Aminu Tambuwal: Na bukaci Buhari ya saka dokar ta baci

mUHAMAMDU bUHARI DA aMINU tAMBUWAL

Asalin hoton, MUHAMMADU BUHARI / FACEBOOK

Bayanan hoto, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto
An wallafa

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziru Tambuwal ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da ya sanya dokar ta baci a jihohin da 'yan fashin daji suke adabbar al'umominsu.

Gwamnan ya ce a ganawar da suka yi da shugaba Buhari ranar Litinin a Abuja, ya ce ya fada ma shugaban cewa kundin tsarin mulki ya ba shi damar yin haka.

A tattaunawar da suka yi da BBC, gwamnan ya ce dokar ta bacin za ta ba sojoji damar daukar matakan dakile ayyukan 'yan bindigar.

BBC: Menene makasudin ziyarar da aka akai wa Shugaba Buhari a Fadarsa da ke Abuja?

Gwamna Aminu Tambuwal: Baabn dalilin da ya sa na kai wannan ziyarar shi ne kan yadda matsalar tsaro ke ta'azzara kuma suke kara tabarbarewa musamman a yankin gabas na jihar Sokoto.

BBC: Cikin makon nan shugaban ya aika da wata tawaga zuwa jihar Sokoto kan wannan batun, shin ba ka gamsu da aikin da wadanda ya aika suka yi ba ne?

Gwamna Tambuwal: Bayan zuwan tawagar shi naga ya dace in zo in kara yi masa bayani kan wanda suka yi masa na yanayin da al'umomi suke ciki a wannan sashe na jihar Sokoto, domin shugaban kasa ya bayar da umarni a dauki matakan kawo karshen wannan matsala.

BBC: To wannan koken da ka kai wa Shugaba Buhari kai tsaye, a ganinka ya sami karbuwa kuwa?

Gwamna Tambuwal: E, ga dukkan alamu shawarwarin da na bayar ina ganin shugaban kasa zai yi amfani da su, musamman shawarar da na ba shi cewa tsarin mulkin Najeriya ya ba shi damar saka dokar ta baci a wadannan bangarori da 'yan ta'addan suke musamman tsakanin jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Kaduna da neja da kuma Kebbi. Wannan zai ba sojoji da sauran jami'an tsaron Najeriya su sami damar shiga wajen ba tare da suna dardar cewa za a tuhume su da take hakkin dan Adam ba. Ina ganin ba a ba shugaban kasa wannan shawarar ba, kuma ba a dauki wannan matakin ba.

BBC: To bayan kun gama tattauna da shugaban kasa, ko akwai wani matakin da ya sanar da kai cewa zai dauka?

Gwamna Tambuwal: E, ya bani tabbacin cewa za a samar da abubuwan da ake bukata na magance wannan matsalar, musamman karin jami'an tsaro da makamai, da kuma hadin kai tsakanin Najeriya da sauran kasashen Afirka ta Yamma irinsu Nijar, irinsu Mali domin a kawo karshen matsalar tsakaninmu da su, domin akwai matsalar makamai da ke shigowa ta kan iyakokin kasashen.

Muhamamdu Buhari and Aminu Tambuwal

Asalin hoton, MUHAMAMDU BUHARI / FACEBOOK

'Ba za mu huta ba har sai mun fatattaki 'yan bindiga'

A wata sanarwa da aka wallafa a shafin Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da ke Facebook, shugaban ya ce "na ba Gwamna Aminu Tambuwal tabbacin samun goyon bayan gwamnatin Tarayyar Najeriya domin dawo da zaman lafiya da tsaro."

Shugaban ya kuma ce "Shugabannin jami'an tsaro sun tabbatar min cewa za a fatattaki wadannan miyagun 'yan bindigan a duk inda suke kuma a yi mu su shari'a. Ba za mu huta ba har sai an cimma wannan kudurin."

Shugaban ya kuma yi addu'a ga wadanda suka rasa rayukansu, inda ya ce rantsuwarsa ita ce rayukansu ba za su salwanta a banza ba.