Heatwaves: Masifar da tsananin zafi kan jefa mutum

A protester wearing a mask is seen amongst smoke

Asalin hoton, Reuters

    • Marubuci, Daga Zaria Gorvett
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Future
  • An wallafa

A cikin watan Yulin shekarar 1988 ne, a faɗin Amurka, an shaida yanayin bazara mai ɗumama da zafi da aka fuskanta.

Mazauna birni sun tattaru a bakin teku daban-daban, amfani da wutar lantarki ya ƙaru fiye yadda aka saba yayin da mutane ke kunna na'urorin sanyaya daki, kana hanyoyi na cika da motocin da suka lalace saboda zafin da ya wuce ƙima.

Alawowin ƙanƙara kan yi saurin narkewa kafin a kai ga sha.

Amma kuma wani abu daban shi ma yana faruwa.

A gaskiya, shekarar 1988 ba kawai shekara ce da aka tafka rana ba, amma har da abkuwar tashin hankali.

An samu abkuwar kisan kai, da fyaɗe, da fashi da makami da kuma cin zarafi da ba za su misaltu ba - har kusan miliyan ɗaya da hamsin da shida.

Shin za a iya danganta yanayin zafin da kuma abkuwar wadannan abubuwa na tashin hankali?

Mutane sun yi zargin cewa yanayin zafi ko ɗumama ka iya sauya halayyarmu har tsawon ƙarni da yawa.

Ƙaruwar aikata muggan laifuka a lokacin tsakiyar bazara

Bincike-binciken farko kan abkuwar wannan al'amari sun bayyana ne a ƙarshen ƙarni na 19, wanda ya zo dai-dai da sahihan alƙaluman aikata muggan laifuka.

Kamar yadda nazarin ya nuna, aikata laifuka a kan mutane kan ƙaru ne a lokacin watannin bazara, yayin da laifukan da a kan aikata kan dukiyoyi an gano cewa suna faruwa ne a lokacin hunturu.

Tun bayan wannan lokacin, shaidu ke ƙara bayyana.

A person stands in front of a burning car at night

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An fi samun tashen-tashen hankula lokacin bazara ba kamar lokacin damuna ba da ruwa ke hana mutane fiu ta wasu lokutan

A ko wace shekara, yayin da duniyar Mercury ta ƙara tasowa, mu kan fuskanci wani sauyi na bai daya.

Wasu daga cikin alamun kadan ne ke bayyana - akwai yiwuwar mutane su riƙa matsa hon ɗin motocinsu a duk lokacin da suka maƙale a cikin cunkoson ababen hawa, galibi kuma jami'an 'yan sanda kan lura da ƙaruwar halayyar rashin bin doka, kuma su kan kasa taimaka wa baƙi.

Amma sauran kan kasance cikin takura.

Wannan layi ne

Tsananin zafin shekarar 2018

Tsananin zafin shekarar 2018 a fadin duniya ya haifar da tsananin fari da kuma abkuwar wutar daji da ba a saba gani ba.

Hakan ya kora tarin dabbobin reindeer zuwa bakin tekunan kasar Finland har ma da rage girman manyan duwatsu a kasar Sweden - amma kuma ana danganta abkuwar hakan da wasu halayyar dan adam.

A Birtaniya, akwai bayanai da aka tattara na adadin kiraye-kirayen lambar wayar 999 ta ɗaukin gaggawa, inda wani jami'in ɗan sanda ya bayyana cewa jama'a na mayar da martani ''na ban mamaki'' game da irin wannan yanayin zafin.

A wasu yankuna, 'yan sanda sun bayar da rahoton cewa kiraye-kirayen lambar waya sun kai kashi 40 bisa 100.

Ko shakka babu, akwai hanyoyi daban na yin ƙarin haske ga ɗaiɗaikun mutane game da abkuwar lamarin.

Ƙaruwar kisan kai da kuma tsananin zafi

A Birtaniya, tsakanin watan Afrilun shekarar 2010 da 2018, an samu kashi 14 bisa dari (14%) na ƙaruwar aikata miyagun laifuka a yanayin ma'aunin zafi na (20C) fiye da na (10C).

A ƙasar Mexico, tsararrun aikata miyagun laifuka lokacin yanayi mai ɗumama - kana wasu ƙwararru sun yi zargin cewa saboda hakan na haddasa abkuwar ''tashin hankali''.

A ƙasar Afirka Ta Kudu, masana kimiyya sun gano cewa a ko wane ma'auni na yanayin zafin kan yi sama, akwai ƙaruwar kashi 1.5% a adadin alƙaluman kisan kan da suka faru.

A ƙasar Girka, wani bincike ya gano cewa fiye da kashi talatin bisa dari (30%) na kisan kai 137 da aka bayar da rahoto a wani yanki sun faru ne a ranakun da ke da fiye da matsakaicin ma'aunin zafi 25C.

An kuma shaida tsari mai kama da haka da ke da alaƙa da miyagun laifuka a yankin Kudu da Saharar Afirka, da Taiwan, da Amurka, da Finland, da Spaniya…da sauran su da dama.

An kuma gano tare da shaida hakan a ɗaruruwan binciken kimiyya.

A wani bincike kuma, masana kimiyya sun bi diddigin tashe-tashen hankula a fadin duniya daga shekarar 1791 zuwa 1880 - tare da gano cewa wannan ƙaruwa mai yawa ta faru ne a cikin watannin lokacin bazara.

Ta ɓangaren ko wace duniya suka kalla, har yanzu dangantakar ɗaya ce. Ga misali, a Turai akwai yiwuwar hakan ta faru a cikin watan Yuli - yayin da a Amurka Ta Kudu akwai yiwuwar su faru a cikin watan Janairu.

Karin wasu sabbin binciken sun tabbatar da alaka tsakanin kai komon jama'a da kuma yanayin.

A person drinking from a water bottle with sun shining through the bottle

Asalin hoton, PA Media

Bayanan hoto, Mutane sun yi zargin cewa yanayin zafi ko ɗumama ka iya sauya halayyarmu har tsawon ƙarni da yawa

A lokacin bazarar bara, hatsaniya ta ɓarke a kasar Netherlands bayan mako mai tsananin zafi tun bayan da ƙasar ta fara adana bayanai.

An banka wa wani gini wuta, an jefa ababen tartsatsin wuta wa jami'an 'yan sanda kana an cafke mutum 27.

Yayin da a bayyana yake cewa rashin adalci da sauran abubuwan da tunzuri ga rashin kwanciyar hankali a tsakanin al'umma ka iya faruwa a cikin fadin shekara guda, akwai alamu cewa za mu iya yin martani a lokacin da ya kasance da ɗumama.

"Akwai gargaɗi," in ji Trevor Harley, farfesan nazarin halayyar dan adam a Jami'ar Dundee. "Dangantaka tsakanin zafi da wasu abubuwa kamar hatsaniya na da fasalin- U.

Don haka a duk lokacin da ake cikin yanayin zafi ko ɗumama, mutane ba sa yin komai saboda abubuwan rashin jin daɗi da suka yi yawa na kasa motsawa.''

Wannan layi ne

Haɗarin kashe kai

Wani bincike na kashe kai 1,320,148 da suka faru a ƙasashe 12 ya gano cewa ƙaruwar yanayain zafi na da dangantaka da ƙaruwar hadarin aikata kashe kai, kana cewa wannan alaƙa a bayyane take kai tsaye a ƙasashen yammacin duniya da kuma Afirka Ta Kudu.

Baki daya, hadarin mafi girma kan faru a lokacin da yanayin zafin ya kai ma'aunin 27C.

Bincike a kasar Australia ya gano cewa akwai alamun karuwa a kwantar da marasa lafiya a asibiti a lokacin irin wannan yanayi, tare da karuwar kashi 7.3% a lokacin tsananin zafi.

Dalilan da suka saka yanayin yake da ƙarfi sosai kan halayyarmu wani abin ɓoye ne da ba a sani ba - amma yayin da duniya ke ƙara ɗumama da zafi, masana kimiyya na ta kokarin gano amsoshi.

Rashin kwanciyar hankali

Daya daga cikin dalilan da ka iya zama gaskiya shi ne yanayi mai tsananin zafi da ɗumama na haifar da rashin kwanciyar hankali, da ke saka mu a cikin wani yanayi na damuwa, tare da haifar mana da halayya mai tattare da illoli.

Akwai shaidu masu yawan gaske cewa ɓangare na farko game da wannan gaskiya ne - yanayi mai tsananin zafi na saka mu cikin halayyar saurin fushi da damuwa, da kuma ƙarancin farin ciki.

Lokacin yanayin zafi, akwai yiwuwar taurarin ƙwallo a gasar wasan kwallon kafa na Amurka (NFL) za su shiga yanayin da zai sa riƙa buga kwallon hukuntawa.

Ƴan sanda na kasancewa cikin amfani da kalamai marasa daɗi a lokacin bayar da rahoto, kana akwai yiwuwar mutane za su rika yajin aiki ko su riƙa barin ayyukansu.

Three men covered in tomatoes lying in a street coated in tomato juice

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Akwai shaidu masu yawan gaske cewa ɓangare na farko game da wannan gaskiya ne - yanayi mai tsananin zafi na saka mu cikin halayyar saurin fushi da damuwa, da kuma ƙarancin farin ciki

Harkoki a lokacin bazara

Ko shin waɗannan harkoki da ke faruwa lokacin bazara da ke sa mu hadu da sauran mutane tare da kara zafafa damuwarmu, ka iya kasancewa manyan dalilan da ke haddasa halayyramu ta lokacin tsananin zafi?

"Yana da matuƙar wahala a iya warware wadannan abubuwa, saboda a koda yause tare suke tafiya,'' in ji Harley.

"Idan ka dauki alkaluman yawan aikata kashe kai - su kan ƙaru a duk lokacin da shiga yanayin dumama kuma hakan na nufin na kashe kai kan kasance a koda yaushe saboda mutane na kasancewa a waje.''

A child is sprayed with water from an irrigation hose

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, "Yana da matuƙar wahala a iya warware wadannan abubuwa, saboda a koda yause tare suke tafiya,'' in ji Harley

Yanayi mafi tsananin zafi nan gaba

Annobar cutar korona ka iya samar da wasu amsoshi, saboda tun bayan ɓullarta, akasarin harkokin da mukan yi a lokacin bazara sun kasance ba masu yiwuwa ba.

Annobar ta riga ta nuna mana wasu gwaje-gwaje da dama da ke buƙatar amsoshi da gaggawa, kamar sum ai zai faru idan aka rage tafiye-tafiye masu nisa ko yadda dabbobin ruwa na whales za su yi idan tekuna suka kasance babu hananiya sosai, don haka me yiwuwa zai nuna ko shin tashin hankali na da alaka da lokacin bazara ko kuma dai kawai lokacin tsananin zafi.

Idan aka ture batun abin da ke haifar da alaka tsakanin yanayin da dabi'armu, akwai wasu munanan tasiri zuwa nan gaba.

Masana kimiyya sun yi hasashen cewa yayin da sauyin yanayi ke karuwa, karin ma'aunin zafi 2C kadai a yanayin dumamar duniya ka iya kara yawan tashin hankali da damuwar aikata muggan laifuka da kasha uku bisa dari a yankunan mafiya zafi a Yammacin Turai.

A halin yanzu, masana da dama sun yi amanna muna kan hanyar shaida karuwar zafi na sama da ma'aunin zafin na 3C, ko da kuwa mun kai ka cimma muradan kare ɗumamar yanayinmu.

Duk da cewa yanayin ya na shafar mu, har yanzu akwai abubuwan da ke boye, me yiwuwa ya kamata mu daura damara ne kan abinda ka iya faruwa nan gaba.