hotunan bogi da ake yada wa a WhatsApp a Najeriya su ne na fashewar da wani sinadarin taki da ya auku a tashar jiragen ruwa ta Beirut a Lebanon.
Masu yada wannan hoton na son yaudarar mutane, suna cewa hoton na nuna irin barnar da Rasha ke yi wa Ukraine ne.
Akwai kuma wani tsohon hoto daga yakin da dakarun Ukraine ke yi da 'yan awaren yankin Donbas na kasar a 2014, hoton da ake yadawa a Twitter ana cewa na wannan yakin da ke aukuwa a yanzu ne. Sai dai daga baya Twitter ta cire hoton.
Akwai kuma wasu labaran bogin da aka wallafa da ke cewa wai Shugaba Putin ya yi barazanar kai wa Najeriya hari.
Wasu cikin wadannan labaran na yin fassarar da ba ta gaske ce ba kan jawabai da hotunan Mista Putin, suna cewa wai ya furta kalaman "Najeriya ce ta gaba".

Jiragen yaƙi na bogi
A sa'o'in farko bayan barkewar rikicin, an wallafa wasu bidiyo da ake cewa na jiragen yakin Rasha ne suna shawage a samaniyar Ukraine kuma sun bazu kamar wutar daji.
Wani bidiyon da aka cire daga baya na nuna wani jirgin yaki na yawo a cikin gari. An rubuta wani sako tare da hoton da ke son yaudarra mai karatu cewa yayin rikin na Ukraine aka dauke shi.

Sai dai bayan an yi nazari mai zurfi, an gano cewa jirgin yakin na Amurka ne samfurin F-16 Fighting Falcon, wanda ba a taba amfani da shi a Rasha ko Ukraine ba.
Wani bidiyon kuma ya nuna wani ayarin jiragen yaki da masu daukar bama-bamai a shawage a saman wani birnin yayin da ake jin sautin jiniya na tashi.

Binciken da BBC ta yi ya gano cewa bidiyon na nuna jiragen yakin da ke shirin gudanar da wani faretin soji ne a samaniyar wani birni a 2020.
An dora sautin jiniyar ne daga baya bisa ainihin sautin da ke cikin bidiyon.
Wani bidiyon kuma na nuna sojojin kundunbala masu fadowa daga jiragen sama da lema na sauka kusa da birnin Kharkiv na Ukraine.

An kalle shi sau daruruwan dubban lokaci a Twitter, sai dai ya fara bayyana ne a wani shafin intanet na harshen Rashanci a 2016.
Akwai kuma wani bidiyon na hudu da aka yada sosai a twitter da YouTube kuma ana cewa an harbo wani jirgin yakin Rasha ne a Ukraine.

Sai dai 'yan jarida daga BBC sun taba ganin wannan bidiyon a da. Na wani jirgin saman gwamnatin Libya ne da 'yan tawaye suka harbo a Benghazi a 2011.
An iyajin muryoyin 'yan tawayen na murnar harbo jirgin, kuma suna magana ne da Larabci.
Wasu hotunan ba sa nuna yaki ma samsam.
Ana hasashen cewa bidiyon wani abu da ya fashe a bayan wani bene a birnin Mariupol da ke kudu maso gabashin Ukraine aka dauko shi.
Cikin masu yada bidiyon akwai shafin Twitter na Volodymyr Yelchenko wanda shi ne jakadan Ukraine a Amurka.

Sai dai wani bidiyo mai kama da wannan ya bayyana a TikTok ranar 29 ga watan Janairu a wani shafi da ke wallafa hotuna da bidiyo da fina-finan abubuwa masu fashewa.
Sannan da alama rubutun da ke jikin bidiyon da Rashanci aka rubuta shi, kuma ya nuna sakamakon yadda walkiya ta fada wa wata tashar samar da lantarki, ba wai an kai hari na soja ne ba.
Masu amfani da shafukan sun kuma bayyana shakku kan yadda bishiyoyin wurin suka kasance masu launi kore shar, inda bayanan da ake da su na cewa yanayi a watan Fabrairu a yankin na Mariupol ya yi kasa zuwa kusan sifili a ma'unin Celsius saboda tsananin sanyi.
Wasu kuma sun yada wani hoto da ake ikirarin wai dakarun Rasha ne ke daga tuta a babban ginin gwamnati da ke birnin Kharkiv a yau.

Duk da cewa rubutun da aka yi a bidiyon gaskiya ne - domin ya nuna Rashawa na daga tuta a wannan ginin da ke Kharkiv - bincike mai zurfi kan asalin hoton ya tabatar cewa a 2014 lamarin ya auku yayin wani rikicin na daban.
Sai kuma bidiyon da aka rika yada wa a wani shafin Twitter na harshen China, wanda aka rubuta "Putin mai girma ya kai wa Ukraine hari".
Ana iya gane cewa hoton fashewar da ta auku ne a wani gini da ke tashar jirgin ruwa ta birnin Beirut a watan Agustan 2020 wanda yayi sanadin mutuwar mutum fiye da 200.

Gaskiya ko Karya
Al'amura masu aukuwa ciikn hanzari na nufin babu makawa sai an wallafa hotunan bogi a shafukan sada zumunta.
Hotunan na da saukin yadawa musamman ga wadanda suka yi imanin na gaske ne.
Masu amfani da shafukan sada zumunta na iya rage yawan labarai da hotunan bogi da ake yadawa ta hanyar saurarawa na wani lokaci domin yin nazari kan ko labaran sun fito daga wuri ne da aka amince da sahihancin labaran da suke fitarwa kafin su aikawa wasu hotunan ko labaran.
Yawancin gidajen rediyo da jarida na daukan lokaci sosai domin tabbatar da sahihancin abubuwan da suke wallafawa, saboda haka dubawa ko labaran da hotunan sun bayyana a gidajen jarida fiye da daya kafin a yada su na taimakawa wajen hana labaran bogi karade shafukan sada zumunta.










