Mata 3 da suka yi gwagwarmayar samun ƴancin Najeriya

Asalin hoton, OTHER
- Marubuci, Fauziyya Kabir Tukur
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja
- An wallafa
A tarihin Najeriya, akwai matan da suka taka muhimmiyar rawa a gwagwarmayar neman ƴancin ƙasar.
Sai dai sau da yawa, ba a cika ambato su ba idan aka tashi bayar da tarihin samun ƴancin Najeriya.
Yayin da ake bikin cikar Najeriyar shekara sittin da samun ƴanci daga turawan mulkin mallaka, mun tattaro bayanai kan mata biyar da suka nuna bajinta kuma suka bayar da gudunmawa a siyasar ƙasar.
Hajiya Gambo Sawaba

Asalin hoton, OTHERS
Zai yi wuya a tsallake sunan Gambo Sawaba idan aka zo kan batun siyasar Najeriya.
Ita ce mace ɗaya tilo 'yar siyasa da ta yi ƙaurin suna a arewacin ƙasar har zuwa shekarun 1990.
An haifi Gambo Sawaba a shekarar 1933 a birnin Zaria da ke jihar Kaduna a arewa maso yammacin kasar, kamar yadda Rima Shawulu Kwewum ya rubuta a littafinsa mai suna The Gambo Sawaba Story.
Gambo Sawaba ta tsunduma fagen siyasa ne tana da shekaru 17 kacal a duniya.
Ta kasance 'yar jam'iyyar adawa a wancan lokacin ta Northern Elements Progressive Union (NEPU) tare da Malam Aminu Kano duk da cewa jam'iyyar Northern People's Congress (NPC) ce ke da matukar goyon baya a arewacin Najeriya.
Ta riƙe muƙamin shugabar mata a jam'iyyar inda ta tsaya tsayin daka don ƙwatar wa mata ƴancinsu na yin zaɓe da tsayawa takara.
Ana iya cewa ta taka rawar da babu macen da ta taba irinta a arewacin Najeriya a wancan lokacin musamman a lokacin da ta hau kan mumbari a wani taron siyasa da maza suka mamaye a shekarar 1950 kuma ta yi jawabi mai jan hankali dangane da siyasar Najeriya.
Wannan ya ƙara fito da ita kuma ya zamar mata wani ginshiki na rayuwarta ta siyasa.

Gambo Sawaba ba ta taɓa riƙe wani muƙami na gwamnati ba amma ta taka muhimmiyar rawa wajen haɗa kan ƴan ƙasa da ƙwatarwa talakawa da mata haƙƙinsu sannan ta ƙalubalanci nuna wariya da ake yi wa mata a arewacin Najeriya.
Ta yi amfani da muryarta wajen sukar auren dole da auren wuri da ake yi wa mata a arewacin Najeriya.
Wannan ƙarfin hali da rashin tsoro na Gambo ya janyo mata ce-ce-ku-ce inda har jami'an tsaro suka taɓa kamata.
Gogewarta a siyasa ta ƙaru bayan da ta haɗa kai da fitacciyar ƴar siyasar nan kuma mai fafutukar kare haƙƙin mata Oluwafunmilayo Ransome-Kuti ta kudancin Najeriya.
Hajiya Gambo Sawaba ta rasu a shekarar 2001 bayan doguwar jinya.
Oluwafunmilayo Ransome-Kuti

Asalin hoton, Ransome- Kuti Family
Mutane da yawa sun fi sanin Funmilayo Ransome-Kuti a matsayin macen da ta fara tuƙa mota a Najeriya.
Sai dai abin da ba a sani ba shi ne tana daga cikin matan da suka yi rawar gani a fagen siyasar ƙasar don ana iya cewa ita ce mace ta farko da ta fara kafa jam'iyyar siyasa a Najeriya.
Haka kuma, ana iya cewa ma tana kan gaba cikin jerin masu fafutukar kare haƙƙin mata a Najeriya a shekarun farko-farko na 1990.
Ita ce ɗaliba mace ta farko a makarantar sakandire ta Abeokuta.
An haifi Funmilayo Ransome-Kutu a shekarar 1900 a Abeokuta da ke jihar Ogun a Najeriya.
Ta yi karatun boko sosai inda neman ilimi ya kai ta har Burtaniya.

Bayan dawowarta daga Ingila ne ta kafa Ƙungiyar Mata ta Abeokuta ko Abeokuta Ladies Club (ALC), wadda mafi yawan mambobinta Kiristoci ne mata da suka yi karatun boko kuma an kafa ta ne don taimakon marasa galihu.
Sai dai daga baya, ƙungiyar ta rikiɗa ta zama ta siyasa kuma mai ƙoƙarin ƙwato wa mata haƙƙinsu.
Dalilin haka, Funmilayo ta sauya wa ƙungiyar suna zuwa Abeokuta Women's Union (AWU), wato Ƙungiyar Mata 'Ƴan Kasuwa kuma ta bai wa duka matan Abeokuta damar zama ƴan ƙungiyar.
Oluwafunmilayo ta kasance mace ta farko da ta fara jagorantar ƙungiyar a shekarar 1946.
A ƙarƙashin jagorancinta, ƙungiyar ta yi fafutukar yaƙi da matsanancin harajin da gwamnatin Oba Ademola II ta sa wa mata masu ƙananan sana'o'i a kasuwa sannan ta jagoranci zanga-zangar da ta yi sanadiyyar saukar Oba Ademola II, sarkin Egbaland na wancan lokacin daga karagar mulki.
Funmilayo ta yi shugabar ƙaramar hukumar Abeokuta sau da yawa a tsakanin shekarun 1949 da 1951.
Tana cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar National Council of Nigeria and the Cameroons, NCNC a shekarar 1944 inda daga baya ta tsaya takarar majalisar dokokin yanki ƙarƙashin jam'iyyar amma ta fadi zaɓen.
Bayan nan ne ta sake tsayawa takarar kujerar majalisar dokokin yanki a matsayin ƴar takara mai zaman kanta bayan da jam'iyyar ta hana ta sake tsayawa takara.
Daga nan ne kuma ta fice daga jam'iyyar NCNC sannan ta kafa wata jam'iyyar mai suna Commoners' People's Party.
Funmilayo Ransome- Kuti ita ce mahaifiyar shahararren mawaƙin nan na kudancin Najeriya kuma mai sukar gwamnatin ƙasar a waƙoƙinsa, Fela Anikulapo- Kuti.
A shekarar 1977, a zamanin mulkin soja a Najeriya wasu sojoji suka faɗa wa gidan da Funmilayo da ɗanta Fela suke zaune kuma suka wurgo ta daga wata taga da ke saman bene.
Ta rasu a shekarar 1978 sanadiyyar raunukan da ta samu a fadowarta daga saman benen.
Cif Margaret Ekpo

Asalin hoton, OTHERS
An haifi Margaret Ekpo a shekarar 1914 a jihar Cross River a kudancin Najeriya.
Margaret Ekpo ta kasance shugabar mata kuma ƴar majalisar dokoki da ta bayar da gagarumar gudunmowa a fagen siyasar Najeriya musamman kafin samun ƴancin ƙasar.
Ta fara tsunduma harkar siyasa ne a shekarar 1945 a lokacin da mijinta ke cike da ɓacin ran yadda turawan mulkin mallaka ke wulƙanta likitocin Najeriya.
Sai dai kasancewarsa ma'aikacin gwamnati ba shi da damar daga murya a kan batun.
Margaret ta ɗaura ɗamarar ƙwato wa likitocin haƙƙinsu ta hanyar halartar tarukan da ake shiryawa don tattauna batutuwan yadda turawan ke nuna wa ƴan Najeriyar wariya.
Ta taɓa halartar wani taro inda ta kasance mace ɗaya tilo a taron wanda Mbonu Ojike da Nnamdi Azikiwe da Herbert Macaulay suka yi jawabi.

A shekarar 1946 ta kafa Ƙungiyar Mata Ƴan Kasuwa a birnin Aba a jihar Abia.
Haka kuma, a daidai wannna lokacin ne ta fara shahara wajen nuna ƙin jinin mulkin mallaka da fatan samun ƴancin Najeriya. Wannan ya sa ta zama ƴar jam'iyyar National Council of Nigeria and the Cameroons, NCNC.
Tana cikin manyan mambobin jam'iyyar NCNC kuma ta taɓa riƙe muƙamin mataimakiyar shugabar ƙungiyar mata ta jam'iyyar.
A shekarar 1954, an naɗa ta shugaba mai taken Cif inda aka ba ta kujera a Majalisar Cif-Cif don ta zama wakiliyar mata. Wannan ba abin da aka saba gani ba ne tunda a baya duka maza ne ke maye guraben.
Margaret ta halarci tarukan gyara kundin tsarin mulkin Najeriya da dama a Legas da Landan a lokacin da ta ke jam'iyyar NCNC kuma ta yi ƙaurin suna saboda ra'ayinta na son ƴancin ƙasar.
A shekarar 1961, Cif Margaret ta tsaya takarar kujerar majalisar dokoki ta yankin Gabashin Najeriya kuma ta ci zaɓen.
Ta kasance 'yar majalisar har zuwa shekarar 1966.
Cif Margaret ta kasance mai fafutukar ganin haɗin kan ƴan Najeriya da tabbatar da samun ƴancin mata musamman a ɓangaren siyasa.
A lokacin da take majalisar dokoki, ta yi yaƙin ƙwato wa mata damar yin kasuwanci da siyasa da ilimi.
Margaret ta rasu a shekarar 2006 a jihar Cross River tana da shekaru 92.












