Hanyoyi biyar na warware rikicin Ukraine

A Ukrainian territorial defence reservist during trains near Kyiv, Ukraine. File photo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Asarar da za a tafka a fannin tattalin arziki za ta yi matukar muni, kana matsalolin da suka shafi biladama za su kara tsananta
    • Marubuci, Daga James Landale
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Diplomatic correspondent
  • An wallafa

Alamun gagarumin yaki a kasar Ukraine mummunan abu ne da za a iya hangor abkuwarsa. Muddin dai kasar Rasha ta kutsa kai, dubbai za su rasa rayukansu. Karin wasu da dama za su tsere.

Asarar da za a tafka a fannin tattalin arziki za ta yi matukar muni, kana matsalolin da suka shafi biladama za su kara tsananta.

Har yanzu Rasha na cigaba da kara yawan dakarunta a kusa da kasar Ukraine, kana kasashen Yamma na cigaba da yin kurari kan mummunan abubuwan da ka iya biyo baya muddin suka ketara kan iyakar zuwa cikin kasar.

Don haka, shin akwai hanyoyi na diflomasiyya na shawo kan matsalolin, da zai kawo karshen wannan fito-na-fiton zuwa zaman lafiya kuma mai dorewa?

Jami'an diflomasiyya sun yi magana a kan ''fita daga gargada''', wata hanya wacce duka bangarorin za su fita daga fadawa cikin mummunan yaki. Amma kuma samun wannan mafita ba abu ne mai sauki ba.

Duk wata sasantawa za ta zo ne da wani sakamako. A nan, akwai wasu hanyoyin da ka iya yin amfani wadanda ba sa bukatar ayyukan soji da kuma sakamako na zub da jini.

Kasashen Yamma za su iya lallabar Shugaba Putin da ya janye

A cikin wadannan abubuwa da ke faruwa, kasashen Yammaci za su iya matukar hana mamayerwar ta hanyar jan jan hankalin Shugaban kasar Russia Vladimir Putin kan yadda mummunan tasirin da zai biyo bayan hakan zai rinjayi amfaninsa.

Za a iya janyo hankalinsa cewa asarar rayuka, da takunkumin tattalin arziki da kuma na diplomasiyya za su kasance masu tsanani koda kuwa ya samu wata galabar soji a fagen yakin.

Dole zai yi fargabar mai yiwuwa kasashen Yamma za su goyi bayan sojoji masu tayar da kayar baya a Ukraine, don haka zai shafe shekaru da dama yana jin jiki.

Dole ne Mista Putin zai amince cewa wadannan munanan tasiri za su rage masa karfin samun goyon bayan da yake samu a cikin gida, don haka barazana ce ga shugabancinsa.

A cikin wannan batu, kasashen Yamma za kuma su amince wa Putin ya yi ikirarin samun galaba a fannin diplomasiyya, tare da bayyana kan sa a matsayin gwanin son zaman lafiya wanda ya ki kula da duk wata tsonanar sojin kungiyar tsaro ta Nato ba.

Mista Putin kai iya yin ikirarin cewa daga karshe ya samu kulawar kasashen Yammaci kana shugabanninta na shawo kan abinda suka kira ''halattaciyar nuna damuwa kan tsaro''.

Kasar Russia ka iya tunatar wa da duniya cewa a baya ita ce mafi karfi a duniya, kana ta kara yawan akarunta a kasar Belarus.

Sarkakiyar da ke tattare da wannan batu shi ne cewa kamar wani abu mai sauki ne yin jayyayar cewa Mista Putin ya gaza.

Kamata ya yi a ce matakan da ya dauka da sun hada kawunan kasashen Yammaci; tare da saka Nato aikewa da dakarunta kusa kan iyakokin kasar Russia; da kuma karfafa guiwar kasashen Sweden, da Finland, da su shiga kungiyar tsaro ta Nato.

Matsalar it ace muddin Mista Putin na fatan karbe ikon kasar Ukraine tare da yin zagon kasa da kungiyar tsaro ta Nato, akwai dalilai kalilan da ken una cewa akwai yiwuwar zai janye.

Nato da Russia cza su iya amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya

Kasashen Yammaci sun bayyana karara cewa ba za su amince a kan muhimman ka'idoji ba, kamar karfin iko da martabar yankin kasar Ukraine; daidai ne ta nemi zama mamba a kungiyar tsaro ta Nato; wacce dole ta kasance a koda yaushe kofarta a bude ne ga ko wace kasa da ke son shiga ciki.

Amma kuma duk da haka, Amurka da Nato, sun amince cewa za a iya samun ra'ayi iri daya a kan batutuwa da dama na harkokin tsaron kasashen Turai.

Wannan zai kunshi sake farfado da yarjejeniyar mallakar makamai da ta sha ruwa, wajen rage yawan makamai masu linzami daga duka bangarorin biyu.

Da kara matakan karfafa guiwa tsakanin kasar Rasha da dakarun Nato; da nuna adalci kan ayyukan soji a wuraren da aka ajiye makamai masu linzami; da kuma hadin kai kan gwajin makaman lalata tauraron dan adam.

Rasha ta riga ta nuna karara cewa wadannan batutuwa ba za su wadatar ba wajen gamsar da muhimman abubuwan damuwarta ba da cewa bai wa kasar Ukraine damar shiga kungiyar tsaro ta Nato zai haifar wa da harkokin tsaron kasar Russia barazana.

1px transparent line

Amma kuma, muddin aka ce an yi gagarumin rage yawan aikewa da makamai masu linzami na kungiyar Nato, hakan zai akalla shawo kan wasu daga cikin damuwar da kasar Russia ke da su.

Ta wasu hanyoyin, Putin ya riga ya samu galaba a nan: Turai ta kasance sabuwa a cikin tattanawar batun harkokin tsaro a bisa sharuddan kasar Russia.

Ukraine da Rasha za su iya farfado da yarjejeniyar Minsk

Wannan wasu tarin yarjeniyoyi ne da aka tattauna a teburin shawara a kai a shekarar 2014 da 2015 a Minsk babban birnin kasar Belarus, da aka yanke don kawo karshen yaki tsakanin dakarun gwamnati da kuma na 'yan tawayen da Russia ke mara wa baya a gabashin kasar Ukraine.

A bayyane ta ke cewa ta gaza - fadan ya cigaba. Amma akalla ya bude wata 'yar hanya wajen tsagaita wuta da kuma kwanciyar hankalin siyasa a bisa kari wasu dokokin gwamnatin tarayya.

Tanks ride during joint exercises of the armed forces of Russia and Belarus as part of an inspection of the Union State"s Response Force, at a firing range in Belarus. File photo

Asalin hoton, Russian defence ministry

'Yan siyasar kasashen Yammaci sun bayar da shawarar cewa yanzu farfado da yarjejeniyar Minsk ka iya zama hanyar warware wannan rikici.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya ce Minsk ita kadai ce ''hanyar da za ta bayar da damar wanzar da zaman llafiya''.

Sakataren harkokin tsaro Ben Wallace ya shaida wa BBC cewa farfado da yarjejeniyar Minsk zai kasance ''gagarumar hanyar samun cigaba na shawo kan rikicin ".

Matsalar ita ce ana ta jayayya da takaddama kan tanade-tanaden yarjejeniyar.

Fadar Kremlin ta bukaci kasar Ukraine da dole ta gudanar da zabuka don karfafa guiwar 'yan siyasar da ke goyon bayan kasar Russian. Kyiv na bukatar Moscow ta fara janye makamai da mayakan kasar Russian.

Takaddama mafi girma ita ce kan ko 'yancin cin gashin kai nawa Minsk za ta bayar don rusa sansanonin da dama a Donbas.

Kyiv ya ce says modest self-go. Moscow na yin jayayya cewa dole ne ya zamanto biranen Donetsk da Luhansk suna da 'yancin fada-a-ji a kan manufofin kasar Ukraine kan kasashen waje, da kuma hawa kujerar naki kan zama mamba a cikin kungiyar tsaro ta Mato.

Kuma wannan wata babban abun fargaba a Kyiv: cewa farfado da Minsk wata gajeruwar hanya ce ta hana kasar Ukraine duk wata dama da shiga kungiyar tsaro ta Nato ba tare da mambobin kungiyar ta Nato sun fito sun fadi hakan ba.

Don haka yarjejeniya da kuma mara wa kasar Ukraine baya ba lallai mai yiwuwa bane.

Ukraine ka iya kasancewa 'yar tsaka-tsaki, kamar kasar Finland

Shin na a iya janyo hankalin kasar Ukraine ta zabi kasancewa 'yar tsaka-tsaki?

Akwai rahotanni - da ake yawan musantawa - cewa mahukuntan kasar Faransa suka bayar da shawarar cewa Ukraine za ta iya yin koyi da kasar Finland.

Kasar Finland ta zabu kasancewa 'yar tsaka-tsaki a lokacin Yakin Cacar Baka, Kasa ce maii cin gashin kai da kuma tsarin dimokaradiyya. Ta kasance - tana kuma cigaba da kasancewa - ba a cikin kungiyar tsaro ta Nato ba.

Shin hakan zai iya jan hankalin Kyiv? Za ta kauce wa sakamakon ayyukan soji. Za ta iya yi, a aikace, gamsar da bukatun Mista Putin kan Ukraine kada ta taba shiga cikin kungiyar ta Nato.

Kana da kwancen bai amince da tsarin manufofin ''kofa a bude''; Da kasar Ukraine ta zabi 'yancin cinta na zabin kin shiga cikin kungiyar.

Amma kuma shin Ukraine za ta goyi bayan wannan? Zai iya yiwuwa ba saboda zama 'yar tsaka-tsaki zai bar Ukraine cikin barazanar kasancewa a tafin hannun kasar Russia.

Zai zama da matukar wahala ta kasance 'yar ba ruwanmu, kana shin kasar Russia za ta bi sharuddanta?

Tsaka-tsaki zai kasnacewa wani babban abin yarjewa a bangaren Kyiv wanda dole ta ture burin da ta ke da shin na kasashen yankin Turai da Atlantika.

Tsaka-tsakin kuma zai iya haifar wa da kasancewa mamba a Kungiyar Tarayyar Turai a nesa.

Halin fito-na-fiton da ake ciki zai cigaba da faruwa

Ko shin zai iya kasancewa halin fito-na-fiton da ake ciki zai cigaba da faruwa - amma ya karfinsa ya ragu zuwa nan gaba?

Russia ka iya janye dakarunta zuwa barikoki sannu a hankali, tare da ayyana cewa ayyukan sojinsu ya kawo karshe. Amma a lokaci guda kuma za a iya barin kayan ayyukan sojin da dama a baya, koda wani abu zai taso.

Moscow za ta iya cigaba da goyon bayan dakarun 'yan tawaye a Donbas, Kana iya tsawon lokacin, harkokin siyasa da tattalin arzikin Ukraine ka iya cigaba da kasancewa cikin rudani saboda cigaba da barazanar kasar Russia.

Daya bayan daya kuma, kasashen Yammaci za su cigaba da kara karfin dakarun kungiyar Nato a gabashin Turai. 'Yan siyasarta da jami'an diplomasiyyarta za su cigaba da yin tattaunawa sosai da takwarorinsu na kasar Russia, inda tattaunawar ke cigaba o amma kuma cigaba kadan aka samu.

Ukraine za ta yi ta fadi-tashi. Amma akalla ba za a samu wani gagarumin yaki ba.

Kana sannu a hankali fit-na-fiton da ake yi zai gushe manyan batutuwan kafofin yada labarai, ya shiga cikin kundin ajiyar labaran rikice-rikicen da suka kau daga hankulan jama'a.

Babu daya daga cikin wadannan abubuwan da ke da sauki ko kuma yiwuwa. Duka suna bukatar sansantawa.

Fargaba a Kyiv it ace akwai yiwuwar Ukraine ta kasance kasa wacce dole ta fi hakurewa. Nazarin a nan shi ne ko shin fargabar mummunan tashin hankalin da gaske ne, in haka ne kuma ko mai ya kamata a yi don kauce masa.

Abu daya kalilan na fatan da ake shi ne yanzu cewa duka bangarorin biyu da alamu na da sha'awar zaman tattaunawa, amma kuma babu nasara.

Kana yawan dadewar da mutane za su yi a kan tattaunawa, shi ne damar karin cigaba da bude kofofin diplomassiyar da za su shawo kan matsalolin, ko da kuwa kadan ne a bude.