Pushpa: Abin da ya sa wakar da aka dinga ambaton maza ta tayar da kura a Indiya

Asalin hoton, Screenshot from YouTube
- Marubuci, Daga Sharanya Hrishikesh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Delhi
- An wallafa
Wata mata da ke rawa da yin wata waƙa wadda ake ganin tana nuna wariya ta jawo ce-ce-ku-ce matuƙa a India.
A lokacin da aka saki sabuwar waƙa daga wani kamfanin fim na Telegu a Disamba, a cikin waƙar wadda aka yi ikirarin kawo sauyi ga yadda maza ke kallon mata.
An yi waƙar ne a harsuna biyar da suka haɗa da Telugu da Tamil da Kannada da Malayalam da Hindi inda kuma aka yi bidiyo na daƙiƙoƙi 19 na waƙar.
Waƙar da aka yi a duka harsunan na ɗauke da saƙo iri ɗaya: Waƙar na bayyana cewa mace ko tsohuwa ce ko matashiya ko doguwa ko kajera ko ta saka doguwar riga ko gajera ba za ta iya kauce wa kallon namiji ba.
Sai dai mata da dama ba su ji daɗin hakan ba, suna kallon hakan a matsayin ɓatanci. Wakar ta yi iƙirarin cewa mata na ɗauke hankalin maza matuƙa su kuma mazan ba su iya haƙuri kamar yadda wasu masu sharhi suka bayyana.
Nuna bambancin jinsi
"Na duba duka waƙoƙin waɗanda aka yi su da harsuna daban-daban. Akwai wani baiti a ciki wanda ya kwatanta mata da abinci." in ji Sowmya Rajendran, wadda edita ce ta The News Minute inda take yawan rubuce-rubuce kan fina-finai.
"A harshen Tamil, ana nufin abinci a Telugu kuma ana nufin inabi, a Malayalam kuma ana nufin sukari. Alaƙanta mata da abinci ya ƙara tabbatar da batun da ake yi na maza na kallonsu.
Waɗanda suka rinƙa kallon bidiyon waƙar waɗanda akasarinsu maza ne suna son waƙar. Sun yaba wa Samantha Ruth Prabhu, wadda ta yi waƙar kuma tana cikin manyan mawaƙa mata na kudancin ƙasar kan irin rawa da waƙar da ta yi a bidiyon.
Har yanzu ba a saki cikakkiyar waƙar ba duk da cewa an fitar da fim ɗin, sai dai a halin yanzu an kalli bidiyon waƙar sama da sau miliyan 100 a Youtube a harshen Telugu kaɗai. Haka kuma taken waƙar na ya shafe kwanaki ana tattauna shi a shafukan sada zumunta.

Asalin hoton, Getty Images
Sai dai abin mamaki, irin wannan waƙar ba ta yawan jawo ce-ce-ku-ce. Akasarin irin waƙoƙin nan na alaƙanta mata da abinci kamar nama ko kuma a nuna a bidiyo, in ji Ms Rajendran.
Ta bayar da misali da ɗaya daga cikin waƙoƙin da take kallo a matsayin ɓatanci wadda a ciki akwai Kareena Kapoor Khan inda ta rinƙa alaƙanta kanta da kaza wadda za a iya wankewa da barasa.
"A lokuta da dama, ba mu san komai ba dangane da matar da ke cikin waƙar ba. Babu wani labari a kanta, an nuna ta ne kawai aka ɗauke ta a cikin fim ɗin," in ji Ms Rajendran.,
Irin waɗannan waƙoƙin da daɗewa sun sha jawo ce-ce-ku-ce musamman kan alaƙanta mata da wasu abubuwa - inda suke saka matsatsun kaya da faɗan wasu irin kalamai.
Amma irin waɗannan waƙoƙin ana son su musamman a ƙasashe waɗanda masu kallon maza ne.
Waƙa mai daɗi a cikin fim a baya na yawan jawo wa fim ɗin farin jini, wanda yake jawo hankalin mutane zuwa wajen kallo da kuma jawo a samu kuɗin shiga da riba mai yawa.
A wannan zamani kuma da ake da YouTube da Instagram, waƙoƙin kuma sun fi tafiya.
Lokutan da aka rinƙa alaƙanta mata da wasu abubuwa
A shekarar 1994, ɗan jarida Arun Katiyar yayi rubutu inda ya ce suna da nasarar da wata waƙa mai ce-ce-ku-ce ta yi a 1993 ya taimaka wajen samar da wata al'ada da ambatar halittar ɗan adam da wani abu wanda mutane suka yi ta rubuta waƙoƙi domin kwatanta ɗan adam da wani abu.
Waƙar ita ce choli ke peeche kya hai, wadda aka fassara ta da me ke bayan rigarki? Amasar a cikin waƙar ita ce: Zuciyata. Sai dai a wata fassara ta daban, Madhuri Dixit, wanda shahararren ɗan Bollywood ne a lokacin ya bayyana cewa akwai wata amsa ta daban dangane da waɗannan kalaman.
Irin waɗannan kalaman sun jawo ran mutane da dama ya ɓaci, ciki har da ƴan siyasa waɗanda suka ce irin hakan ya tunzura maza cin zarafin mata.











