Gujarat: Jaririn da aka sace sau biyu a India

An sace wani jariri a garin Gujarat da ke yankin yammacin Indiya har sau biyu. Wakilin BBC a yankin Bhargava Parikh ya bibiyi dalilin hakan.
"Ba zan sake barin a sace ɗana ba," in ji Meena Wadi, wata mai aikin kwadago da ke rayuwa a kauyen Gandhinagar da ke birnin Gujarat.
Uwar jaririn, mai shekara 25, har yanzu tana ɗimauce sakamakon sace ɗan nata da aka yi har sau biyu.
Tashin hankalin da Meena ta samu kanta ciki ya fara ne kwana guda bayan komawarta gida daga asibiti a ranar 1 ga watan Afrilu.
Ta ce wata mata da ta nuna mata ita ma'aikaciyar asibiti ce a inda ta haihu, ta bita gida inda ta nuna mata akwai buƙatar a yi wa jaririn riga-kafi. Don haka Meena da jaririnta suka bi wannan mata zuwa asibiti. Matar ta karbi jaririn ta cewa Meena ta jira ta za a fara yi masa hoto.
Bayan shafe awanni, matar dai bata koma wajen Meena ba. Cikin rudewa Meena ta shiga neman matar. "Lokacin da masu gadi suka ji ina ta kuka sai suka tambaye ni menene ke faruwa. Da na basu labari sai suka kira 'yan sanda," in ji ta.
Sama da jarirai 43,000 aka sace a Indiya a bara, kamar yadda ma'aikatar habbaka harkokin mata da yara ta kasar ta bayyana. Bayanan gwamnati kuma sun ce a kowacce shekara yara 3,500 ne ke ɓata.
masu fafutukar kula da hakkin yara sun ce adadin zai iya zarce haka, ganin cewa iyayen da ke fama da talauci ba sa iya shigar da koken an sace yaransu - amma Meena da mijinta Kanu sun shigar da kokensu ga 'yan sanda nan da nan.
Binciken
"Meena ba ta san komai ba game da wannan mata, ko da sunanta kuma. Ta ma gaza kwatanta matar," in ji jami'in da ke gudanar da bincike HP Zala.
Dan haka Zala da sauran tawagarsa sai suka fara duba na'urar CCTV da ke naɗar duk abin da yake faruwa a asibitin. Anan ne suka fara samun bakin zaren - wata mata da ta fita titi da wani abu a boye a cikin rigarta. Babu wanda ya sani ko jaririn ne a ciki.
Bayan an ta tambayar masu tuka ababan hawa kusan 500, anan aka gano mai yafaru: hoton bidiyo ya nuna matar ta dauki babur mai kafa uku zuwa wani kauye da ke kusa da asibitin. Wani da ya shaida hakan ya ce tabbas akwai jariri a hannunta.
'Yan sandan sun ci gaba da duba wannan kyamara tare da tambayar wani mai kayan masarufi da ke kan babbar hanyar kauyen, bibiyar hakan ya kai su ga wani kauye, inda rahotanni suka ce daga nan ba a kara jin ɗuriyarta ba.
Binciken ya kai su ga wata gona da aka yasar a nan ne aka ga kayan matar da katinta na 'yar kasa. Abin dai ya daure musu kai, daga baya suka bi kwatancen da aka rubuta a jikin katin shaidar.
Sun gano matar da jariri a tare da ita, sai dai kuma ba jaririn Meena ba ne.

Asalin hoton, Getty Images
Matar ta shaida wa 'yan sandan cewa mijinta na da aure a boye da wata mata, wadda ta zarga da sace kayayyakinta, ciki har da katin shaida da suka tsinta. Ta kara da cewa jaririn ta same shi ne a aurenta na biyu.
"Mun shiga neman mijin nata daga baya mun sami wasu ma'urata da wani jariri a kwatancen da matar farko ta yi mana," in ji Zala. Gwajin kwayar halitta ta DNA da aka yi ya tabbatar da cewa jaririn na Meena ne.
An kama ma'auratan daga baya kuma aka ba da belinsu.
Matar ta amsa zargin da ake mata na sace jaririn Meena ta kuma so ta goga wa mutumin da yake da matar farko ta hanyar ajiye kayanta da katin shaidarta a gonar. mutumin ya ce shi bai san komai ba akan wannan batu na cewa jaririn nasa ne.
"Ina na bukatar haihuwar ɗa namiji maimakon 'ya mace anan," in ji wani tsohon dan sanda Deepak Vyas. "Suna bukatar yaro ko ma ta yaya ne. saboda wannan bukata sukan saci yaran talakawa a ko ina."lies."
Yunkuri na biyu
Meena da mijinta Kanu sun yi matukar murnar dawowar ɗansu, sai dai murnar ba ta yi tsayi ba.
A ranar 9 ga watan Yuni, an kara sace shi, wata biyu bayan an dawo musu da shi.
Meena ta fita karbar yasassun abubuwa lokacin yaron yana barci a karkashin bishiya, a cewarta. lokacin da ta dawo sai ta ga fili fayau babu shi babu tsumman goyonsa.
Lokacin da suka garzaya wajen 'yan sanda sai Mista Zala ya yi matukar kaduwa da ganin ma'auratan a karo na biyu.
Haka dai aka ƙara yin sa'a kyamarar da ke sanya idanu ta kara nuna musu wanda ake zargi - a wannan karon wani mutum ne a kan babur a ranar da jaririn ya ɓata.
Lokacin da 'yan sanda suka same shi sai yace ba shi ba ne akan babur din a ranar - wani abokinsa ne da ke zaune a jihar Rajasthan.

Tawagar Mista Zala ta tuntuɓi 'yan sanda a Rajasthan kuma an gano jaririn a gidan abokin.
Shi da matarsa da har yanzu suke tsare, sun ce sun saci dan gidan Meena ne saboda ba su da ɗa nasu na kansu.
"Yana aiki ne a wani kamfanin gine-gine tare da mijin Meena. Lokacin da ya ji labarin jaririn sai ya fara shirin dauke shi," in ji Mista Zala.
Bayan kwana hudu Meena ta kara haduwa da jaririnta.
Yanzu dai 'yan sanda na ziyartar gidan Meena akai-akai domin duba jaririn - Meena ta ce sukan kai wa jaririn kyauta kuma su rika wasa da shi.
"Yan sanda na nuna masa kauna sama da mu," in ji ta.
Mista Zala bai ko nuna shakka ba. "ba za mu kara barin jaririn ya ɓace mana ba."











