Matar da tashin hankali da kyama bai hana ta raba wa mata audugar al'ada ba

Irfana rike da audugar al'ada

Asalin hoton, Irfana Zargar

Bayanan hoto, Irfana Zargar ta ce mata da dama a Kashmir ba su samun damar sayen audugar al'ada
    • Marubuci, Daga Khadeeja Arif
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
  • An wallafa

Lokutan kullen korona da dokokin hana zirga-zirga, da kuma tsananin nuna kyama a cikin al'umma, ba su hana wa Irfana Zargar gudanar da aikin da ta saka a gaba ba.

A cikin shekaru bakwai da suka wuce, mata da dama a birininsu na Srinigar, na dogara da ita wajen samun abin amfanin yau da kullum - audugar al'ada.

Irfana ta taba samun kanta a mawuyacin hali - lokacin tana karama, abu ne "mai wahala" a gare ta ta sayi audugar al'adar da kanta.

"Mahaifina ne ya kan saya min. Bayan rasuwarsa, ban taba tunanin iya tambayar 'yan uwana maza ba,'' in ji ta.

Wannan wahala ce ta sa Irfana jajircewa wajen kokarin taimaka wa matan da ba su da galihu a birnin, mafi girma a yankin Kashmir da ke karkashin mulkin kasar Indiya.

"A koda yaushe na kan yi tunanin cewa idan na samu kudi da kuma hanya, zan sayi audugar al'ada ga duka mata.'' kamar yadda ta shaida wa BBC.

Tashin hankali da nuna kyama

Irfana na raba audugar al'ada ga wata mata 'yar Kashmir

Asalin hoton, Irfana Zargar

Bayanan hoto, Irfana yanzu tana raba audugar al'adar kai tsaye ga mata matalauta a unguwanninsu

A yankunan kudancin Asia, ana daukar mata masu jinin al'ada a a matsayin wadanda ba su da tsarki - har ma abin kunya.

A lokacin da suke jinin a'ada, a kan kulle su ko kuma a daina mu'amala da su.

Wannan nuna wariya da kyama ce ta dole Irfan da rika kokarin jurewa, kuma wadannan matsaloli sun fi muni a yankin na Kashmir mai cike da tashin hankuli, inda sayen ko wane abu kan kasance da kalubale.

Kasashen India da Pakistan sun yi ta artabu a kan mallakar yankin Himalaya kuma har yanzu akwai sauran burbushin rikicin yana dan faruwa, da ke haifar wa da mata cikas wajen samun 'yancin walwala. Iyalan da babu maza a cikinsu kan yi ta fama wajen samun kayyakin amfanin yau da kullum.

Audugar al'ada ita ce musamman ta fi zama matsala, saboda maza kan ki amincewa su saya wa 'yanuwancu ko danginsu mata.

Irfana ta ce ko su kansu matan Kashmiri da suke da halin sayen audugar al'adar ( kuma za su iya fita) su kan gamu da cikas wajen jure wa nuna kyama da ta shafi jinin al'ada a cikin al'umma.

Irfana Zargar na rungume da wata matashiya da ta samu audugar daga gare ta

Asalin hoton, Irfana Zargar

Bayanan hoto, Irfana ta ce ta san aikinta ba wani babba bane

"Mata da 'yan mata da dama kan rika jin kunyar zuwa shago sayen audugar. Ko da sun yi hakan, za su tambayi mai shagon, 'dan uwa' miko min wancan'. Ba za su iya ambaton kalmar audugar al'ada ba tare da jin kunya ba,'' in ji Irfana.

Ba wai kawai tana son audugar ta wadata ga duka matan ba kadai, har ma da sauya tunanin mutane game da munanan camfe-camfe game da jinin al'ada da su ne ke haifar da wannan matsala.

"Jinin al'ada yanayin yadda abubuwan jikin halittu ke tafiya ne don haka babu damuwa idan ana magana a kai,'' a cewarta.

Nuna halin ko in kula

Da farkon fari, Irfana kudinta kalilan ne - ko kuma tallafi.

Ba ta manta da abin da mahaifinta ya yi mata ba, kuma ta girma da matukar kaunarsa, amma sauran danginta ba su damu da yunkurinta ba.

Irfana dauke da damen kayan audugar al'adar

Asalin hoton, Irfana Zargar

Bayanan hoto, Damen kayan Irfana da kunshe da audugar al'adar da kamfai da kuma sinadarin goge hannu

"Da farko, yayyane maza ba su so abin da nake yi ba. Ba su damu da bayar da kyautar audugar a'ada ba, amma kuma ba sa son in riuka magana a kan jinin al'ada a shafukan sada zumunta," a cewarta.

Tana nufin duka al'adar nuna halin ko in kula da yin shiru game da duk abubuwa da suka shafi jinin al'ada.

Ganin cewa ta fito daga iyalai da kuma al'umma mai ra'ayin mutanen da, Irfan ba ta yi mamaki ba lokacin da danginta suka nuna adawa da shirinta da rabon audugar al'adar - ta hanyar amfani da wuraren ba-haya na jama'a.

Mastalolin annoba

Lokacin da ta fara rarraba audugar al'adar tana daliba ce kuma ba ta da isassun kudi, amma duk da haka ta iya ware dala bakwai a ko wane wata.

Bayan da ta samu aiki da wata ma'aikata a karamar hukumarsu ta iya samu halin kara yawan audugar da ta ke bayarwa.

Yanzu Irfana na kashe yawancin albashinta - akalla rupees 10,000 na India, kwatankwacin dala 140 a ko wane wata- a ayyukan nata.

Tana kuma amfani da lokutan da ba ta aiki wajen sarrafa auduguar al'adar, da kuma igiyoyi a tsakanin kawaye da kuma danginta.

Amma kuma annobar ta tilasta wa Irfana ta sauya yanayin yadda ta ke tafiyar da yadda ta ke kai wa ga mabukata.

Irfana talking to a group of women

Asalin hoton, Irfana Zargar

Bayanan hoto, Irfana na karfafa wa mata tattanawa kan tsafta lokacin jinin al'ada

"Duka birnin na karkashin dokar kullen korona. An rufe duka wuraren ba-haya na jama'a kuma na kasance kulle a cikin gida,'' in ji ta.

Tana amfani da shafukan sada zumunta wajen kai wa ga sauran matan. Wasu matan da suka saba daukar tasu audugar daga wuraren ba-hayan sun tuntubeta kai tsaye.

Yanzu ta gano daga ina bukatun suke fitowa, ta shirya game da rarraba kunshin kayan - da suka hada da audugar al'adar da kamfai da kuma sinadarin goge hannu - har ya zuwa inda mai ya kare mata.

"Bayan samun izini daga hukumomi, na fita domin rarraba kunshin kayan ga mabukata.''

Ko wane kunshin auduga daya ana sayar da shi kan cent 50 ko dala daya - kudi ne mai yawa ga wasu matan a Kashmir - kuma ana bukatar kunshin kayayyakin na Irfana.

"Mutane da dama sun rasa aikin yi saboda annobar. Na taba samun kiran waya daga wani matashi da ya saba aiki a matsayin mai jiran shago. Mahaifiyarsa makauniya ce kuma yana da 'yanuwansa mata su bakwai. Ba zai yiwu ya iya biya musu kudin sayen audugar al'adar ba.''

'Tauraruwa ce'

Hasina Bano na da 'yaya mata hudu, kuma daya daga cikin mata da dama da saboda talauci ba za su iya sayen audugar ba. Mijinta ya mutu, kuma tana samun tallafi ne daga dangi.

Irfana Zargar da Hasina Bano

Asalin hoton, Irfana Zargar

Bayanan hoto, Hasina Bano ta ce ita da ƴayanta ba su iya sayen audugar mata

"Mu kan yi amfani da tsofaffin tufafi ko gundarin auduga lokacin da suke yin jinin al'ada kafin Irfana ta shigo cikin rayuwarsu,'' in ji Hasina.

Tana zaune ne a daya daga cikin unguwannin matalauta da Irfana ta saba ziyarta.

"'Yan mata sun saba fama lokacin da suke jinin al'ada kuma ba su da wata hanyar sayen audugar. Irfana na yawan zuwa nan.. Ita tauraruwa ce a gare mu."

"Babu wanda ke taimaka mana da audugar al'ada saboda a nan babu wanda yake da tunanin cewa abu ne mai muhimmanci na amfani,'' in ji Hasina 'yar Hansa.

"Babban abin jin dadi ne idan ka samu yin amfani da audugar al'adar.

A gare mu ya kasance mawuyacin abu mu iya sayen su. Duka 'yanmatan da ke yankin nan na kaunar Irfana," kamar yadda Hansa ta bayyana.

'Mai kyautar audugar al'ada'

Yanzu ana yi wa Irfana lakabi na kauna mai suna 'the pad woman' wato mai kyutar audugar al'ada ta yankin Kashmir, Bayan wani film din India da ya yi fice a shekarar 2018 mai suna 'Pad Man' da ya nuna rayuwar Arunachalam Muruganantham, da ta kirkiro yadda ake hada audugar al'ada a gida a kuma farashi mai rahusa.

Irfana ta ce ta san mahaifinta zai goyi bayanta

Asalin hoton, Irfana Zargar

Bayanan hoto, Irfana ta ce ta san mahaifinta zai goyi bayanta

Ta kan rarraba kusan kunshin kaya 350 na jinin al'ada a ko wane wata, kuma a lokuta da dama ta kan ajiye irin wannan dauri a wuraren ba-haya na jama'a.

Tana so ta kai ga karin wasu mata da 'yan mata da har yanzu ba sa iya sayen audugar, kuma tana mayar da hankali wajen yin audugar al'adar da za a iya sabunta amfani da ita.

"Ina son shiga yankunan karkara a Kashmir inda har yanzu mata na amfani da tsumman tufafi a maimakon audugar al'ada. Wasu matan ma ba sa samun tsaftatattun tufafi da kan tilasta amfani da tsummokarai da ba su da tsafta, da kan haifar da yaduwar kwayoyin," a cewarta.

Ta san cewa aikinta kalilan ne, amma sakonnin fatan alkahairin da ta ke samu na karfafa mata gwiwar ci gaba da abin da da sa a gaba.

Irfana na tunanin da ace har yanzu mahaifinta na raye da zai yi alfahari da ita.