Taliban: Yadda ‘yan kungiyar ke kara mamaye kasar Afghanistan

Asalin hoton, EPA
- Marubuci, The Visual Journalism Team
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
- An wallafa
'Yan kungiyar Taliban da suka sake farfadowa sun kwace karin wasu yankuna a kasar Afghanistan cikin wata biyu da suka gabata fiye da duk wani lokaci tun bayan da aka hambarar da gwamnatinsu a shekaar 2001.
Sama da shekara 20, tasawirar yankunan da gwamnatin Afghanistan ke iko da su na sauyawa a kodayaushe saboda ayyukan Taliban. Mun duba yadda yanayin yawan sauyawar riko da ikon da yankuna ke yi.
Da alama kungiyar Taliban ta kara karfi a cikin makonnin bayan nan daga janyewar dakarun Amurka - tare da sake karbe ikon gundumoni da dama daga hannun dakarun gwamnati.

Binciken da sashen Afghanistan na BBC ya gudanar ya nuna cewa yanzu masu tayar da kayar bayan suna da karfi a fadin kasar.
Yankunan sun hada da lardunan arewaci da arewa maso gabashi da tsakiya - kamar su Ghazni da Maidan Wardak. Suna kuma kara dosar birane kamar su Kunduz da Herat da Kandahar da Lashkar Gah.

A batun rike ikon, muna nufin gundumomi da cibiyoyin mulki da helkawatar 'yan sanda da sauran hukumomin gwamnati na karkashin ikon Taliban.
Dakarrun Amurka da aminansu na kungiyar tsaro ta NATO da kuma aminanta na yanki sun tilasta wa kungiyar Taliban ficewa daga yankunan da ta ke rike da ikon a shekarar 2001.
Kungiyar ta rika bai wa Osama Bin Laden da sauran manyan 'yan kungiyar al-Qaeda masu alaka da hare-haren 11 ga watan Satumbar shekarar 2001 a Amurka mafaka.
Amma duk da cigaba da kasancewar dakarun kasashen waje a yankin, da tallafin biliyoyin daloli na horar da dakarun Afghanistan, 'yan kungiyar Taliban din sun sake hadewa kana sannu a hankali suka kara karfi a karin wasu yankunan masu nisa.
Manyan yankunan da suka ke da tagomashi na kusa da yakunansu da suka fi karfi a kudanci da kudu maso yammaci - lardunan arewacin Helmand, da Kandahar, da Uruzgan, da kuma Zabul.
Amma har ila yau, a dutsunan kundancin Faryab a arewa maso yammaci da kuma tsaunukan Badakhshan ia arewa maso gabashi.

Wani bincike da BBC ta gudanar a shekarar 2017 ya nuna cewa 'yan Taliban sun rike cikakken ikon gundumomi da dama. Amma binciken ya kuma nuna cewa suna da karfi a sauran yankunan kasar da dama, inda suka kaddamar da hare-haren mako-mako ko wata-wata a wasu yankunan, tare da nunin gagarumin karfi fiye da na baya da aka kididdige.

Mutane kusan miliyan 15 ne - rabin yawan al'ummar kasar - aka bayar da rahoton cewa na zaune a yankunan da ko Taliban ke rike da iko, ko kuma inda Taliban din ke kasancewa a koda yaushe suna kuma kaddamar da hare-hare a kai-a kai kan dakarun gwamnati.
Shin kungiyar Taliban na kara karfi?
Duk da cewa yanzu suna rike da ikon karin wasu yankuna fiye da yadda suka yi a shekarar 2001, halin da ake ciki mai sauyawa ne.
A dole sai da gwamnati ta bar wasu cibiyoyin mulki na wasu gundumomin, inda ba za ta iya jure wa hare-haren da babu kakkautawa daga kungiyat Taliban ba.
An karbe wasu da karfin hare-haren.
A inda gwamnati ke iya sake hada kan dakarunta ko kuma mayakan sa-kanta, ta sake karbe wasu yankunan da ta rasa - ko kuma cigaba da fadan a wadannan yankunan.

Duk da cewa dakarun Amurka sun fice a cikin watan Yuni, wasu ragowar sun rage a birnin Kabul, kuma dakarun sojin saman Amurka sun kai hare-hare ta sama a kan mastugunan mayakan na Taliban a cikin kwanaki kadan da suka gabata.

Akasari dakarun gwamnatin Afghanistan na rike da birane da gundumomi da suke tuddai ko kuma kwari - wanda kuma nan ne inda akasarin al'ummar kasar ke rayuwa.

Yankunan da Taliban suka fi karfi na da yawan al'umma, mai fiye da mutane 50 a ko wane fadin murabba'in kilomita a wurare da dama.

Gwamnati ta ce ta aike da karin dakaru zuwa manyan biranen da ke fuskantar barazanar kungiyar Taliban, kuma ta kafa dokar hana fitar dare a fadin kusan duka biranen kasar da aniyar hana 'yan kungiyar Taliban kutsawa cikin birnin.
Duk da cewa alamu sun nuna suna kara nausawa ta tsakiyar biranen Herat da Kandahar, 'yan kungiyar Taliban ba su riga sun cafke ko da guda day aba.
Amma kuma, nasarorin kama yankunan da suka yi ya kara musu karfin matsayinsu na neman tattaunawa, kana da kara samun kudaden shiga ta hanyar haraji da kuma ganimar yaki.
An hallaka fararen hula da dama sakamakon tashin hanhalin a farkon rabin wannan shekarar.
Majalisar Dinkin Duniya ta dora alhakin akasarin mutuwar fararen hula 1,600 a kan kungiyar Taliban da sauran masu adawa da gwamnati.
Fadan ya kuma tilasta wa mutane da dama tserewa daga gidajensu - kusan 300,000 sun rasa matsugunansu tun farko fara fadan a cikin shekarar.
Hukumar Lura da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta ce sabon karuwar da aka samu na mutanen da suka rasa matsugunansu a fadin lardunan Badakhshan, da Kunduz, da Balkh, da Baghlan da kuma Takhar na faruwa ne a yayin da Taliban ta kwace manyan wurare na yankunan karkara.
Wasu mutane sun tsere daga kauyuka ko gundumomi masu makwabtaka kana daga baya suka dawo gida, saura sun cigaba da kasancewa ba su da matsugunai har na tsawon lokaci.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa hare-haren Taliban sun kuma Tilastawa 'yan gudun hijirar Afghanistan da dakarun gwamnati tsallaka kan iyaka zuwa cikin kasar Tajikistan.

Asalin hoton, Getty Images
'Yan kungiyar Taliban sun kuma bayar da rahoton karbe ikon tsallaken kan iyakoki da dama, da suka hada da Spin Boldak, wani babban mashigin kasar Pakistan.


Yanzu kungiyar Taliban c eke karbar kudin harajin da jami'an hukumar lura da shige da ficen kaya ta kasar ke karba wajen shiga da kaya cikin kasar ta kan tsallaken iyakokin kasar - duk da cewa babu tabbaci kan adadin yawan kiyasin koma bayan kasuwancin da aka samu a sakamakon fadan.
Amma kuma, Islam Qala da ke kan iyaka da kasar Iran alal misali, na iya samar da fiye da dala miliyan 20 a ko wane wata.
Tsaikon da aka samu na shige da ficen kaya ya yi mummunan tasiri a kan farashin kayyakin amfanin yau da kullum a kasuwanni - musamman makamashin girki da kayan abinci.









