Nigeria a 61: Amsoshin muhimman tambayoyi 8 kan Najeriya

Asalin hoton, Presidency
- Marubuci, Halima Umar Saleh
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- An wallafa
Najeriya ta cika shekara 61 da samun 'yancin kai daga Turawan Mulkin Mallaka na Ingila.
Wannan mikakkiyar tafiya ce da za ta sa 'yan kasar da suka samu damar ganin wannan rana su yi tsam, tare da waiwaye kan irin dumbin ci gaba da tarnaki da Najeriyar ke fuskanta.
Amma a wannan makalar, za mu duba muhimman abubuwa 10 ne da ya kamata a ce kowane dan kasar ya san da su.
1. Su waye suka yi fafutukar samun 'yancin Najeriya?
A ranar 1 ga watan Okotoban shekarar 1960 ne zaratan 'yan Najeriyar da suka yi fafutukar neman 'yancin kasar suka yi nasarar samun hakan. A shekarar 1963 kuma Najeriyata zama jamhuriyya.
Wadannan 'yan kasa matasa ne masu jini a jika sosai a lokacin da lamarin ya faru, kuma sun kasance masu kishin kasa.
Da yake suna da dan yawa, a nan za mu ambaci kadan daga cikinsu ne kuma wadanda suke kan gaba-gaba a fafutukar.
- Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto
- Sir Abubakar Tafawa Balewa
- Cif Obafemi Awolowo
- Cif Nnamdi Azikiwe
- Oluwafunmilayo Ransome-Kuti
- Cif Margaret Ekpo
- Eyo Ita
- Herbert Macaulay
- Anthony Enahoro.

2. Yanayin kasa na Najeriya
Najeriya tana yankin Afirka Ta Yamma ne. Ta yi iyaka da Jamhuriyyar Nijar daga arewa, sannan ta yi iyaka da kasashen Chadi da Kamaru daga Gabas, sai ta yi iya da Mashigar Tekun Guinea na Atlantika daga Kudu da kuma Jamhuriyyar Benin daga YAmma.
Girman Najeriya ya kai murabba'in kilomita 923,768. Manyan kogunan da suka ratsa kasar su ne Kogin Neja da na Binuwai, wadanda suka yi mahada a birnin Lokoja na jihar Kogi da ke tsakiyar kasar.
Yanayi a Najeriya ya hada da damina da bazara (zafi) da hunturu. Sai dai yankin kudancin kasar ya fi samun damina mai tsawo, yayin da ba a faye yin hunturu ba a can.
A lokacin samun 'yancin kanta Legas ne ya kasance babban birninta, har sai a shekarar 1991 da aka mayar da shi Abuja.
A yanzu Najeriya na da jihohi 36 a yankuna shida da suka hada da:
- Arewa maso gabas mai jihohi shida
- Arewa maso yamma mai jihohi bakwai
- Arewa ta tsakiya mai jihohi shida
- Kudu maso gabas mai jihohi biyar
- Kudu maso yamma jihohi shida
- Kudu maso kudu jihohi biyar.

3. Karfin tattalin arzikin Najeriya - GDP
Najeriya tana daga cikin kasashen da ake kira masu tasowa a duniya, wato ana nufin masu matsakaicin tattalin arziki, kuma wadanda ba su bunkasa sun kai sun kawo ba a bangaren karfin masana'antu.
Najeriya ce ta 27 a jerin karfin tattalin arzikin kasashen duniya 211 a shekarar 2021 yayin da ta zamo ta daya a Afirka, a ma'aunin arzikin da kasar ke samarwa a cikin gida, kamar yadda shafin worldpopulationreview ya wallafa.
Sannan Najeriya ce ta uku a mafi yawan arziki a Afirka inda take da dala biliyan 207 kamar yadda shafin statista ya wallafa.
4. Wadanne ne albarkatun kasar Najeriya?

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya kasa ce da Allah Ya yi wa arzikin dumbin albarkatun kasa. Man fetur shi ne bababn albarkar da kasar ta fi alfahari da shi, wanda shi ne kashi 10 cikin 100 na arzikin da take samarwa a cikin gida.
Kudin shigar da kasar ke samun daga man fetur din da take fitarwa ya kai kashi 86 cikin 100.
Sauran ma'adanan da Najeriya ke da su sun hada da:
- Fetur
- Iskar gas
- Ma'adanin tin
- Iron ore
- Ma'adanin kwal
- Limestone,
- Zinc
- Gishiri
- Kasar noma
- gwal
- Koko (cocoa)
- gahawa
- auduga
- rake
- man-ja
- goro
- gyada, da sauransu.

5. Yawan al'ummar Najeriya fa?

Asalin hoton, Getty Images
Ana kiyasin cewa yawan al'ummar Najeriya ya kai miliyan 212, abin da ya sa ta zama kasa mafi yawan al'umma a nahiyar Afirka.
Sannan ita ce kasa mafi yawan bakaken fata a duniya, kuma ta bakwai a mafi yawan al'umma a duniyar.
Manyan birane biyar da suka fi yawan al'umma su ne Legas da Kano da Kaduna da Fatakwal da Ibadan.
6. Kabilu da yaruka nawa ne a Najeriya?
Wannan shi ne wani batu mafi daukar hankali kan lamarin Najeriya.
Turanci shi ne yaren da ake amfani da shi wajen gudanar da al'amuran gwamnati da ilimi a kasar.
Bayanai sun nuna cewa akwai sama da yaruka 300 a Najeriya, amma manya daga cikinsu su ne Hausa da Yarbanci da Igbo da Fulani da Kanuri da Nupe.
Wasu daga cikin sauran yarukan sun hada da Efik da Ibibio da Ijaw da Tiv da Idoma
Jihar Bauchi ce ta fi kowacce yawan yaruka inda take da 60, yayin da Jihar Adamawa ke da 58 da suka hada da Bura phabir, Fultfulde, Huba (Kilba), Bacama/Bata (Bwatiye), Longuda, Mumuye, da Samba Daka.
Jihohin Borno da Binuwai da Delta da Edo da Gombe ma na daga cikin wadanda suke da yawan yaruka
Wannan yawan kabilu da yaruka ya sa kasar ta zama mai al'adu daban-daban masu ban sha'awa da ke jan hankalin duniya.

7. Mulkin soja nawa aka yi a Najeriya?
A shekarar 1966 ne aka fara samun gwamnatin mulkin soja a Najeriya bayan da Manjo Janar Johnson Aguiyi-Ironsi ya dare mulkin shugabancin kasar a ranar 16 ga watan Janairu ya kuma sauka a ranar 29 ga Yulin 1966 wato bayan kwana 194.
Daga nan sai gwamnatin Janar Yakubu Gowon daga 1 ga Agustan 1966 zuwa 29 ga Yulin 1975. Ya shafe shekara takwas da kwana 362.
Gwamnatin Janar Murtala Mohammed daga 29 ga Yulin 1975, aka kashe shi ranar 13 ga Fabrairun 1976, bayan shafe kwana 199 a kan mulki.
Janar Muhammadu Buhari ya hau mulki ranar 31 ga Disamban 1983 bayan hambarar da gwamnatin shugaban farar hula Shehu Shagari. Janar Buhari ya shafe shekara 1 da kwana 239 a mulki.
Janar Ibrahim Babangida ya zama shugaban kasar farar hula ranar 27 ga Agustan 1985, ya yi murabus ranar 26 Agustan 1993.
Sai gwamnatin Sani Abacha da ta fara ranar 17 ga Nuwamban ya kuma rasu ranar 8 ga Yunin 1998, abin da ya kawo karshen wa'adin mulkinsa.
Janar Abdulsalami Abubakar shi ne shugaban gwamnatin soja na karshe har zuwa yau a Najeriya, ya hau ranar 8 ga Yunin 1998 ya mika mulki ga farar hula ranar 29 ga watan Mayun 1999.

8. Mulkin farar hula fa?

Asalin hoton, Getty Images
Bayan samun 'yancin kan Najeriya, sai da Turawa suka rike kasar tsawon kwanaki kafin mulkin ya koma hannun 'yan kasa.
Ranar 16 ga watan Nuwamban 1960 Dr. Nnamdi Azikiwe ya zama shugaban kasar farar hula na farko, yayin da Sir Abubakar Tafawa Balewa ya zama firaminista, an kifar da gwamnatinsu ranar 16 ga Janairun 1966.
Mulkin farar hula bai dawo ba sai da Alhaji Shehu Shagari ya zama shugaban kasa a ranar 1 ga watan Oktoban 1979.
An samu gwamnatin rikon kwarya ta Cif Ernest Shonekan daga 26 ga Agustan 1993 zuwa 17 ga Nuwamban 1993
Gwamnatin fara hula ta dawo a Najeriya a 1999 bayan shafe shekaru a karkashin mulkin soja. Cif Olusegun Obasanjo ne ya sha rantsuwar kama aiki ranar 29 ga watan Mayun 1999 a karkashin jam'iyyar PDP, ya kuma sauka ran 29 ga Mayun 2007 bayan shafe shekara takwas.
Alhaji Umaru Musa Yar'Adua ya karba shi ma a karkashin PDP ran 29 ga Mayun 2007, kuma Allah Ya masa rasuwa ranar 5 ga Mayun 2010, lamarin da ya kawo karshen mulkinsa.
Mataimakinsa Goodluck Jonathan ya karbi mulkin inda ya karasa karo na farko ya kuma ci zabe ya kara shekara hudu a karkashin PDP, inda ya sauka ranar 29 ga watan Mayun 2015 bayan shan kaye daga Muhammadu Buhari.
Ranar 29 ga watan Mayun 2015 ne Shugaba Buhari ya sha rantsuwar kama aiki bayan lashe zabe a karkashin jam'iyyar APC kuma ya kammala karo na farko a shekarar 2019 inda aka sake zabarsa yake karo na biyu a yanzu.










